← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 269

Sashe 98

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Ina yarinyar take ?wanne hali take ciki ? Ina cikin jikin ta ? Gaba ɗaya martabar gidan sarautar maraɗi na cikin barazana , !

Dawowa yayi ya zauna a gefen sa gami da kautar da kai ,"

     Sai ka faɗi wanne yunƙuri kayi wajen neman gafarar ubangiji gami da nemo yarinyar tare da wanke kan ka , ka fa sani Yarima Youssouf ɓacin sunan ka daidai yake da zubewar martaba da ƙimar mahaifin ka "Maimartaba," tare da gaba ɗayan masarautar mu ,"

  A yau Yarima shi ya koma tamkar bawa da ake ba umarni babu ja ya shiga bawa Tafeedah labari tun daga ranar da kome ya fara wanzuwa a tsakanin su irin mawuyacin halin da ya shiga akan ɗiya mace a lokacin da yadda kome ya cigaba da gudana har zuwa ranar da ya tafi ya bar ta ,"

Tsumu Tafeeda yayi yadda yake zaton kome ba haka ya ji ba , tabbas ya san Youssouf bai yin ƙarya da garaje , yayi zaton da son ran sa ya aikata kome , amma a yanzu da ya saurati bayanin bakin sa idan kuwa gaskiya ne tabbas akwai lauje cikin naɗi ,"

  Ya zama dole a nemo yarinyar nan tare da cikin jikin ta ," domin mu samu tabbacin abun da ke cikin ta bashi alaƙa da kai , domin kai ma baka tabbatar ba , bani fatan ya zam naka ne ,"   ya kuma zama dole ka gyara kuskuren ka ɗan ouwa kamar yadda kayi niyya nima ina goyon baya ɗari bisa ɗari ka taimaki rayuwar yarinyar nan son samu ...ka aurar ta ga wani !

  Basu gushe ba suna tsara yadda lamura zasu musu sauƙi wajen samun ta har dare ya shiga , nan suka bar duk wani shirin su zuwa gobe ,"

      ****
   9pm

Doctor Hamza ya kammala duk wani shirin sa da ya ɗau tsawon kwanaki goma yana yi kafin rubuta hutun ƙarshen shekara da yayi na tsawon sati shidda da zai fara daga gobe ,

Kamar yadda ya tsara a goben zai bar garin zuwa zaria inda yake so ya ƙare hutun nasa a chan Jami'ar Ahmadu Bello , sashin horas da likitoci inda ya ƙirkirawa kan sa wani guntun shiri na faɗaɗa ilmin sa da bincike akan sashin da yake da ƙwarewa ta fannin sa na tsawon sati shiddan

, duk a ƙoƙarin sa na son ganin ya yakice duk wata damuwa da Yakaka ta ɗarsa masa cikin ran sa domin kuwa bai san yana son ta har haka ba , bai san son da yake mata yayi masa mugun kamu , ya kafu yayi rassa a cikin ran sa ba ,

sai cikin kwanakin da suka biyo bayan gudun da tayi ta bar shi , ya kuma gano duk wata rufa-rufa tare da yaudarar da tayi masa , kullum da tunanin abun yake rayuwa cikin ran sa ,

ko kaÉ—an bai jin sa dai-dai kewa tare da tsantsar tsanar ta da ya cusawa kan sa na barazana ga walwalar sa ,

aikin sa da kan sa ya fara samun tsiko a cikin sa , bai tare da kwanciyar hankalin da ake buƙatar irin sa cikin aikin sa , hakan ya sa ya rubuta Annual leave na dole , kuma a karo na farko cikin shekaru shida da fara aikin sa ," bai taɓa rubuta hutu ba sai fa wannan karon da So ya jefa shi a damuwa ,!

Dan haka ya zaɓi yayi ɗan nisa da inda ta taɓa zama da duk wani abun da ya shafe ta na ɗan wani lokaci ko zai samu ya danni zuciyar sa ya yakice ta baki ɗaya daga cikin tunanin sa ya fuskanci rayuwar sa ta gaba , cikin taka tsantsan da duk wani lamari na mata , haka yake fata haka yake buri.

Ya gama tanadar kome da mahaifan su zuwa ƙannen sa zasu iya buƙata na kimanin watanni biyu a gaba , gefe guda bai ƙi ba , bai ɗauke kai ba , bai kuma yi fatali da marayun da yakaka ta wofantar ba duk da cewa ya so yin hakan da farko amma tausayi da ya riga ya zama bangare mafi kyau a cikin jerin halayen sa ya sanya shi gaza yin ko oho da lamarin Falmata da baby mama ,
   toh meye laifin su ? me suka yi masa ,?  basu da laifin kome basu kuma yi masa kuskuren kome ba, su ɗin Raunana ne abun a taimakawa

Duk da cewa ya ɗauke ƙafafun sa daga cikin saboda kiyaye zuciyar sa da tuno masa da yakaka da take yi , amma cikin tanadin da yayi akan tafiyar da zai yi bai manta Falmata da mama ba su ma ya tuna da su ,

Ya sayi Cartons na madarar baby mama zuwa daiper , wiper , da tarin kayan jarirai himili guda , Falmata kuwa cikin kuɗin da ya danƙawa Rahima yace ta raba uku ta bada kashi ɗaya ga Fatima ,

Bayan ya kammala haɗa duk wasu abubuwan da zai buƙata Zama yayi akan kujera ya miƙe ƙafafun sa aƙasa tare jingina kansa da fuskar kujerar ya ɗaga kan sa sama , "

Tunanin da bai so shi ya fara , kafin kunnuwan sa su fara jiyo masa kukan ta char-char -char tana yi babu ƙaƙƙautawa , shiru yayi yana jin yadda tausayin ta ke lulluɓar sa ,  yasan ba kukan kome take ba illa kukan rashin jin ɗumin jikin uwa ,

Lumshe idanun sa yayi yana jin sunan da wani sashi na zuciyar sa ya ƙira yakaka da shi ,"muguwa ,"

Ji yayu kukan ya tsawaita , kuma kasantuwar dare ne tamkar a gaban sa take yi , har cikin ran sa yake jin kukan nata , dan haka ya mike cikin rashin kuzari ya sanya takalmun sa ," gami da yiwa cikin gidan tsinke , 

A tsaye ya tarar da su su uku , Falmata Rahima , Da kuma hajja mai wurya ,"  Baby mama tana rungume tsam a kirjin falmata hajja mai wurya da Rahima sunyi sunyi ta basu ɗiyar su gwada rarrashin ta taƙi , sai faman jijjiga ta take tana hura mata kunne , idan ban da kuka da mimmiƙewa babu abunda jaririyar take yi ,"

  Meye same ta ?

Yace da su lokacin da yake ƙarasowa inda suke ,"

  Da sauri Falmata ta nufi inda taji tashin muryar sa ,"
    Muryar ta tana karkarwar kukan da ta riga ta fara yin sa tun tuni , tace
   Yaya dakta Dan Allah duba min Ita meya same ta ko bata da lafiya ne ? Tun ɗazu taƙi shiru ,

    Bani ita yace yana karɓar ta daga hannun ta ba musu ta sakar masa ita , ta kafe inda take jin tashin muryar sa da ido , "

   Jujjuya ta yayi a hannun sa , kafin yace ungo ta hajja rage mata waɗannan dogayen kayan ,

  Zuruf Falmata tace kawo ta yaya dakta na iya cire mata , kuka take yi baza ta tsaya a cire mata a hankali ba , kar hajja ta ji mata ciwo ,"

   Sakin baki hajja tayi cikin hasken falon ta dallawa falmata harara ,

   Zata yi magana Dakta hamza yayi mata alama da hannu tayi shiru ,
Miƙewa falmata baby mama yayi,
   
Ga mamakin sa tsaf ta cire mata kayan jikin ta ta barta da diaper tana ta sharar ƙwalla , ta miƙa masa ita dudduba ta yayi ya tattaɓa cikin ta inda nan take ya gane cikin ta ne ya kumbura ,
       Ɗaura ta a kafaɗa yayi a hankali ya shiga shafa mata baya yana ɗan jijjiga ta , ba'a fi mintuna huɗu ba ta fara fitar da iskar da ta cika mata ciki , a hankali kuma kukan ya fara lafawa , kafin mintuna goma ƴar jaririyar tayi bacci abin ta ,

Sauƙe ta yayi ya rungume ta a ƙirjin sa , yana kallon ƴar zagayayyar fuskar ta da take ruwan hoda dan fari , gashin da ya kwanta a gaban goshin ta har ya haɗe da girar ta , ,"irin na maman ta ya aina cikin ransa ,"

   Da sauri ya miƙawa Falmata ita
Ungo karɓe ta Fatimah , nan gaba idan zaki bata madara ki tallafo kan ta , sannan bayan kin gama bata ki ɗora ta akan kafaɗar ki ki dunga shafa bayan ta kar ki kwantar da ita sai kin tabbatar tayi gyatsa , sannan kar a bata madara da ya zarce ka'idar da aka umarta a bata ,

waye ke hada madarar ?

  Ita take haɗa mata cewar Rahima

Ita kuma ?  Tayaya zata auna ?  Meyasa ke bakya haɗa mata ?

Kafin tayi magana Hajja mai wurya tayi wuf tace ,
    Yo wannan yadda take ƙwalafacin ƴar nan da wa ta yarda ? Ko fa ɗaukar ƴar bata yarda ayi , koyaushe tana ƙunshe a hannun ta kamar lalle ,!

Cikin siririyar murya falmata tace ina ganewa yaya dakta , idan na É—ibo madarar a cikin É—an ludayin É—ibar madarar sai na shafe kan sai na zuba a robar bata madarar, sai nasa ruwan É—umi dai-dai zanen layin na biyu ko ?

     Hakane , haka zaki cigaba da yi mata
    yace , yana kama hanyar barin wajen ,
   Yaya dakta
    Ta ƙira sunan sa .
  Chak ya tsaya kafin ya waiwayo ta
    Na'am Fatima
Mun gode da kome , Mun gode da taimako, Allah ya ninka maka ya saka da Alheri,
    Jim yayi kafin yace mata
  Ameen Fatima , gobe zan yi tafiya ki min addu'a
    Allah ya kiyaye hanya , Ya dawo da kai lafiya , Allah ya baka sa'a

   Ameen Yaa Rabb
Yace yana ƙarasa barin falon , cikin ran sa wani irin yanayi yake ji na taso masa , Ina ma ? Ina ma ? Kai ina ma daga bakin ta waɗannan kyawawan addu'o'in ke fitowa  ?

          Washegari
Chapter 98 · 0% Book details