← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 269

Sashe 49

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ficewa yayi bayan ya tabbatarwa yakaka duk inda kuɗi suke ta nemo ta biya sa kayayyakin da ya sissiyawa falmata domin shi bai yin asara koh ta sisin kobo , kuma kar falmata ta sake taka ko da kofar ɗakin sa ne , idan har kuwa ya gan ta a gaban ɗakin sa babu abun da zai hana ya kirɓe ta ,'

Toh yanzu da ku ka nace kar a kore su akan ku zasu dunga kwana su biyun ? Kun san dai ku ukun ma a matse kuke tamkar kifin gongoni , cear madam saly

Da sauri yakaka wacce har lokacin rungume take da falmata da take ta faman sauke ajiyar zuci akan kukan da ta sha , tace
Ni zan dunga kwana a kan benci cikin rumfa idan ya so falmata ta kwanta tare da su a É—akin idan kin yadda ,
Sai da madam saly ta wurga mata harara domin har yanzu tana É—an jin haushin su
Ƙya ce haka mana dan kun samu na ƙyale ku algungumai , ni dai ku kiyaye ni kar ku bari na sake kama ku da wani laifi domin gaba ko kun fi kuturu naci sai kun bar gidan nan , tun da kin zaɓi kwanan kan benci a cikin shagon toh ke kika sani sautun mahaukaciya , duk abun da ya biyo baya ki kuka da kan ki , kar ki ce ban faɗa miki ba ,

Ba tare da fargabar kome ba yakaka ta amince da zantukan madam saly cikin ran ta tana sa mata albarka ,

Wanene Alhaji basko ?? Aina kika san shi ? meye haÉ—in ki da shi ? Kuma ta yaya yasan cewa ke mace ce ??
Su ne tambayoyin da yakaka ta jerowa falmata lokacin da take taya ta shiryawa cikin É—aya daga cikin kayan da take warewa take ajiyewa falmatan su ,

Ba tare da jinkirin kome ba falmata ta fayyace mata kome ,

Hawaye ne yake sauka bisa kumatun ta , meyasa mutanen duniya suke son zukatan su ?meyasa taimako domin Allah yayi ƙaranci meyasa zalunci ya yawaita , meyasa fasikanci ya zama mahaɗin rayuwar mafi yawan mutane ,??? Meyasa meyasa ? Ji tayi tsanar dukkanin mutanen da suke kewaye da duniyar ta ya kama ta idan aka ɗauke ƙanwar ta ,'
Nan gaba kar ki sake yadda da kowa falmata , idan na ce kowa ina nufin kowa ,! Kin ji ko ?
Ba tare da falmata ta hakiƙance da inda kalaman yakaka suka dosa ba ta amsa mata da toh ,"

Daga ranar yakaka ta koma kwanan cikin rumfar da suke sana'ar su ciki , yayin da idan kafafu sun yanke a wurin kamar sha biyun dare sun riga sun gama sana'ar su, zuwa lokacin duk ƴan iskan sun watse wasu sun shige ɗakunan su tare da abokan iskancin su sai ta haɗa teburan da suke gaban kujerun , guda huɗu ta shimfiɗa zanin ta akai tayi matashi da hannunwan ta tare da rufuwa da wani zanin , sai tayi baccin ta ba tare da tsoron duhu da shirun da wajen yayi ba ko kuma tsoron ƴan iskan da ka iya kawo mata farmaƙi , wurin kwanan ta na cikin ɗakin kuwa ta barwa falmata ,

A haka kwanaki suka fara miƙawa har yau da ake kwana na uku da faruwar lamarin falmata ta gagara sakewa dan kuwa tuƙuru ƴan matan gidan suke tsokanar ta , har suna cisge mata ɗan kwali , suna faɗin ta koma shigar maza ta fi yi mata kyau , da hakan ba ƙaramin sanya ta takaici yake ba , sai dai tayi matuƙar koƙari wajen boye damuwar ta domin kar ta jefa yakaka cikin damuwa ita ma , duk wani abun da idon ƴakakar bai gani ba game da tozarcin da ake yi mata bata faɗa mata .

Juyi yake ta yi akan katifar sa kaÉ—an-kaÉ—an yana jin wani sabon yanayi da ya fara ziyartar sa a tun lokacin da agogon wayar sa ya nuna masa sha biyun dare cib wanda a lokacin yana kan computer sa yana wani aiki sai dai wannan yanayi da ya fara ji yana taso masa ya sa shi rufe computer tare da wani irin bingirewa akan katifar sa tamkar dai an tunkuÉ—a shi ,'
daran ranar ya zo dai-dai da cikar sa shekaru talatin cif a lissafin watanni turawa ,

Miƙewa yake so yayi ya fita ya ɗauro alwala , domin ya samu damar raya ƙarshen daren da ibada Kamar yadda yake aikata hakan jifa-jifa , sai dai ga mamakin sa ya kasa tashi , haka yake jin sa kamar an ɗaure shi ko kuma an aza masa wani abu mai nawi an danne shi , yana jin sa a wani yanayi mai cike da fargaba da tsoro zuciyar sa na wani irin bugu , yana jin sa ɗan mitsitsi kuma sakayau tamkar ba shi ba , shi ya san ba bacci yake ba ba kuma a farke yake ba sannan ba mafarki yake yi ba , yana jin sa kawai a wata duniya ta daban , duk yadda ya so yayi addu'a ya kasa ,

Haka ya shafe tsawon awannin karshen daren har zuwa lokacin da alarm ɗin da ya saita a wayar sa ya fara rangwaɗo sautin kiran sallah cikin zazzaƙar muryar balarabe , wanda cikin ikon Allah ya ji cimak wannan nawin da yake ji ya hana shi motsi , babu shi tamkar dai an sauka a kan sa , da gudu ya miƙe tsaye , jikin sa ya jiƙe sharaf da gumi , wannan tsoron da yake ji ya kau , sai dai har yanzu ɗan sauyin da yake ji a jikin sa yana nan , amma cikin ran sa sai ya dangan ta hakan da zamantowar sa cikakken ɗa namiji lafiyayye da ya kai minzalin da ya kamata ya buƙaci mace , duk da cewa shi youssouf ba manemin mata bane , bai taɓa zina ba , bai taɓa kusantar kowacce mace ba duk yadda ya kai ga cuɗanya da matan bariki matan banza , shi mutum ne mai tsantsani ta wannan fannin ,
Da sauri ya ɓude ruwan leda ya juye cikin ɗan bokatin da yake yin amfani da shi wurin yin wanka , ya cika shi taf da ruwa gami da sunkuta ya fito daga tantin sa zuwa ɗan bayan gidan da aka samar masa na wucin gadi wanda yake mallakin sa shi ɗaya ,'

Ruwan na da sanyi sosai dan haka yayi tunanin zai taimaka wurin kawar masa da yanayin da yake ji a jikin sa , sai dai ga mamakin sa daga lokacin da ruwan ya sauka akan fatar jikin sa , ya ji tamkar an ƙara masa masifa ne domin gaba ɗaya tsikar jikin sa tashi tayi da ya sa dukkanin wasu jijiyoyi na jikin sai da suka taurara tare da fitowa baro-baro ,wani irin ƙullewa ya ji marar sa tayi ,

Ba shiri ya sanya tufafin sa gami da É—auro alwala ya dawo cikin tantin sa , a daddafe ya idar da sallah saboda yadda marar sa take tamkewa tana sakewa ,

Kwanciya rub da ciki yayi bayan ya sanya ɗaya hannun sa ya riƙe marar sa ,tun da yake bai taɓa tsintar kansa cikin wani hali makamancin wannan ba, a hankali ya fara jin ciwon marar yana raguwa , wani ɗan daddaɗan bacci yana fisgar sa a sakamakon lafawa da ciwon yayi tare da daɗin ƴar sassayan iskar asuba da take shigowa ta tsakankanin rumfar tantin sa ,,'

Bacci yake yi sosai da bai samu irin sa ba duk tsawon daren jiya , kafin sautin kiran wayar sa ya tashe shi , miƙa hannu yayi ya jawo wayar tare da miƙewa zaune saboda sautin kiran ya bayyana masa girma tare da muhimmancin mai kiran na sa

Allô mama oui meilleur sava,?

Daga chan ta amsa masa sava bien yaro na ya kwanan ka ? Da dama kou ?
ÆŠan jim yayi yana son faÉ—a mata yadda yake jin jikin sa saboda ya saba bayyana mata duk wata damuwar sa , sai dai kuma yanayin da yake jin yayi masa nawin faÉ—i a kan harshe musamman ma ga mahaifiyar sa *

Daga bangaren ta kuwa zuciyar ta ce ta buga a sakamakon tunowa da mummunan mafarkin da tayi akan sa asubahin daren jiya da ya haddasa mata rashin nutsuwa , da ya sa tun asubah take neman layukan sa domin ta ji lafiyar sa kou ta samu kwanciyar rai amma rashin kyaun hanyoyin sadarwa ya sa sai yanzu da safe ta cimma nasarar samun sa a wayar ,"

Yaro na yi min magana mana hankalina ya tashi ,

Da sauri ya katse ta ," da dama umma ya É—aura da tambayar ta ina merama ? Ta amsa masa da lafiya take , "
Cigaba tayi da tambayar sa lamuran da suke gudana daga wurin sa , yana bata cikakkun amsoshin da suka gaza wurin gamsar da ita , zuciyar ta ta gaza nutsuwa duk lokacin da ta tuno da mafarkin da tayi sai ta ji bata son ta daina jin sa a waya , inda da hali so take ya kasance a idanun ta cikin waÉ—annan kwanakin dan tana jin kamar wani abu marar daÉ—i zai faru da su,

duk da ta san sau dayawa mafarki bai zama gaskiya a mafi yawan lokuta daga shaiÉ—an yake , kuma ita bata da ikon kare kan ta ma bare wanin ta , ta san ko da agaban idanun ta yake , bata isa ta bashi kariya ba , illah addu'ar ta da ka iya yin tasiri akan ko ma menene , kuma duk nisan tazarar da ke tsakanin su ta san addu'ar zata isar masa ,

sanin da tayi youssouf ba sosai sosai yake tsayuwa yayi addu'a ba , shi dai mai tsayar da ibadun sa na farillah ne , bayan su sauran lokutan sa ƙorafi yake aiki ya cinye su ,wanda ita kuma hakan bai mata daɗi , ta san duk wata nasar da kariya daga wurin ubangiji ake samun su ,
Chapter 49 · 0% Book details