Sashe 178
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma ko kusa ƙudurin ta na raba su da rayuwar gidan bai sauya ba ,
Ganin ta ta mayar kan Hajja wacce take addu'o'i ganin ta idar ya sa ta gaishe ta ,
Hajja ta amsa mata tana tambayar ta yaya kwanan baƙunta ?
***
Kafin tara da rabi sun gama aikin gyara gidan da cikin sa bai wani cika datti ba sai ƙura da suka gog-goge , Hajja ta ɗaura musu girki ita kuma Yakaka ta fito sharar harabar gidan ,
Da kallo take ta bin Babbar ƙofar da take gefe tana fuskantar mai shigowa gidan wacce take da ƙofar gilashi , amma ba'a iya hango abunda ke ciki saboda tafka-tafkan labulen da suka rufe ,
Takawa tayi a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar ta tsakanin labulen da bai kai ga haɗewa ya rufe ba take iya hango cikin Babban Falon ,
Ta ɗan sake matsawa jikin ƙofar ta sa fuskar ta sosai tana leƙen cikin falon da haka kawai ta damu da son ta ga menene a ciki ?
Akan idanun ta ta ga giftawar Mutum a cikin falon , da ya sa tayi saurin ɗago fuskar ta lokaci guda tana tunanin aka ce kuma babu kowa a gidan sune ma suka buɗe gidan , kuma sun rufe tun cikin dare har kuma yanzu ma gidan a rufe yake to waye kuma ta gani ta cikin falon ko nan ɗin ba ɓangare bane na gidan ?
Sake mayar da kan ta tayi tana leƙen cikin falon bata ga kowa ba , amma ta cigaba da yawata idanun ta a ciki har zuwa wani ɗan lokaci kafin ta ji an dafa ta ta baya ,
A tsorace ta waiga , ganin Hajja ce a tsaye tana bin ta da wani jirkitatcen kallo , ya sa ta yin ajiyar zuciya ,
"Hajja akwai mutum a falon nan ko ?
Wani kallon yatsu-tsu Hajja tayi mata ,
"akwai mutum fa kike tambayata 'yar nan ? Gidan mutane kya tambayeni ko da mutum ? Nan da kike gani sashin shi Maigidan ne Baban Mama , Mijin Falmata .
"Amma kamar na ga fa mutum yana yawo a ciki Hajja ko shi É—in yana nan ne ?
"wa ya sani ko Fatalwar sa ce kika hango , saboda shi dai kam baya gari , sai dai in kuma binbinin sa kike a zuci abunda ni dai nake so da ke ɗaya ne ,
" ki kama kan ki , saboda kin ga dai yanzu a matsayin sirikin ki yake , ke kuma a matsayin Fatalwa kike a wajen sa ,
"Dan haka ki kame ki dunga nuna halin surukutaka, ki manta da mu'amalar ku ta baya da ta riga ta shuɗe muddin kina son nuna dattaku ato .
Jikin ta a sanyaye ta kama yin sharar da take da nufin yi , kalaman Hajja suna mata yawo a zuci , duk da ta sha faɗa matan hakan yafi sau shurin masaƙi daga ranar da ta ƙudurci niyyar biyo ta , amma kalaman basu taɓa huda zuciyar ta irin na yanzu ba ko me yasa ?
Ƙarfe goma direban da ya kawo su yazo , gaisawa kawai suka yi da Hajja tace yayi tafiyar sa anjima su da kan su zasu kasuwa ,
Ransa ya nuna ba haka ya so ba , amma ba yadda ya iya haka ya tafi yana muzurai .
Rochester New York
Tun bayan bayyanuwar cikin jikin Falmata laulayi ya sako ta gaba , laulayi take irin mai wahalarwa , kome ta ci amai take , ga kasala da rashin ƙarfin jiki , kusan kwance take yini , Youssouf ke yin kome na daga aikin gidan da bai cika yawa ba .
Ga ranta da yake a dagule saboda batun komawar su gida , so tayi Mama ta warke kafin komawar su wacce cikin kwanakin nan jikin nata yake yawan matsanta mata .
Sai dai duk yadda ta so Baban Mama da ya yarda ya É—age komawar su gida saboda a yiwa Mama akai tunda ga damar ta samu , ita ta amince a yi amfani da jinin abunda ke cikin ta a yi Mama aiki ,
Amma yaƙi amincewa , hankalinsa yayi gida , har saɓani suka kusa samu a ƙarshe ya ce ba zai amince ba da abunda yake cikin ta da Mama duk ɗaya suke a wajen sa , hakkin su ne ya kare lafiyar su , su duk biyun ba zai yi abunda zai iya sa abunda ke cikin ta a hatsarin da zai salwanta ba , kamar yadda ba zai so rasa Mama ba ,
Su haƙura su bar kome zuwa lokacin da za'a haifi abunda yake cikin nata ya girma zuwa munzalin da shi ko ita da kanta zata sadauƙarwa da 'yar uwar ta/shi ɓargon ta .
Falmata tayi kuka akan wannan batun , a ganin ta Baban Mama baya tausayin Mama , yaya zai ce har sai Mama ta jira shekaru kusan ishirin nan gaba tana fama da wannan ciwon ?
Wannan ya ƙara mata damuwa duk ta rame sai haske da ta ƙara yi da ƙyalli irin na mata masu ɗauke da ƙaramin ciki ,
Ana gobe tafiyar su bayan sun dawo daga ganin likitan ta , inda ya bata tsawon watanni goma nan gaba da zata sake dawowa a duba idon saboda sanar da shi batun komawar su gida da suka yi ,
Sannan babu wata sabuwar matsala da ta taso akan idanun nata sai ma cigaba da ake samu kaɗan-kaɗan ganin nata yana ɗan sake ƙarfi duk da dai har yanzu bata gani tar-tar .
Yossouf ya dubi Falmata wacce ta rungume Mama akan cikin ta suka yi lamo akan kujerar ta naɗe musu jiki da babban bargo ɗaya , duk kuwa da cewa sanyi ya ragu sosai ƙasar .
"Fatima nace ki daina É—aura Mama bissa ga cikin ki , kada ta miki ciwo ko kuwa abunda ke cikin ki .'
Ɗan murmushi tayi bata ce kome ba illa sake rungume Mama da tayi wacce take taɓa ƙailula saboda rashin jin daɗin jikinta ,
Ba tare da ya janye idanun sa daga kan su ba ya cigaba da cewa ,
"dagga mun koma gida zan kai Mama école ko doumin ta huttashe ki , ki yi fama da kan ki kadda ta kawo matsala ga Baby ,Â
Da sauri ta katse shi ,
"Baban Mama a yanayin wannan jikin na Mama zaka kai ta makaranta , da dai ka dauka mata mai koyarta darussa a gida , makaranta yara zasu doke ta ko kuwa ta yi tsalle-tsallen da zai iya kawo tashin ciwon ta , ga....
Shima katse ta yayi cikin taushin murya ,
"Fatima ciwon Mama ai bai hana karatu , baki da labarin masu ɗauke da irin cutar ta har suna kaiwa ga matakin kammala jami'a har ma suyi aikin bautama ƙasa , al'umma kouma ta ci moriyar su ?
"Mama zata tai ecole inshaAllah , ki dunga ƙarfafa mata a matsayin ki na ouwa gareta , wataƙila watarana ita ma ta zam likita ,
Ya ƙarasa zancen zuciyar sa cike sa burin son Allah ya gwada masa wannan ranar ,
"Allah ya sa Baban Mama , Allah ya raya mana Mama mu kai zuwa ga wannan ranar .
Ta amsa fuskar ta É—auke da murmushin da ta kwana biyu bata yi irin sa ba ,
***
Washegari bayan sun kammala duk wasu shirin su , sun haɗa kayan su da suke son komawa da su gida a cikin manyan Jakankunan su da suka zo da su alhalin babu kome a cikin su , a yanzu cike suke da tarin suturu , magunguna , zuwa kan kayan buƙatun su na yau da kullum da suke son tafiya da su .
Sauran tarkacen da bashi yiwuwa su kwasa Youssouf ya zubda a babbar shara , bayan sun gama tattara kome nasu ,
Youssouf ya zare katin kuÉ—in sa da ake cirar kuÉ—in ruwa da na wuta tare da gas da suke amfani da shi tsawon lokacin ,
Suka jawo jakankunan su waje , inda suka tarar da waɗanda suka basu hayan gidan suna jiran su , miƙa ƴsn mukullin gidan ya yi ,
Suka yi musaba tare da godewa juna , ya matsa kusa da Musa da Ramlat wanÉ—anda suke tsaye ,
Fuskar su cike da alhinin rabuwa da zasu yi a yau bayan ɗan takaitatcen zaman jin daɗi da mutunta juna gami da shaƙuwar da ta fara shiga tsakanin su , suka gaisa
Basu wani jinkirta ba suka shiga mota baki ɗaya da kayan su Musa ya jaa su kai tsaye zuwa Airport inda jirgin da zai sada su da ƙasar su kai tsaye daga nan harabar tashi da sauƙar jiragen sama na birnin New York zuwa harabar tashi da sauƙar jiragen sama na Niamey .
***
Ƙarfe huɗu na agogon Niger jirgin su ya dira , inda daman direban sa na musamman yana jiran sa , ba wanda ya ke kai Falmata makaranta da daukota ba wanda shine yake kai Hajja Maiduguri ,
Wannan direban sa ne musamman daga wajen aikin sa , da daman sun san da isowar sa ,
Gidan sa ya nufa da shi duk cewa Falmata ta so su zarce asibiti saboda Amai da Mama ta dunga yi tun a cikin jirgi , jikin nata ba daÉ—i sosai ,
Har cikin gidan direban sa ya shiga da motar , ya buɗe musu ƙofar motar suka fito ,
Youssouf ya riƙo hannun Falmata da ita ma ba wani jin daɗin jikinta take ba ɗauriya kawai take yi amma baki ɗaya zuciyarta hautsinawa take dan haka ne ma ta ƙi cin kome , yunwa kuwa sai sasuƙar ta take yi ,
Ya É—auki Mama a kafaÉ—ar sa wacce take kukan zafi tana son a cire mata kaya masu É—an nawin da suke jikinta saboda sauyin yanayi .
Kai tsaye suka doshi cikin gidan sojan da ya É—auko kayan su yana bin su a baya , bakin su duk É—auke da Sallama suka shiga , shiru babu wanda ya amsa musu domin babu kowa a falon .
Da shigar su falon Yossouf ya zaunar da Mama bisa kujera , gefen Falmata ta sanya hannu ta jawo Mama jikinta ,