Sashe 19
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta kawar da kai tare da tsirtar da wani mugun yawun da taji ya taru mata a baki tace ,"yakaka anya wurin nan kuwa ya dace da wajen alwala ? Gaskiya ku zo mu koma
Bata gama rufe baki ba ,"taga wata mata da goyon ƴar ta, ta zo tayi ƴar tsallaƙe ta tsallake tarin kazantar dake wurin tare da shiga ɗaya daga cikin banɗakin wajen ,"cikin ƴan dakikai kuma wata mace ta fito daga ɗayan banɗakin .
Yagana babu yadda zamu yi kin ga kowa dake nan wurin da nan É—in suke amfani , dan haka muma dole mu bi ayari .
Tana rufe baki ta saki hannun falmata gami da tattare zanen ta , ta tsallaƙa cikin dauke numfashi ta nufi bandakin ,"tare da cewa falmata ki jira ni anan kar ki motsa ",
Bayan sun idar da sallolin da ke kan su da suka yi ta a ɗanɗaryar ƙasar kan baranda ,cikin rashin wadatuwar suturar da zasu suturce jikin su kamar yadda ya kamata a yayin sallar ," duk da daman ba wani sani suke da shi sosai game da ibadar ba .
Tsumu suka yi kowaccen su cikin taÉ—in zuci ,"
Ƙarar jiniya da tayi musu kama da ta motar sojojin nan da suka ji ya dumfaro farfajiyar masaukin nasu ,shi ya firgitar da su suka miƙe ba shiri cikin ransu kuwa cike da taraddadin da me jiniyar ta sake zuwa musu a karo na biyu cikin ƙasa da sa'o'in su biyar a cikin birnin na maiduguri ?
Sai dai sabanin tunanin su a yanzu ba daga motar sojojin da suke zato bane ƙarar jiniyar take fitowa ba ," daga wasu jerun gwanon manyan bakaƙen motoci masu daukar ido tare da kyallin sabuntar dake nuni da tsadar su , karar take fitowa ",
BuÉ—e baki da hanci yakaka,da yagana suka yi suna bin motocin da kallo waÉ—anda har matukan su suka riga suka sama masu matsaya ,"
Sai dai basu kai ga sauke numfashin farin cikin da suka riƙe na ganin cewa ba waɗannan sojojin da ganin su ba alheri bane a wurin su ,suka dawo ba , idanun su suka yi arangama da jerin gwanon motocin sojojin daga baya da ma na wasu jami'an tsaron masu mabanbantan kayan sawa wadanda basu kai ga rarrabewa da banbancin su da sojojin ba ,"
Mukut ! Yakaka ta haɗiye yawun tsoron da ya cika mata zuciya fal ! Lalubar hannun ta falmata tayi cikin maƙyarkyatar murya take cewa " yakaka, yagana kun ga abun da nake faɗa muku koh ? Ni daman nasan da kyar idan ba gidan bayar da horo sojojin nan suka kawo mu ba ," ai tun daga horon yunwar da aka fara yi mana ɗazu ya ci ace kun fahimci irin kurkukun da muka shigo ," kawai ban faɗa miki bane yakaka , amma tun sanya kafafuna cikin garin maiduguri naji ajikina babu alheri cikin sa , naji cewa akwai wani babban al'amari marar daɗi da zai same mu a cikin sa ,"
Kuwwar mutane tare da dararrakin su da ya cika musu kunnuwa shi ya katse surutun da falmata take yi cikin É—imaucewa ta koma cewa "menene yakaka ? Harbi ake ? Kashe mu muma zasu yi ? Toh ku zo mu gudu mana tsayuwar me muke ?
Ki nutsu falmata ! Yagana ta furta "cikin É—an É—aga murya" a sakamakon surutun da hargowar da falmatan take yi musu cikin ruÉ—ewa ya hana ta , ta gano abun da take hasashe , ganin yadda taga fuskokin kowa a wurin ya yalwatu da fara ,"ta ko'ina bullowa jama'a suke suna tururuwa a harabar wajen ,"
Da gudu yagana ta dira daga kan baranda kafin ta waiwayo cikin tsantsar farin cikin da kamar anyi mata babban bisharara ,"yakaka falmata ga gwamna wallahi gwamna ne yazo ,gwamnan jahar borno ", kuyi sauri ku taho kar wajen tsayuwa ya cika ," daga haka ta kara da gudu kamar yadda taga sauran jama'a maza da mata suna kwasar gudun zuwa gaban dandamalin da jami'an tsaro suka kewaye ta ko'ina wanda da alama anan gwamnan yake tsaye .
Saƙare suka yi a tsaye cikin rashin sanin takamaimai halin da suke ciki na farin ciki koh saɓanin hakan , a zahiri basa jin wani farin ciki a dan saboda zuwan gwamnan musamman ma ga falmata ," wacce ta sauke boyayyar ajiyar zuciyar samun kwanciyar hankali jin ba zuwa aka yi domin azabtar da su ba kamar yadda ta zata ," sai dai ita bata wani farin ciki da zuwan gwamnan domin rashin sanin muhimmancin zuwan nasa .
A hankali yakaka ta fara jaan hannun falmata cikin cewa mu ma muje falmata muga gwamnan kuma muji bayanin sa kin ga duk mutane sun tafi .
Bayan gajeren bayanin da gwamnan ya gabatar musu cikin yaren su wanda duk na ban hakuri ne game da halin da suke ciki tare da yi musu alkawurwukan kyautata musu da ababen more rayuwa , sannan a karshe yayi musu albishirin tarin kayan abinci da suke tafe da shi , gidajen sauro , butoci da kuma bargunan rufuwa , ya kuma ƙara da albishirin za'a ƙara musu matakan kula da lafiyar su da sauran bukatun su na yau da kullum,
a karshe kuma ya basu dama wasu daga cikin su suka faɗi irin matsalolin da suke ciki a sansanin nasu , inda mafi yawan korafe-korafen nasu ya tafi akan ƙarancin abinci da ruwan shaa, uwa uba da cizon da sauro da ƙwarin gurin suke musu wanda cizon sauron yake kawo musu mummunar masassarar da har take iya kaiwa ga rasa rayuka idan ya zo da ajali musamman ga mata masu ciki da kananan yara .
Bankwana yayi musu bayan da ya basu tabbacin za'a samu sauyi daga yanzu inda ya nemi da a naÉ—a kwamiti da shuwagabanni a tsakanin su kashi-kashi domin lura da matsalolin su .
Nan take aka shiga ihu da kalmomin yabo ga gwamna da tawagar sa har zuwa lokacin da ƙurar motocin su suka bace .
Babu laifi , ziyartar da gwamna ya kawo musu sosai ta saisaita ciwukan da suke cikin rayukan al'ummar sansanin yayin da ya haifar da farin ciki a cikin zukatan kashi tamanin na cikin É—arin mutanen.
Idan aka ɗauke falmata wacce har kawo yanzu da ake kammala raba musu gidajen sauro tare da barguna, inda ake haɗa mutum biyu da gidan sauro guda bayan an damƙa musu bargunan su ɗai-ɗaya da buta ɗaya ," dukkanin su ba'a haɗa su da juna ba ,an ware su ne daban-daban yayin da aka haɗa yagana da wannan budurwar wacce ta basu kwatancen inda banɗaki yake , yakaka kuwa da wata yarinyar mace mai yara biyu ƙanana aka haɗa ta , falmata kuma da wata mata wacce take yanayi da zaurawa ,"domin ta wuce a sata sawun ƴan mata ƙanana irin su ,"kuma ita bata da ɗa ," babbar budurwa dai .
Babu yadda yakaka bata yi da wannan babbar budurwa da aka haɗa su da falmata akan tayi musu lamini ta bar musu ita da falmata gidan sauron idan ya so sai itama yakaka ta bar mata wajen ta ,"ma'ana suyi musanye wuri," saboda a zahiri ta shiga tashin hankali ganin za'a raba musu wurin kwana da ƙanwar ta ," Amma fir budurwar nan taƙi ,tace ita gaskiya baza ta iya kwana cikin gidan sauro guda tare da mai yara ba , karshe ma ta fatattaki yakaka ta kuma ce idan har ta matsa toh fa sai dai falmatan ta bita su tafi chan su ƙarata "ta bar mata gidan sauron ita ɗaya "
Da farko yakaka tayi tunanin su haƙura kawai da kwanan cikin gidan sauron su haɗu su dunga kwanan su tare, sai dai tunowa da korafe korafen da taji ɗazu sun yi da suke faɗin illar da cizon sauron yake yi da har yake iya kisa , yasa taji babu yadda zasu yi dole ta kiyaye lafiyar falmata , dan haka tana ji tana gani aka raba musu wurin kwana da ɗaki ita da ƙanwar ta .
Dare ya raba tsakiya idan banda juyi babu abun da falmata take yi gaba daya ta kasa bacci saboda tsananin takurar ta da budurwar da ake kira da "ajus" taƴi duk ta bi ta ture ta, tare da janye mata bargonta ta rufu da shi ,sakamakon sanyin damina tare da raɓa irin na tsakiyar daren yanayin damina ,"
sakamakon turo ta da ta dunga yi yasa gidan sauron nasu duk ya buɗe sauro da cinnaku masu fiffike sun samu damar shiga ciki sai faman ɗallara mata cizo suke ,"sau biyu tana yunƙurin jaan bargon ta amma sai ajus ta ɗallara mata mintsini tare da haure ta da ƙafa ,"
Lalubawa tayi ta tashi ta zauna tayi tsumu , gefe ɗaya na zuciyar ta cike taf ! da kewar mahaifan ta da ƴan uwan ta ,"kamar yadda take sake ganin daren na yau ma kamar sauran ukun da suka wuce babu mahaifiyar ta babu mahaifin ta babu ƙannen ta ," duk wani buri da take da shi na samun gamuwa da mahaifiyar ta da sauran ƴan uwan ta taji yana barin ran ta , wani sashi na ranta yana raɗa mata tare da bata tabbacin sun rabu kenan har abada," fashewa tayi da kuka dai-dai lokacin da wata gwarzuwar cinnaka ta sake mallara mata cizo a dokin wuya ,"cikin zubar hawaye take tuno irin kulawar da mahaifiyar su ke basu a irin wannan yanayin na yawaitar muggan kananan kwarin damina sam bata bari su cutar da su ,"toshe kunnuwan ta tayi da hannayen ta biyu a sakamakon rugugin hadarin da taji wanda take da tabbacin ruwan sama gaf yake da tsinkewa