Sashe 66
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai gasu sun iso ,
  A gurguje ya ansa gaisuwar su ya shiga shagon sa ya fiddo musu da jakankunan kayan su gami da tabarma mai biyu da kuma wasu robobin abinci da suke rufe guda biyu , sai jakar ruwa ɗaya , yayi musu sallama bayan ya gargaɗe su a Kan su kula da kan su ,"
Ga mamakin yakaka sai ta ga ya sauke musu jibga-jibgan labulen da aka yi da yadin tamfol duk kusurwa uku na rumfar wanda aka yi domin kare zubar ruwan sama zuwa cikin rumfar ,
kirif suka rufu daga barin idanun mutanen da suke kai kawo ba za'a san ma da mutane a ciki ba idan ba leƙawa aka yi ba , yana daga waje yayi musu sallama akan sai da safe , suka bishi da doguwar addu'a tare da godiya !
Cikin jim daÉ—in karamcin da yayi musu yakaka ta shimfiÉ—a musu tabarmar tare da kama hannun falmata ta zaunar da ita a gefen jakar kayan su daga jikin bangon shagon sai lokacin ta lura da ledar mai É—an girma da take hannun falmatan ,"
Falmata menene wannan a cikin ledar hannun ki ??
  Abincin ki ne yakaka , naga yanzu kin fi son tuwo miyar yakuwa shine na saya miki lokacin da naji baba mai kayan miya yace mai abinci ta kawo mishi , shine nima na bada kuɗi aka kawo miki , na naira ɗari da hamsin ne , ga sauran kuɗin da na samu yau ƙirga ki gani , "ta miƙa mata ledar da ta tara kudin a ciki ,
Da tarin ƙaunar ta da tausayi ta karɓi kuɗin ta kirga su naira ɗari hudu da sittin ne idan aka haɗa da kuɗin abincin da ta saya mata ya zama ɗari shidda da goma , ai kuwa lalle sun samu kuɗi ita ma ga nata naira ɗari bakwai hansin ɗin safe na abincin ta, kuɗin su sun kama dubu ɗaya da ɗari biyu da goma ,"
Falmata nima na nayi aiki na samu kuÉ—i har É—ari bakwai kin ji su ,
ta É—ora mata kuÉ—in akan hannun ta , da murna ta shafa kuÉ—in
kai yakaka amma wallahi mun ji daÉ—i kin ga sai muyi ta tara kuÉ—in da zaki dunga zuwa asibiti ana duba lafiyar yaron mu kamar yadda likita ranar ya faÉ—a ," kuma mu dunga ware ko É—ari É—aya ne kullum muna ajiyewa dan mu sayi kayan jarirai koh ?
Idon ta cike da ƙwalla ta ce
hakane falmata kin kawo shawara .
Bari na ci abincin yunwa nake ji sosai falmata , ke ma ki ci wanda mutumin nan mai kirki ya bamu ga shi har kwano biyu , É—ayan sai mu bari da safe mu ci koh ?
Ni ban jima sosai da cin abinci ba yau sau biyu na ci abinci na saya da hansin É—in safen kuma baba mai kayan miya ma ya saya min biski da miyar yakuwa naci É—azu da la'asar ,' anjima da dare kafin muyi bacci sai mu ci wannan É—in , yanzu ni sallah nake so nayi ,!
******
Dare ya tsala yakaka ta gaza yin baccin kirki daga ta fara sai ta farka, sai juyi take yi ta tattake a cikin abun rufuwar ta tayi matashi da jakar kayan ta ,
Ba kome ne ya hana ta bacci ba illa ciwon baya da kai , ga kuma matsanancin tsoron karnuka da take jiyo kukan su kurkusa da inda suke , zuciyar ta sai dakan lugude take ,
A hankali ta zira hannu ta lalubi wurin da falmata ke kwance , wayam ta ji bata nan , sake baza hannun ta tayi , ba shiri ta bankaɗa abun rufuwar ta gami da miƙewa zaune , duhu ne bakikkirin a cikin rumfar har ba'a iya ganin tafin hannun , murya ƙasa-ƙasa ta kira sunan falmata ,"
  Shiru ta ji
Da ɗan ƙarfi ta sake kiran sunan tana mai miƙewa tsaye ,
  Haske ta ga ya ratso rumfar kafin ta ga shigowar falmatan tana lalube , da sauri ta taka ta kamo ta zuwa cikin jikin ta ta riƙe , murya ƙasa-ƙasa tace
  Falmata ina kika je ? Meyasa kika fita ? Ke bakya tsoron dare ne ?
 Yakaka fitsari na ɗan je baya nan nayi ba nisa sosai ba
Meyasa baki tashe ni ba ,? Kar ki sake irin haka , ba a cikin gida muke ba a bakin kasuwa muke bakin titi cikin rumfa , babu kowa sai mu kaÉ—ai !
  Toh ta amsa mata
Daga haka suka kwanta ƙwaƙume da jikin juna ko yaya ɗayan su ya motsa ɗayan zai iya ji ,"
Asubar fari suka tashi suka yi sallah suka ɗan sake kwanciya zuwa lokacin da gari zai ƙarasa wayewa ai kuwa waɓi daddaɗan barci ya kwashe su tare da taimakon sanyin asuba ba su suka farka ba sai da hayaniyar jama'ah da ƙarar motoci ya fara yawa wuraren takwas da rabi ,
 Yakaka mun yi bacci dayawa , cewar falmata
  Mu wanke baki mu ci abincin ALLAH ya sa bai lalace ba , ilai kuwa suna buɗe robar warin lalatatcen wake da shinkafa da miyar ya bigi hancin su ba shiri suka maida murfin ,
Bari na fita na sayo mana abin karyawa me zaki ci ? Fanke ko ƙosai ? Ko doya ko masa ?
Ni kawai duk abinda zaki ci yakaka , ki nuna min wurin da zanje na zubar da abincin nan na wanke masa kwanukan ?
Kwanci tashi suka yi kwanaki a bakin kasuwa suna gudanar da al'amuran su cikin jin dadi , ƴanci tare da walwala , sosai rayuwar da suke yi a bakin kasuwa ta fiye musu duk wata rayuwar da suka taɓa yi a cikin birnin maiduguri daɗi da kwanciyar hankali , zasu ci su sha kuma su adana ƴan kuɗaɗen su , babu ƙyara babu tsangwama ,
Ka'in da na'in yakaka ta kama aikatau ɗin ta ta riƙe kullum a chan take yini tana aiki chan take cin abincin rana , sai yamma lis take komawa gida , tayi wankan ta fes a banɗakin wurin aikin ta , a hanya zata ɗan saya musu ƴan kayan gwari da ake yayin su lokacin , karas ,lemo ,cashut da sauran su ,
Falmata kuwa har ta gane hanya daga wurin barar ta zuwa Æ´ar rumfar kwanan su , dan haka ta daina jiran yakaka ta zo ta mayar ta , daga ta ji kasuwa ta fara alamun watsewa sai ita ma ta tafi bakin rumfar ta jira zuwan yakaka , a hankali har suka fara sabo da jama'ar kewayen wurin ,
Yau an tashi garin a É—an hargitse sakamakon kwana da aka yi ana É—auki ba daÉ—i da Æ´an tawayen boko haram da suke neman shigowa garin ta karfi ta wani yanki , sai dai basu samu nasara ba dakarun soji sun tarwatsa su wanda hakan ya jaa dayawa daga cikin su sun fantsama cikin gari da hakan kuma yake babbar barazana ga rayukan al'umma .
 Saboda ɗaukar mataki sai soji suka fantsama cikin gari , tare da sanya dokar hana zirga-zirgan motoci akan manyan titunan garin , kasuwar kan ta yau ba'a buɗe ta ba duk inda ka bi motocin soji ne suke kai kawo ,
Jugum-jugum falmata da yakaka suka yi , su sam basa ƙaunar wannan jiniyar ta motar sojoji , tsinka musu zuciya take ta tada musu hankula kamar yadda ya faru a yanzu tun safe sun gaza ko cin abinci sai faman wuri-wuri suke , ko ƙwaƙwarar magana sun gagara yi da junan su , illa hannun su da yake cikin na juna , lokaci zuwa lokaci yakaka tana ɗan leƙawa ta tsaƙanin labulen rumfar su tana ganin yadda garin yake shal tamkar an share .
Sun kwashe tsawon lokaci a haka , har zuwa lokacin da suka ji an kamo wasu gungun mutane an wuce da su ana ta dukan su ,
Basa fahimtar maganganun da suke tashi a wurin illa dai suna jin ana yawan ambaton kalmar boko haram , boko haram , boko haram !
Yakaka ta so leƙawa ta ga ko su waye ,? Amma sai ta ji falmata ta sake damƙe mata hannu , ƙasa ƙasa ta ji tace
  Yakaka kar ki leƙa , tsoro nake ji , zuciya ta bugawa take , yakaka mu yi addu'a kar su gan mu su kashe mu .
Wucewar mutanen bai fi da mintoci biyar ba suka ji ƙarar fashewar bam da matuƙar ƙarfi har sai da rumfar da suke ciki ta girgiza ,
Harbe harben bindigogi ya biyo bayan tashin bam É—in tare da guje -guje har ta gaban rumfar su suke jin takun gudun mutane tare da wucewar harsashi ,"
Iyakacin ruÉ—ani tare da tashin hankali sun shiga kuka suke yi suna tsaye charko charko cikin rumfar ,"
Suna nan tsaye falmata ta ji wani ƙaƙƙarfan abu ya bugi kafaɗar ta ya wuce wanda sai da ya sa tayi baya da karfi ta bugu da jikin kofar shagon kafin ta silale ƙasa , cikin wani irin azabar raɗaɗi da take ji yana gauraya illahirin jikin ta takamaimai bata san ina ne yake mata ciwo ba ,
a razane yakaka ta jiyo jin yadda hannun falmata ya kufce daga cikin nata , abun da tayi arba da shi ya sa zuciyar ta ta tsaya da bugawa , bata san lokacin da ta zube a ƙasa ba tare da tallafo falmata wacce jini ke malala daga jikin ta , idanun ta suna rufuwa su buɗu da kan su , jikin ta kuwa babu inda baya rawa ,.'
 Falmataaa
ta kira sunan ta da wata irin murya tamkar ba tata ba , wani irin ihu ta kurma lokacin da ta fahimci abun da ya faru ,.......!
  Masha Allah ina gaida masoyan littafin mafari a duk inda suke !
Vote
Share
Comments
 Â
 Â
 Â
[6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
22