Sashe 27
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
   Kai ina bazai yiwu ba malama waɗannan sun yi girma da hawa kan inji a jere su uku rus ,
     ya karasa zancen yana me jifan su yakaka da kallon banza wadanda suka yi tsilli tsilli a tsaye cike da taraddadin ganin samu da rashi ,sanin cewar idan aka ƙi ɗaukar su toh fa babu su babu tafiya dole su koma cikin sansanin su .
   Tsalle konduktan yayi ya ɗale motar gami da bubbuga murfin tare da cewa ",Muje oga,"
   Tsaya tsaya nima zan sauka tun da baza ka ɗauke mu tare da ƴan uwana ba ," Burki direban motar ya jaa lokaci guda ya juyo cikin hargagi yake tambayar me ya faru ne ?
   Konducto yayi masa bayani ," sake tambaya yayi akwai sarari ne akan injin ,"
   Akwai sarari oga sai dai sun yi girma sosai mutanen da ke kan sit zasu takura sosai ,"
   Wani banzan kallo direban ya wurga masa da jajayen idon sa ,"
  Ganin hakan ya sa da sauri konducton ya sauka gami da buɗe motar , yayi wa su yakaka alamun kira da hannun sa saboda har motar ta ɗan gifta ,"
     Miƙo kuɗin ku
    Cewar karen motar lokacin da direba ya daidaita motar sa akan titi
  Da sauri kolo ta miƙa masa tsohuwar naira ɗarin da ta gama shan wahala a hannuwan jama'a
  Â
     Azabar zafin inji da zafin ranar da motar ta ɗauka suka haɗu suka sa su yakaka , falmata da yagana haɗa gumi kirshiɓ suna ta ɗiga , yayin da suka kasa zama wuri ɗaya akan injin sai mutsu-mutsu suke suna jin zafin ƙunar da injin motar yake musu a ɗuwaiwai , uwa uba yadda suka takura suka cure guri guda kamar "kifayen gongon" gefe guda ga warin da konducton yake wanda ya buɗe hannayen sa ya tokare ɗaya hannun dai-dai fuskar falmata wari da tsamin hammatar sa na barazanar sanya su haraswa ,"
   Bayan tsawon lokacin da bai kamata ace sun yi shi ba daga tsakanin sansanin su zuwa bakin kasuwar , amma a sakamakon rashin kyaun motar ,tsufan ta da kuma tsayawa a sauke fasinja a ɗau wasu a hanya ,ya sa suka kusan shafe mintuna arba'in a kan hanyar da bai fi suyi mintoci goma zuwa sha biyar ba , "
    Cikin jigata suka sauko daga cikin motar , fuskar kowaccen su na nuna wahalar da ta sha a yayin tafiyar ,"
  Yawatawa da idanun su yakaka da yagana suke yi cikin mamakin ganin yawan jama'ar da suke ta hada-hadar su a wurin duk kuwa da cewa hantsi ne bai wuce karfe tara da rabi zuwa goma na safiya ba ,"
  Toh ku zo mu tsallaka titi kun ga chan ita ce kasuwar monday market maiduguri ( ita ce babbar kasuwar da take ci a kullum cikin birnin na maiduguri )
     kolo ke yi musu wannan bayanin .
Ba ƙaramin ɗauki ba daɗi aka yi cikin turƙa-turƙa kafin su yakaka suka iya tsallaka babban titin na Ahmadu bello da yake daura da kasuwar ta monday market ba ,"
Â
         BAYAN AWA ƊAYA
Duk wani zagaye sun gama shi amma basu yi dacen samun gurin da zasu yi aiki ba a zagayen har ma da ainahin cikin kasuwar , kama tun daga kan masu tuwo-tuwon da suke ciki da wajen kasuwar har zuwa kan goge-goge koh jiran shago , hasalima wurare da dama da suka je korar kare aka yi mu su ,"
 Yagana , yakaka , kun dai ga yadda aiki ya gagara samuwa a gare ku a cikin kasuwa , hakan ya sa ya zama dole ku shiga cikin unguwanni ku kutsa koh gida-gida da wuraren sayar da abinci na cikin gari koh Allah zai sa ku dace , ni yanzu gaskiya rana ta riga ta ɗaga aƙalla yanzu sha ɗaya da rabi ta kusa kun ga na riga na makara zuwa gidan aiki na , duk da dai cewa daga nan zuwa cikin unguwar da nake aikin babu nisa amma yakamata ace tun tuni ina bakin aiki kamar yadda na saba , saboda haka ni zan tafi idan ya so anjima da yamma mu haɗu a tasha inda mota ta sauke mu ɗazu , amma kafin nan ita falmata yakamata ta samu wurin zama domin yin barar ta domin kuwa babu inda ya kai bakin kasuwa samun sadakha , dan haka mu matsa daga chan wurin gefen bankin chan ta tsaya ko ta zauna a wurin har zuwa lokacin da zaku dawo , ina mai tabbatar muku da zata samu kuɗaɗe sosai ,
      Duk kalma guda da take fitowa daga bakin kolo dai-dai take da ƙaruwar luguden da zukatan su yagana ke yi , wannan fa shi ake kira " anyi gudun gara an tadda zago " toh su kuwa ina zasu fuskanta cikin wannan turmutsutsu da taron jama'ah ?
Ta ina zasu fara dilmiyar da kan su cikin gari alhalin basu da tabbacin zasu iya gane hanyar da zata dawo da su nan mahaÉ—ar ta su , wanda a zahiri cikin zagayen awa É—aya jal da kolo tayi da su a tsukin kasuwar , a halin yanzu koh tashar da mota ta sauke su baza su iya komawa ba saboda kan su ya riga ya juye , ina ga batun kutsawa cikin gari cikin unguwanni , ai wannan zancen ma bai taso ba ,"
 Kusan a tare su ukun suka haɗa baki gurin fara magana ," amma sai yakaka da falmata suka saurara domin bawa yagana damar faɗin abun da ke nata bakin duba da cewa ta fisu kusanci da kolo ɗin ,"
  Kolo mun gode sosai da dukkanin dawainiyar da kika yi mana amma a gaskiya daga ni har yakaka babu wacce zata iya tunkarar cikin garin da nufin neman aiki ba domin kome ba kuwa dan gudun bacewa mu rasa hanyar komawa a matsayin mu na baki ," jaan numfashi tayi lokaci daÆ´a tana mai sake marairaicewa , dan Allah kolo ki idasa taimakon da kika yi niyyar yi mana ki yadda mu biki zuwa unguwar da kike yin naki aikin idan ya so sai mu shiga gidajen cikin unguwar mu nemi aikin koh Allah zai sa mu dace ?Â
  Ɗan jim kolo tayi cikin nazari a zahiri bata son su yakaka su bita su ga irin aikin da take yi sanin cewa ta boye musu gaskiyar aikin nata , amma ita sosai take tausayawa musu musamman yagana wacce take da wani boyayyen buri akan ta , "
    Toh shikenan ku biyo ni amma da sharaɗi ," kamar yadda kuka ce kun fito neman aiki ne dan haka baku da wani zaɓi akan irin aikin da zaku yi ,"domin unguwar da nake aikina ta sha banban da sauran unguwanni ," nan ne gaba kaɗan tsallaken titin nan ta karashe zancen tana yi musu nuni da wata hanya da ta gangara kwari ta miƙe sosai daga gaban su ,"
 Ke kuma ta juya ga falmata muje ki zauna akan dutsen chan ki ɓuɗe hannun ki ki fara bara , kar ki motsa koh nan da chan zuwa yamma zamu dawo mu same ki ,",
Â
    Cikin rashin kuzari yakaka take taku domin raka falmata wurin zaman ta inda gefen titi ne daf da bakin kwalta kuma ta baya jikin bangon kasuwa ne da yake kewaye da shagunan saide-saide, gefe da gefe duk masu saide-saide ne na kayayyaki iri daban-daban wasu sun yi kashi-kashi akan buhu da algarara wasu a wulbaro wasu akan tire ,wasu kuwa ƴan tebura ne da su ,yayin da gaba kaɗan kuma wani babban gini ne mai kama da ma'aikata ( banki ) ,"
   Dai-dai gefen wani ɗan tsoho mai sayar da kayan gwari suka cewa falmata ta zauna kan wani ɗan dutse ,'
    Cikin nutsuwar da take halittar ta ta laluba ta ɗosana duwawun ta ,",
  Â
Durkusawa yakaka tayi akan guwowin ta gami da kamo hannunwan falmatan tace ,"
    Falmata dan Allah ki kula da kan ki kin ga inda muka ajiye ki ɗin nan ki zauna kar ki motsa koh nan da chan ,
     "ɗaga kan ta tayi ta dubi sama taga akwai rangwamen hasken rana sakamakon manyan giza-gizan da suke yawo suna kare ranar ,
" idan kin ji kishirwa ga wannan",
ta kunce bakin zanen ta ta ciro wata tsohuwar naira goma wacce ita falmata bata san inda ta samu ba ,"
ki sayi ruwa da shi ki sha idan kuma Allah ya sa kin samu sadakha idan kin ji me tallar abun sayarwa ki sayi wani abu ki ci ,
sake damƙe hannun falmatan tayi tana me jinjina hannunwan su da suke haɗe da na juna ,
falmata kar ki je koh ina ki jira ni dan Allah , kuma ki kula min da kan ki ,"
    Yakaka ni fa sauri nake da Allah ki taso mu tafi ,"
cewar kolo cikin gundura da doguwar maganar da yakakan take yi da ƙanwar ta ta , wanda ita da yagana ba jin abun da take faɗa suke ba sakamakon ƙasa da muryar ta da tayi ,ga kuma hayaniyar motoci da ta muryoyin jama'ah ,"
Yunƙurawa tayi ta mike tare da cewa '" yi hakuri kolo mu tafi ,
     idanun ta akan fuskar falmatan wanda a zuwa yanzu ta kasa fahimtar a wanne yanayi zuciyar falmatan ke ciki ,"