← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 269

Sashe 181

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun tsagaita daga dariya , Hajja ta kallesu tana nazarin tarin ingantatciyar ƙaunar da ke ga junan su , a hangen ta irin na manya ta fuskanci kowaccen su tana ƙokarin binne damuwar ta ne daga 'yar uwarta saboda zallar ƙaunar da suke yiwa juna , idan kuwa hakane Madallah da irin wannan ƙauna ta tsakani da Allah ,

Miƙewa tayi tare da cewa ,

"Yakaka yayar Falmata zo muje daga ciki ki ga irin 'Ya'yan itatuwan su na nan Niger ba irin namu na Nigeria ba ,

"Uwarɗakina Falmata a kaiwa Mama abincin kadda yunwa tayi mata lahani  , tana sashin Baban ta ai kin san hanyar ko ? Kin kuma san kitchen ɗin ga shi nan ,

"nasan Hanya Hajja ,

Falmata ta furta hakan tana jin son ta tafi ga Mijinta ta ga halin da yake ciki , sannan ta fuskance shi ko zata iya ganin wani sauyi a tare da shi na daga zallar ƙaunar da yake nuna mata muddin suna tare , a sanadin bayyanar Yakaka ?

Yakaka bata ce ƙala ba ta bi bayan Hajja , har ta ɗan gifta Falmata , sai ta ji ta ƙira sunan ta ,

"Yakaka nyei

Juyowa tayi fuskarta da Murmushi

"Na'am Falmatan nyei

"Yanzu zan zo da Mama tayi miki hira duk da bata da lafiya sosai , amma ta iya hira sosai , zan kawo miki ita .

Murmushi kawai Yakaka tayi ta juya tana ƙarasa barin wajen ,

Suna shiga É—akin ta cewa Hajja ,

"Hajja ina 'ya'yan itatuwan ? Mu ga irin su ?

Kallon tsakar ido Hajja ta yi mata ,

"Yo ina kuwa wasu 'ya'yan itatuwa nan ? Kin tsare yarinya kin hana ta kaiwa mijinta tattattun 'ya'yan itatuwa tayi aikin lada ubangiji ya samar mata da lambun 'ya'yan itatuwa a Aljanna , ke haka ake yi yanzu tsakani da Allah ? Haba Babba uwar Mama .

Kallon Mamaki Yakaka tayi mata , ta samu waje ta zauna daga gefen gadon dake É—akin

"kenan Hajja dai ba gaskiya kika faÉ—a min ba wayo kika min dai ko ?

Hajja bata dube ta ba ta fara ninke gyalen ta , ta bata amsa da

" to kuma dai , karo ɗaya ai ko da ƙwai da dutse a yi sa .

Shiru Yakaka tayi bata ce kome ba , cikin ranta damuwarta ce ta dawo sabuwa fil akwai wani alamu da ta hango tare da Falmata wanda bata fatan tabbatuwar sa ,

Falmata bayan ta jera abincin su da ta tarar a rurrufe cikin mazubi , sai ta ɗauka ta nufi sashin Youssouf da ta san yana ta harabar gidan duk kuwa da cewar bata taɓa zuwa ba , sannu-sannu take tafiya saboda duhun dare da ya fara shigowa daf ake da ƙiran sallar Magariba ,  tare da taimakon hasken fititulun da suke girke a harabar gidan da suka kunna kan su , ta iso Bakin babar ƙofar ta tsaya tayi sallama ,

daga ciki Youssouf wanda tuntuni yake kai kawo a cikin falon ya taho da saurin sa jin muryar ta ya buɗe mata ƙofar

Tunda ta shigo falon Biyamuradi yake binta da kallo mai wuyar fassara , so yake ya tantance yanayin da take ciki , amma ya gaza gano wata alama, maimakon haka sai ya shagaltu wajen kallon tsarin kyakkyawan jikin ta da take sanye da doguwar rigar roba da ta bi jikin ta lafe , koyaya ta motsa sai wani sashi na jikinta ya É—au hankalinsa .

gefe guda Mamakin kansa yake yi yadda yarinya karama take mamaye tunaninsa a duk lokacin da suke tare ko ya koma gida. Akwai wani abu game da Fatima Zahra da ya kasa fasaltawa a ransa da a farko yake yawan sakawa a ransa cewa saboda irin kulawar da take yiwa 'yarsa ne.

Sai dai zuwa yanzu ya hiƙaƙancewa kansa cewa ƙaunar Fatima ɗarsuwa tayi a cikin ransa tun a ranar da ya soma ganinta , alhalin lokacin bai san cewa ma zata zam mariƙiyar ɗiyar sa ba .

Akan É—an teburin dake tsakiyar falon ta ajiye farantin hannunta wurin da yake zaune ta waiga , cikin kwantatciyar murya tace

"ga abinci".

Shiru taji kamar babu kowa waigawa tayi sai dai duhun da yake falon tare da rashin ƙarfin ganin ta sun hana ta damar hango shi , wanda yana sane ya rinka tafiya a hankali ,

Ji tayi kamar abu na nenam rufeta ta baya ta dan ja jikinta kadan sai kawai taji tayi karo da mutum. Gabanta ne yayi wata irin faduwa ta rikice tana neman hanyar barin wurin saboda tsintar kanta kawai tayi da kasa sakewa da shi yadda suka saba ,  shi kuma yaki matsawa sai ma hannuwa da ya saka ya zagaye kunkumin ta tare da haɗa bayanta sosai da ƙirjinsa

"Hankali Zahra" yace da wata irin murya a daidai kunnenta har tana jin saukar numfashinsa.

"Uhmmm zan wuce ka matsa" ta hado kalaman ta furta a hankali.

"Baki zuba min abincin ba zaki tafi?" Ya ce yana karewa kyakkyawar fuskarta kallo, bayan ya juyo da ita ya kamata suka zauna ,

Turo baki tayi tana jin kanta a takure 

"ni da kasan bana gani sosai idan dare yayi ?" kuma ai kasan ban iya zuba abinci ba .

Ya dage gira daya "yau kuma? Na dauka Zahra ta iya komai ashe da sauranta tunda bata iya zubawa miji abinci ba." Ya sake matsawa kusa da ita daga zaunen da suke ,

Sai dai bai bari jikinsu ya hadu ba saboda ko kadan bai yarda zai iya mallakar kansa ba a yadda yake ji ba , saboda shi da kansa buƙatar inda zai sanya kansa a rarrashe shi yake ,

da kuma ya tabbata Fatiman tasa a wannan gaɓar bata isa bashi kulawar da yake so ba , 

"gashi yau da hannunki nake so ki bani"

Yace mata yana murza ƴan yatsunta da ya riƙe cikin hannunsa

Yana kallon yadda idanunta suka kara girma kirjinta yana hawa da sauka cikin sauri da firgicin da bai san dalilin samuwar sa ba a dai-dai lokacin ,

"me zan baka?"

Tace muryar ta na É—an rawa ,

"Abinci mana yadda kike bawa Mama"

Bata san lokacin da tace "kai alanguro Yarima" cikin wani irin amon murya mai nuni da tsoro da mamaki ba.

Murmushi yayi , tare da kai hannunta bakin sa ya sumbata ,

  "me kika ce ? Aina kika ji wannan sunan ? Sake ƙira muji kamar naji kince wata kalma ta daban me kalmar ke nufi ?

  Shiru tayi tana murmushi ,

"to shikenan idan baza ki zuba min ba  , bakya ƙara fita a ɗakin nan sai gobe ,

Bai rufe baki ba ta laluba ta É—au farantin ,

Tana turo baki ta zuba abincin tana faman kunkuni "yaushe kaji nace ba zan baka ba to?"

"Afuwan nayi tunanin kin fada a zuciyarki ne"

ta dauki cokali ta ciko shi taf "bude" tace kamar tana magana da baby.

Cokalin ya kalla a tsorace "duk wannan a bakina Fatima?"

Tayi murmushin keta "ba irin na Mama kake so ba? Haka nake bata"

"Amma ni da hannu nake so"

Tunanin yadda za ta tsere takeyi ta ajiye ta diba da hannunta tayi sama dashi tana laluben bakinsa,Hannu taji irin na mazan da suke gwagwarmayar yau da gobe ya rike tsintsiyar hannunta

a hankali ya kai bakinsa ya ci kadan sai da ya hadiye ya kara sai a karo na uku taji yatsunta gabadaya cikin bakinsa. Ita kanta bata san yanayin da ta tsinci kanta ba bare kuma shi uban gayyar da yake jin inama bakin tsiwar ya samu haka ba yatsunta ba kawai,

"Ashh Alangubro zaka cinye min yatsu ne ?

" da zan iya haÉ—iye ki ma baki É—aya da na haÉ—iye ki Fatima , da kuma hakan shine kaÉ—ai zai fiddani daga zullumi

Bata ce kome ba sai murmushi kaɗan da tayi , cikin ran ta tana aiyana , "ina ma da zata iya shigewa cikin jikinsa ta fake wataƙila da rabuwar su baza ta kasance ba ,

Cigaba tayi da ciyar da shi abincin , kafin ta ji ya riƙe hannun ta ,

"na ƙoshi Fatima , buɗe bakin ki na baku ke da Baby ,

Bata musa ba ta buɗe baki ya shiga ciyar da ita , ita ma kaɗan ta ci tace ta ƙoshi ,

"kaɗan kika ci Fatima , ki ƙara saboda Baby ,,

"Na ƙoshi , ai kaima kaɗan ka ci ,

Bai ce kome ba , sai jawo ta da yayi jikinsa ya haɗe ta da ƙirjinsa tsam-tsam ,

Cikin kunnen ta yace

" ina sonki Fatima Zahra ,

Lumshe idanun ta tayi , wasu siraran hawayen da bata san dalilin sauƙar su takamaimai ba suka silmiyo suka sauƙa a fatar ƙirjinsa , runtse ido yayi yana jin tausayin ta mai tarin yawa yana mamayarsa a wajen sa babu abar tausayi sama da ita ,

Sun É—an yi mintoci kaÉ—an a haka kafin ya zare ta daga jikin sa , "Fatima , magarib tayi muyi Sallah ,

****

Bayan sun idar da Sallah sun yi addu'o'i shiru ne ya ratsa tsakani kafin Falmata tace

" ina so na shiga wajen Yakaka ,

Shiru Youssouf ya yi bai ce ƙala ba , saboda har ga Allah bai son su dunga kaɗaicewa saboda bai san da wacce manufa Yakaka take tafe ba , sai dai koma menene yana fatan kar Allah ya bata damar fayyacewa Fatima kome .

Jin yayi shiru ya sa Falmata sake cewa

"zance wajen Yakaka muyi hira kaÉ—an , ga shi Mama ma tana ta bacci ba abun na tayar da ita ba ta je Maman ta ta gan ta ,

"ki rabu da ita , mu je na raki ki kiyi mousu sallama ki dawo nan ki kwanta ki huta , gobe kun yi hira ,

Youssouf yace haka yana kama hannun Falmata cikin zuciyar sa dan babu yadda zai yi ne , da ba zai bari ta fita ba ,

Tare suka shiga har falon , basa nan dan haka Falmata ta ƙarasa ƙofar ɗakin Hajja , shi kuma ya dakata daga tsakiyar Falon ,

Ƙwanƙwasa ƙofar tayi ,

"Yakaka , na dawo .
Chapter 181 · 0% Book details