← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 264 OF 269

Sashe 264

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kar kiyi zaton ke ce rai ta farko da na kashe a kan Hamza ke ce ta uku na farkon jariri ne lokacin da aka bani tabbacin idan har ba'a yi mummunan aikin da aka raba tsakanin jaririya da uwar ta ba to babu shakka uwar jaririyar ita ce matar da Hamza zai aura ba ni ba idan kuwa har aka raba tsakanin su za'a kaÉ—a uwar wani waje mai nisan gaske ni kuma cikin shekarar Hamza zai aureni hakan ne kuma ya kasance .

"Na sha wahala kafin na samu wani ɓangare na daga zuciyar Hamza wanda a ƙarshe sai da aka min aikin da aka kashe wani Mijin da zuciyar sa ta mutu a ƙauna matar sa a can ƙasar india bayan duk na sha wannan wahalar ina zaman daɗi da Mijina za ki ratso rayuwar mu ?

"Ya kike tunanin ba za ki zama ta uku ba a cikin jerin Mutanen da za su mutu ba ? Dole ki Mutu dole ki zama mutum ta farko da zan kashe da hannu na akan Hamza .

Wasu kauraran hawaye ne suka zubo mata kafin ta cigaba da cewa "kin ga laifi na ne ? Ki duba yadda na lalata jikina saboda kawai na burge Hamza na lalata Mahaifata saboda kawai muyi rayuwar hutu da Hamza bana son ko 'ya'yan cikina su ratsa tsakanin mu .

Juyowa tayi ta wani irin fisgo Yakaka da daman tuni alhinin Mutuwa ya safko mata bata da wani sauran ƙarfi .

Ta gwara kan ta da bango kafin tayi majaujawa da ita a tsakiyar ɗakin ta yasar da ita da wani azabar ciwo ya sarƙe Yakaka yasa ta saki ihun da ya daki dodon kunne Falmata wacce duk take jin abunda Sofi ke cewa..

Ita ma ihun ta saka da ya amsa sashin ta gaba ɗaya da ƙarfi ta miƙe tsaye lokacin da take sakin wayar hannun ta ta faɗi ƙasa tunanin ta yana tabbatar mata da cewa Sofi ta kashe mata Yakaka a yau .

Da gudu Hajja da wasu bayun ta biyu suka shigo waɗan da ihun ta ya je har kunnen su Hajja tana shigowa ta gan ta a durƙushe tana murƙususun ciwo tare da ihun ƙiran sunan Allah da na Yakaka cewa take "Yakaka na ta mutu Sofi ta kashe Yakaka dan Allah ku kaini Nigeria .

Hajja wacce kallo ɗaya ta yiwa Falmata ta ga alamun haihuwa a tare da ita ita kuma cewa take "To Alhamdulillah abun yau yazo kenan fatan mu Allah ya raba lafiya sannu Uwarɗakina sannu kin ji daure kowacce Mace da haka ta zama uwa daina iface-ifacen nan ikon Allah ke kuma taki naƙudar da ƙiran sunan 'yar uwar ki ta zo miki o wannan ƙauna ta ku ta girmama .

Kafin mintoci goma sha biyar labari ya je wa Hajiya Umma kan cewa Falmata na naƙuda nan take ita da kan ta ta taso zuwa sashin .

Ƙarƙashin Umarnin Sarki aka fita da ita zuwa asibiti da kawo lokacin Falmata ta daina surutai saboda ganin idon Hajiya Umma sai dai ruwan hawaye da suka ƙi daina zuba mata a zahiri ciwon da take ji a cikin ranta na rashin 'yar uwar ta yafi ciwon da take ji a sassan jikin ta na buɗuwar ƙasusuwan ta sakamakon abunda yake cikin ta da ya shiryawa fitowa duniya a yau .

***

Ciwon da ya turnuƙe Yakaka daga ƙasa ya riƙe mata mara shi yasa ta kasa yin wani yunƙuri na kwatar kanta har lokacin da Sofi ta ƙaraso inda ta jefar da ita tana mata wannan kallon da salon murmushin da zuwa yanzu ta san manufar ta ta kuma gane dalilin da yasa take jin matsanancin tsoron Sofi ashe dan ta ita ce ajalin ta

Ɗaga wukar Sofi tayi da iyakar ƙarfin ta ganin  haka ya sa Yakaka kare fuskar ta da tafukan ta biyu tana maimaita kalmar shahada a cikin ran ta kamar yadda take jin kome da ya shafi duniya yana shafewa daga ƙwaƙwalwar ta lahira na maye gurbin sa .

duhun da yake da alaƙa da tsanantar gudun jinin jikin ta da aikin da ya wuce misali da zuciyar ta ke yi ya safko yana mamaye ganin ta ya koma dusu-dusu take iya hango abunda yake faruwa ta tsakanin yatsun hannunta

Ba zata iya tantance mafarki ne ko ido biyu ba lokacin da ta ga kamar an É—aga Sofi anyi cilli da ita gefe .

Doctor Hamza take Iya gani ya gifta ya É—ago Sofi da ta faÉ—i a gefe.

Mari ya shiga ba ta a fuskar ta dama da hagu kafin ya ji cewa marin bai gamsar da shi ba ya shiga ƙoƙarin zare belt ɗin dake kunkumin sa da muryar da ba tayi kama da ta shi ba yake cewa "Sofiya ashe haka kike ? Haka kika min Sofiya ? Haka za ki min ?  Kisa kike ?  daman Sofiya kisa kike yi ? .

Ta ko'ina yake zuba mata belt É—in a jikin ta kafin ya fisge ta su ka fice daga É—akin ya tunkuÉ—a ta ta bugu da bango jikin ta gaba É—aya ya farfashe yayi shatin belt .

Ragwab ya zauna akan kujera kamar kuma ya zauna akan ƙaya sai ya sake miƙewa gaban ta ya dawo ya tsaya yana kama goshin sa da hannun sa ɗaya muryar sa na karkarwa yace "Sofiya duk abunda na ji kina faɗa da bakin ki gaskiya ne ? Gaskiya ne ? Kin yi kisan kai kina kuma yunƙurin sake yin wani a cikin gidana duk kuma a dalilina ?

Fisgota ya sake yi a inda take yashe tana wani wuri-wuri da ido ko ɗigon ƙwalla babu a idanun ta illa wani irin ƙuna da ran ta ke yi ganin kome take kamar a mafarki .

Fisge jikin ta tayi muryar ta a hargitse tana sarƙewa bata cikin hayyacin ta tace " Duk abunda ka ji nace na aikata a ta dalilin ka nayi kuma a shirye nake da nayi abunda yafi haka Wallahi ni Sofiya a shirye nake da na kashe kowa akan ka , idan kuma aka nemi raba ni da kai ta ƙarfi zamu Mutu tare ni da kai zan kashe ka na kashe kaina .....'

Wani marin ya daÉ—a bata kafin ya fisgota Yana tunkuÉ—a ta hanyar barin gidan yake cewa ,

"Na sake ki Sofiya Ni Hamza na sake ki saki Uku ki fita daga gidana kar ki sake nuna min fuskar ki har abada na tsane ki .

Chak! Sofi ta tsaya ta tirje taƙi tafiya lokacin da kalmomin sa ke mata amsa kuwwa a kunnuwan ta suna zama kamar ɗigon ruwan narkakkiyar dalma a kogon kunnen ta .

Zata silale ƙasa ya ɗago ta da ƙarfi ya ƙarasa tunkuɗa ta waje ya rufo ƙofa a fuskar ta da har sai da ƙofar ta bugi bakin ta ya fashe .

Wani ihu tayi ta shiga buga ƙofar kamar zata ɓalla da yasa makofta fara leƙowa wasu ma daga sama suke buɗe windows suna leƙen ta .

Lokacin da ta fahimci ta zama mahaukaciya sai ta tashi da gudu ta nufi bakin titi ta tare taxi .

Tana zama ta faɗi inda zai kai ta kafin ta cigaba da Sambatu cewa take " wallahi ban saku ba Hamza ƙarya kake ni da kai mutu ka raba ahaf ai daga aikin karnataka ya fara ci nan da gobe ma zan dawo gidana Kashe Yakaka kuma ban fasa ba wallahi sai na kashe ta wallahi sai ta mutu..

Ƙiiii mai taxi ya ci birki abinda kawai ya iya cewa shine "Hajiya Dan Allah sauƙa na fasa yin Area da kika faɗa .

Haka ta sauƙa bayan ta cusa masa zagin rashin tarbiya da turanci shi kuwa ya jaa motar sa da ƙarfi ya buɗa mata ƙura '

Haka ta taka da ƙafa tana tafe tana surutai a dai-dai lokacin ba wanda zai gan ta ba tare da ya mata ganin mashahuriyar Mahaukaciya ba .

***

Lokacin da Doctor Hamza ya koma É—aki inda ya bar Yakaka anan ya tarar da ita yana share guntun hawayen idanun sa ya É—ago ta ya rungume ta tsam a jikin sa yana jin yadda bugun zuciyar ta ke sassarfa da yasan hakan hatsari ne ga lafiyar abinda ke cikin ta .

Nan take ya fara ƙoƙarin bata agajin gaugawa sai dai bisa tilas ya shirya ta suka nufi asibiti saboda fahimta da yayi cewa dole abinda ke cikin ta da bai yi ƙwari ba sai ya fita saboda bakin mahaifar ya riga ya buɗe jini ya fara sauƙa.

A can babban asibiti na ƙasa da yake aiki suka mata abinda duk ya dace kafin a mata allurar bacci na ɗan wani gajeran lokaci da ana sa ran idan ta farka firgicin da take ciki ya bar ta .

Zama yayi akan kujera yana riƙe da hannun ta ya zubawa fuskar ta ido a can cikin ransa kuwa lamarin Sofi ke daɗa sanya shi a ruɗani a bayan kowacce daƙiƙa yadda yake jin kome kamar a mafarki

Wai Sofi ta aikata duk abubuwan da ta lissafa da bakin ta.? Ga kuma ƙwaƙƙwarar shaida nan tana yunƙurin kashe masa Mata da ba domin Allah ya kawo shi ba da babu shakka Wafaa bata raye yanzu a duniya .

Sake runtse hannun ta yayi a cikin nasa yana jin ciwon rashin gudan jinin sa da yayi wanda har ƙaunar sa ta fara yaɗo a cikin ransa "Safiya Annoba ce da ya dace ɗan Adam ya nemi tsari da mata ire-iren ta .

Maradi

Duk yadda likitoci suka yi kokari tare da son ganin Falmata ta haihu da kanta abu yaci tura gaba ɗaya ta gaza yin yunƙuri yadda ya kamata saboda firgicin da ta kasance a ciki ya tafi da duk wani ƙarfi nata .

Mafi munin abun shine jinin ta da yake daÉ—a hauhawa a bayan kowacce minti talatin .

Ba hajiya Umma kadai ba har Maimartaba ma ya shiga zullumi da yasa yake ƙiran waya bayan duk ƙaramin lokaci .
Chapter 264 · 0% Book details