← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 269

Sashe 158

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai kula ta ba ya jijjiga hannun ta dake cikin nasa ,

,"Khaalty Rahima tahadah 'iilaya rja'a ,
   Ya furta hakan yana sake kallon ta da ta sunkui da kai tayi ƙiƙam kamar bata jin sa , bai yi aune ba ta warce hannun da ƙarfi , ta sunkuya tana tattara kayan hannun ta .

Durƙuso yayi yana taya ta kwashewa ,tare da leƙa fuskar ta yana son sake ganin ta .

"Khaalty Rahima"

ya sake ƙira da wata irin murya , fuskar sa na nuna tsantsar damuwar da ta maye gurbin farin cikin sa .

"Yau ga ikon Allah Malam kurma ce fa kake ta faman yi mata magana , '

Tare suka miƙe da ita , da wani yanayi na firgici ya juya yana kallon matar .

"Kurma ?

"Eh kurma ce mana , hala ka san ta a wani waje ? Mamar Bulama da yawan gidajen masu kuɗi take ,  Ai manyan gidaje ɗaya-ɗaya ne a cikin garin nan da bata yi aiki ba , har gidan inn-in wannan mashahurin attajirin mai tashen kuɗi na bala'i da masifa , bani sunan sa ma ? Ga shi da suna mema sunan na sa ??,'

," kika ce kurma ce ? Mamar Bulama ? Wacece ita ? Ba gaskiya bane wannan ƙanwar Mama ta ce .

Juyowa yayi , sai dai ko alamar ta bai gani ba a wajen ,

" ina take ?,"

",Tayi tafiyar ta , ai kaga halin ta na miskilancin da yake sa ake tisa ƙeyar ta a kore ta daga gidajen da tayi aiki , miskilanci da faɗin rai na tsiya , to Allah na tuba kana talaka faƙiri mai neman na sawa a bakin salati ina kai ina faɗin rai ? Wa kuma zaka gwadawa ya ɗauka?  Gidaje daban-daban huɗu muka yi aiki tare , biyu akan halin ta aka ƙore ta biyu akan wannan ifiritun ɗaya-ɗayan ɗan nata Bulama haba me ake da batsal-tsalewa irin ta Bulama ya ɗan yayen biri ? .

Bai ƙarasa sauraron matar da take tsakiyar yi masa bayani har bakin ta na kumfa ba yayi wucewar sa ya bi sawun ta ,

  Cikin ran sa yana faɗin

",haba me ake da É—an banzan surutu marar ma'ana ?

Duba ta yayi har É—akin da ya san marar lafiyar da suke zuwa wajen ta na ciki amma bai gan ta ba.

Bai kuma tambayi matan da ya tarar a É—akin ba da ko alamu basu da nasaba ta jini da ita , dan haka sai ya koma.

kichiɓus suka yi da matar da ya baro a waje ,

," ka same ta....

Da hannu ya dakatar da ita , alamar tayi masa shiru  ya wuce cikin ran sa yana bawa kansa tabbaci babu shakka Khaalty Rahima ce , ita ya gani

Ƙanwar mamar sa ce da kusan tare suka tashi  , tunda ya buɗi ido ya gan ta a gaban iyayen sa kafin daga baya kaddarar da bai san ta mecece ba ta gifta tsakani ta raba su .

Sai dai koma menene yana ganin yazo ƙarshe , zai bi kuma duk hanyar da ta dace domin dai-daita rayuwar iyayen nasa daga walagigi .

Kai tsaye wajen motar sa ya nufa zuciyar sa cike da tunanin hanyoyin da zai bi domin gano haƙiƙanin rayuwar da Khaalty Rahima take tsawon shekarun nan, shin ita ce ko kuwa ba ita bace ?

Khaalty Rahima bata da wata larura da ta shafi ji ko gani , ance wannan kurma ce ??

Tada motar sa yayi , zuciyar sa maƙare da wasi-wasi , wajen Amne yake da burin zuwa a yau ɗin to amma yadda yake jin zuciyar sa a yanzu bai son kome illa ya kaɗaice .

Yana isa gida kai tsaye sashin su Rahima ya nufa saboda yunwa da yake ji tana ƙwaƙular ƴan hanjin sa ,

Da sallama ya shiga falon , idanun sa suka sauƙa akan ta da ta juya baya tsaye a gaban hoton ƴar yarinyar da bai kai ga rarrabewa ɗiyar wacece a tsakanin Hafsa da Zainab ba ?

Zama ya yi akan kujera tare da yin baya da kan sa ya jingina da kujerar

"Rahima idan akwai abinci ki kawo min , idan kuma babu ki dafa min Noddles yanzu ina jin yunwa sosai ki haÉ—o min da tea .'

Numfashin ta ne yayi sassarfa lokacin da sautin muryar sa ya sauƙa a kunnuwan ta,

shikenan addu'ar ta bata karɓu ba , domin kuwa tunda Rahima ta tabbatar mata da cewa hutu ya zo zai ya koma garin Abuja inda ya koma aiki da zama baki ɗaya tare da matar sa ,

take addu'ar Allah ya raba ganawa a tsakanin su har ya gama hutun sa ya koma .

To sai dai addu'ar ta ta a iya ranakun jiya da shekaranjiya tasirin ta ya tsaya , domin ga shi yau ko azahar bata yi ba Alƙadarin ta ya karye ,

Ita kunyar sa take ji , kunya mai tsanani kuwa , kunyar abunda ta aikata , me zata ce masa ? Da wanne ido zata dube shi , anya duniya da gaskiya ita tana da tsaurin idon sake kallon sa ?

"Rahima baki ji na ?

Satar kallon inda yake Yakaka tayi ta gan shi har yanzu yana yadda yake kan shi a kwance bisa kujerar ya miƙe ƙafafun sa .

Ba tare da ta juyo ba ta kama hanya da Æ´ar sassarfa da nufin barin wajen tsawar da ya daka mata ya sa ta dakatawa tana jin yadda zuciyar ta ke tsananta bugu .

"Rahima yaushe kika zama haka , marar ɗa'a ? Ni nake yi miki magana kina tafiyar ki ?  Zo nan .

Juyowa tayi a hankali , ta tsugunna a wajen da take , muryar ta tana sarƙewa tace

"Ba-ba Rahima bace ni ce Yaya Dakta .

Tamkar a ire-iren shuÉ—aÉ—É—un mafarkan sa da ya saba yi a shekarun baya ya ji sautin muryar ta , dan haka ya buÉ—e idanun sa da suke lumshe a hankali .

"Rahima zo nan nace "

Ya sake maimaitawa cike da burin son kawar da mummunan tunanin da ya bijiro masa da sautin ta a yau .

Ni ce Yaya dakta ta sake maimaitawa tana kif-kifta ido daga inda take .

A wani irin yanayi ya yunkuro kamar an tunkuɗo shi , ya zauna da kyau lokacin da yake ɗora idanun sa akan ta , da ta sunkui da kai ta ƙi kallon sa illa bakin hijabin ta da take wasa da shi a hannun ta ,

Ita ce ? Me ya dawo da ita ? Me ta zo yi nan ?

"Ke ce wa ?

Ya furta hakan da wata buɗaɗɗiyar murya me amo da ya sa Yakaka yin rau-rau da idanun ta da suka kawo ƙwalla ,

Shiru tayi ,

"Ke ce wa nace ? Me kika zo yi gidan nan ?

,"Ni ce Yakaka ."

  Ta bashi amsa cikin sanyin murya ba domin tana da yaƙinin bai gane ta ba , sai domin yunƙurin ta na ganin ta wanke kan ta .

Miƙewa tsaye yayi yana jin yadda wani irin bacin rai da ya sauƙo masa tun daga tsakar ka yana neman rufe masa idanu , 

"Tashi ki bar gidan nan ," ko kuwa na sa maigadi ya fita da ke , nan da kike gani ",
ya buga ƙafar sa guda a dandaryar falon cikin yi mata nuni ,

"   Ba gidan Karuwai bane , ba kuma gidan giya bane , tashi nace ,"
   Ya kwatsa mata tsawa

  Tsawar da yayi mata bata razana ta ba , bata kuma huda zuciyar ta ba irin kalmar karuwa da gidan giya da danganta ta da su ,

A hankali ta ɗago kan ta , idanun ta suna zubar ƙwalla tace ,

",Yaya Dakta kayi hakuri dan Allah na san nayi kuskure amma wallahi ba karuwanci naje ina yi ba makarant....

,"Shut up,

"Ki tashi ki fita nace ,

ya furta hakan yana kusanto ta da takun ƙafar sa  ,

," Big Bro ,

Ya tsinkayi muryar Rahima daga bayan sa ,

Ƙarasowa tayi tana raba ganin ta a tsakanin su biyun , da sauri ta ƙarasa wajen Yakaka wacce zuwa lokacin kuka take haiƙan , ta ɗago ta tsaye

"Big Bro , Mamar Mama ce fa Yakaka , bata mutu ba , kai ma kayi zaton Fatalwa ce kamar yadda ta tsorata ni da farko ko ? ,

"Rahima ki min shiru ,

yace yana nuna ta da allin ɗan yatsan sa , goshin sa a tattare da mabayyanin ɓacin rai .

,"ke ki tattara ki bar gidan nan yanzu-yanzu , kar ki ƙara minti goma idan ba haka ba kuma zan sa a fitar da ke ,"

Da sassarfa ya bar falon ,

Babu shakka kunya tayi ƙaranci a zamanin da muke ciki , idan banda tsagoron rashin kunya ita wannan yarinyar har tana da ƙarfin guiwar dawowa cikin gidan da ta gudu ta bari ?? Shin da wata alaƙa ta jini ne a tsakanin su bayan taimakon da yayi mata da ta saka masa da tarin butulci ,?

Da har kuma yanzu zata ɗebo ƙafafu ta zo gidan su to a matsayin wa take ? Kuma gurin wa ta zo ?

Har ta gama barikin ne ta gaji ta dawo ? Zaton ta nan matattarar karuwai ne ?  Ko kuwa har auren nasu da uban ƴar ta ta ya ƙare ne ?

Dole ta bar gidan kamar yadda tayi a baya,  tayi nesa da shi da dangin sa domin mumini ai baya sanya hannun sa a ramin Macijiya sau biyu .

Ba zai taɓa saurarar ta ba , ita ɗin zantukan bakin ta ai duk ƙarya ne , da yaudara , kirkin baka ne da ita tare da ladabin banza .

Runtse idon sa yayi yana tura ƙofar sashin sa da ƙarfi , ɓacin ran ganin ta yana sake hauhawa a ran sa hatta yunwar da yake ji tayi ƙaura .

,"Rahima dole na tafi tunda Yaya Dakta ne da kan sa ya kore ni kin manta shi ne ya fara kawo mu ? Dalilin sa muka zo gidan ku Rahima bani da ikon cigaba da zama ,"
Chapter 158 · 0% Book details