← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 269

Sashe 57

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana matsawa a jikin motar ya shiga gami da jan motar sa , a cikin ran sa yana mamakin al'amarin hatta tafiyar su iri ɗaya ya furta hakan a fili yana sake leƙen ta ta jikin madubin motar ,"  gefe guda na ran sa ƙaunar yarinyar da har yau bai ko kai ga sanin sunan ta ba yana tasowa , ya so ƙwarai ya nemo ta , domin a ranar da suka bar asibiti ita da ƙanwar ta ba ƙaramin damuwa ya shiga ba , so yayi ya ɗauke su ya kai su gidan sa inda yake zama tare da mahaifin sa da ƙannen sa ya ɗau nawin su ya inganta rayuwar su ita da ƙanwar ta , ya sha wahalar neman su da kwatance su a sansanin su dakyar aka samu wacce ta san su aka ce tare suka zo , tashin farko da ya tambaye ta game da su tace da shi YAKAKA DA FALMATA SUN BAR GARIN .

Assalamu Alaykum  my dear sisters ! How are you guys doing today  ? I hope everything is well ? Please don't delete comments because I didn't reply straightaway . I hardly get time to come frequently , but I do dedicate some time every now and then to reply to y'all Insha Allah  !

I hope you guys enjoyed this chapter  ??  buckle up cause chapter twenty is going to be a sadness one! 

LET ME KNOW WHAT YOU GUYS THOUGHT ,PLEASE  COMMENT , VOTE, AND SHARE WITH YOUR FRIENDS AND FAMILY.
    THANK YOU .

   

     
   
[6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: MAFARI .......
Hargitsin Rayuwa

umm"muaz

20

Yakaka tana shiga gida Kai tsaye sashin samy baby ta nufa , ta ci sa'ar samun kofar É—akin ta a buÉ—e kai tsaye ta danna kai cikin É—akin idanun ta a rufe da ruwan hawayen da yake ambaliya ,"

Zube guiwar ta tayi a ƙasa tare da yin jifa da kuɗaɗen hannun ta suka tarwatse a tsakiyar ɗakin ,hannuwan ta biyu ta sa ta rufe fuskar ta lokacin da take sakin kukan da yake cin ta a zuci .

Sautin kukan da yayi sanadiyyar tashin samy baby a firgice daga baccin tofon girar da take shaƙa ," 

Da sauri ta zo ta kama ta

Yaks meye ya same ki ? Duka aka miki ? Ko meye ?

Kusan ba a hayyacin ta ba ta riƙo hannun samy baby ,
  Dan Allah ki ce masa ya dawo kar ya bar ni , idan bana ganin sa mutuwa zan yi , kin ga nan ,"ta ɗora hannun samy baby akan zuciyar ta ,"ciwo take min ina jin wani abu ya tokare ni ," INA SON SHI WALLAHI INA SON SHI,"

Kalmar ta ta ƙarshe ita ta sa samy baby kwashewa da dariya bayan fitar ta daga ruɗanin da kukan yakakar ya haifar mata shi da farko ,"

   Shashashar banza yanzu ke yaks akan soyayya kike wannan uban kukan ? Kamar wacce aka cewa uwar ta ta mace ? To wai ma tsaya yaushe kika fara soyayya ban sani ba ? Duk kuwa da kashedin da nake yi miki ? Koh daga tafiyar da nayi ta sati biyun ce har kananan ƴan iskan nan da nake raba ki da su suka samu damar hure miki kunne ,ah lalle fa ga ki kuwa kin sauya kin yi lumui lumui kin cika kin yi clean , hala saurayin naki mai ɗan gwaɓi-gwaɓi ne naga ya wanke min ke , ah toh ai babu laifi tun da mai maiƙo ne ,"
      shi ya baki wannan kuɗaɗen kenan ? ," ta furta hakan tana mai bin kuɗaɗen da kallo , " idanun ta suka sauƙa kan ɗan wani hoton fasfo wanda ga alama daga tsakanin kuɗin ya fito , ta kai hannu gami da ɗaukar hoton ,
      Hoton sa ne sanye da kakin sa na soji daga kirjin sa zuwa fuskar sa ," kallon hoton tayi da kyau tabbas ta san shi abokin saurayin ta nuhu ne ,'bata manta ba nuhu ya bata ɗan takaitatcen tarihin sa a wani yammaci da taje bariki wurin nuhu ta tarad da youssouf ɗin , bayan tafiyar sa take tambayar nuhu  yaya ta ga launin uniform ɗin su ya banbanta ? Nan ya shaida mata youssouf sojin niger ne , ya ɗora da bata labarin sa kar ki gan shi haka anan fitattace ne a ƙasar su ɗan sarki ne , yarima ne mai jiran gadon birnin maraɗi ,babbar masarauta ce a niger ,"

     Yaks wanene wannan ?? Ko shine masoyin naki ?

Da sauri yakaka ta É—ago kan ta domin ta ga wanda samy baby take kira da masoyin ta ,
    Idon ta ya sauka akan ƙaramin hoton biyamuradi , da sauri ta kaiwa hoton chafka !
     Shine wallahi shine , ina son shi dan Allah anty idan kin san shi , ki kai ni wurin sa ,"

   Cikin mamaki samy take yi mata kallon kan ki ɗaya ?
   Ke yaks wannan ne saurayin ki ? Kar ki min ƙarya , gaya min ta yaya ya zama saurayin ki ?

    Yakaka bata boye mata kome ba daga ranar haɗuwar su ta farko da youssouf zuwa yau ,"
       Jinjina kai samy bby tayi bayan ta gama jin bayanin yakaka da ta tabbatar ba ƙarya bane ,! Domin ta san goge yaks a ɗan ƙaramin lokaci ta zama fes yadda ta gan ta sai mai kuɗi ,

Idan kuwa hakane babu shakka tayi farincikin ƙulluwar alaƙar sa da yakaka , daman irin namijin da take mata hange kenan wanda zasu tatsi arziki daga jikin sa  !tab , ai batun yace ya rabu da yakaka ma zancen iska ne , wasa tsakanin sa da yakaka yanzu aka fara , zata yi duk yadda zata yi taga mu'amalar sa da yaks ta ɗore , har sai ya gama wanke yaks ya zamar da ita mace mai aji yadda baza ta yi wahala ba wurin samun irin sa ko ma wanda ya fi shi koh da shi ya zo ya bar ta , ! Ai da ruwan ciki akan jaa na rijiya ,' idan yaks bata wanku ba ina zata samo masu attajirai irin wanda take buri???

      Share hawayen ki yaks idan wannan ne na san shi abokin saurayi na ne , duk inda yake sai na nemo miki shi , kin ji ? Bai isa ba ya wurgar da ke bayan ya morewa ƙuruciyar ki , dole ya zo ya ƙarasa aikin da ya fara ,"

Cikin murna yakaka ta fara share hawayen ta , tana jin damuwar zuciyar ta fiye da rabi ta kau , jin cewar samy baby ta san bature kam silum har tayi mata alkawarin nemo mata shi ,"

   A saboda murna tana tattara ƙudaɗen da ya bata , ta miƙawa samy baby ,"
     Ga shi anty na baki gaba ɗaya !

Da murmushi samy baby take kallon ta , sa hannu tayi ta karɓi kudin ta ƙirga su dubu arba'in da shida ne ,"

Naira dubu goma ta zara a ciki ta miƙawa yakaka sauran ,"

    Ki riƙe sauran kuɗin a hannun ki zasu miki amfani kafin na gama shirya yadda zan yi na dawo miki da yarima , wannan wanda na ware kuma , kafin ya dawo ku cigaba da harka dole zamu je asibiti a baki kariya daga samun ciki , kin sai dai ba'a cin moriyar bariki idan ana yi ana kwasar ciki .

    Da sauri yakaka ta amince da shawarwarin samy baby , nan dai suka ƴar taɓa hira samy baby tana sake kitsawa yaks shawarwarin yadda zata riƙe yarima idan ya dawo ,

    Falmata tayi jugum a zaune tana tunani, wata irin kewa take ji , tun da yakaka ta samu aikin da take yi yanzu  ya zama bata da lokacin ta irin da , duk da cewa dai idan tana gidan tana bata kulawar sosai da sosai bugu da ƙari ga cimaka masu kyau da daɗi da suke samu a yanzu , ga wasu ranakun ma biya yakakar take yi ayi aikin wanke-wanken falmata , amma duk hakan sun gaza samar da farin ciki mai daɗi ga falmata ,yanayin su na farko da ko yaushe suna tare yafi mata kome daɗi , bata da kowa bayan yakaka ,! Ga shi wannan aikin da yakaka ta samu yana neman raba tsakanin su , domin a yanzu duk zata iya ƙirga ƴan awowin da suke yi tare da juna a wuni ,

daɗewar da yakaka tayi yau bata dawo daga wurin aikin ba ya dagula ran ta , tana aunawa da zafin ranar da yake buso ta tare da kusancin ranar da take ji a jikin ta ta tabbatar yanzu rana ta fara kaiwa tsaka ! Ina yakaka take tun jiya da yamma har yanzu bata dawo ba ? A hankali wasu siraran ƙwallah suka silalo zuwa kan ƙuncin ta ,!

  Bata ji zuwan ta wurin ba , sai saukar hannun ta taji ta share mata ƙwallar ,!

Cikin ƙaruwar rashin kuzari akan wanda tafiyar youssouf ta jawo mata ganin hawayen falmata ya sake taɓa ranta , " ta zauna daga gefen falmatan
       Falmata na ! Meyasa ki kuka ? Wani abun aka miki ? Ko baki da lafiya ne ?

Yakaka yanzu kin rage kula da ni , bayan kuma kin san ke kaÉ—ai nake da ita wacce take bani kulawa , " yakaka dan Allah nima ki yadda na dunga bin ki sabon wurin aikin ki nafi son koyaushe muna tare duk inda muke , bamu da kowa sai junan mu ,"
   Kiyi hakuri falmata nima daga yau ɗin bazan sake zuwa ba !
   
    Meyasa baza ki je ba ? Ni fa ba nace ki daina zuwa bane , toh shikenan na hakura ki dunga zuwa kin ji ,?

   An dakatar da aikin ne wanda nake yiwa aikin ya tafi ,! Sai idan ya sake dawowa watarana ,"
Chapter 57 · 0% Book details