Sashe 20
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali yakaka ta sauke ɗan jaririn mai kimanin watanni biyu zuwa uku daga kan kafaɗun ta a yadda take durƙushe cikin gidan sauron tana ta faman jijjiga shi ,"tayi niyyar kwantar da shi a gaban uwar sa wacce take bararraje , tayi wawiyar kwanciya cinyoyi duk a buɗe kai ba ɗankwali ," cikin addu'ar Allah yasa kar ya farka domin hakika ta gaji da rainon sa tun farkon dare yake hannun ta lokacin da uwar sa ta dungura mata shi tace ta jijjiga shi yayi bacci, ita ta gaji bacci take ji ,ta jaa ɗayan ɗan nata gaban ta suke shaƙar baccin su ,"sau uku tana ajiye shi amma daga yaji an ajiye shi baya yin minti ɗaya yake sake challara kuka ," cikin gigin bacci da hargowa uwar sa zata ce dallah ta ɗauke sa zai hana sauran mutane bacci .
Cikin sa'a har ta kwantar da shi bai tashi ba ," tsurawa kofar ɗakin ido tayi tana ganin yadda walƙiya take haskawa tare da rugugin hadari nan take hankalin ta ya tashi tunowa da falmata da tayi koh a wane hali take ciki a ɗakin da take ? Ji tayi baza ta iya kwanciya ba idan bata ganta ba .
A hankali ta É—aga gidan sauron da suke ciki da niyyar fita dai-dai lokacin da aka yi wani tsawa da rugugin tasowar hadari da ya sa jaririn nan ya firgice tare da tsanyara kuka ," a daburce uwar sa ta farka gami da fara cewa ke ke keh kina ina ne kika bar shi yana ta irin wannan ihun ji min Æ´ar banzar yarinya ,"muguwa ,cikin sanyin murya yakaka tace wallahi yanzu na ajiye shi koh kwanciya ban kai ga yi ba , kuma ma da alama kamar yunwa yake ji ", ta furta hakan cikin fatan Allah yasa uwar ta É—auke shi ,"mts ta jaa tsaki tare da surar É—an jaririn kamar ta suri yaro mai shekaru biyu ," ta koma ta kwanta tare da shi tare da ciro abincin sa ta cusa mar a baki ,É—if yayi shiru .
Sauke ajiyar zuci yakaka tayi ganin uwar da ɗan sun koma bacci ,"ta siɗaɗa ta fita dai-dai lokacin da kakkarfan ruwan saman ya tsinke kamar da bakin ƙwarya ," gudu-gudu ta tsallaka ɗayan barandar ɗakin da falmata take ,'ba tare da ta damu da duhu tare da shirun da harabar wajen ya ɗauka ba ,ga ƙarar ruwan sama ,"
Tana shiga ta fara yawata idanun ta ," a hankali ta fara jin ƴar siririyar muryar ta tana kuka ,"ɗas-ɗas zuciyar ta ta buga tare da taruwar ƙwalla cikin gurbin idon ta, cikin sauri ta fara taku tana kewaye gidajen sauron jama'ah tare da tsallaƙe su cikin taka tsantsan ," tana nufar inda take jin sautin ta domin bata son yin magana kar ta tashi mutane
Cak ta tsaya da kukan jin takun sawayen ƴar uwar ta ,"yakaka ta furta cikin sanyin murya dai-dai lokacin da ta ƙaraso tare da durƙusawa a bakin "shingen"(gidan sauro) .
Ƙasa-ƙasa tace falmata meye yasa ki kuka ? Me aka miki ," da shishiƙar kuka tace babu kome yakaka na tuno da su mama ne ,"yakaka cikin daren nan kika fito kuma ana ruwan sama ? Meyasa ? ki koma ki kwanta dan Allah
cikin ƙura ido tare da taimakon hasken walkiya ta fahimci a dandaryar ƙasa kanwar ta take takure a zaune ," cikin takaici ta maida duban ta ga ajus da take ajiye numfashi ɗaya bayan ɗaya tare da sake duƙunƙunewa cikin jin daɗin barcin ta ,take ta fahimci abun da yake faruwa ,"
Zuruf ta miƙe cikin cewa ina zuwa falmata ," bata saurari amsar falmatan ba ta fita ,
Jim kaɗan ta dawo tare da bargon ta a hannun ta zura hannu ta miƙawa falmatan bargon,"ungo falmata buɗa shi ki kwanta akan rabi ki rufu da rabin duk da ma dai fitsarin yaron matar chan ya taɓa jiki amma ki kwanta a haka ,"
Jin falmatan tayi shiru yasa tace matsa na shinfiÉ—a miki kin ji ,"? Cikin rawar murya tace yakaka ke kuma ki koma ki kwanta akan me ?
Shittt ," falmata lafiyar ki tafi min kome , bamu da kowa a yanzu daga Allah sai junan mu , menene amfani na idan har ban zamar miki garkuwa ba falmata ,"Â tana furta hakan ne dai-dai lokacin da take gyara mata bargon tana shimfiÉ—a mata ," kama mata tayi ta kwanta ,"
Yauwa toh bari ruwan ya É—an tsagaita sai na koma É—akin mu kiyi baccin ki kin ji ?
GyaÉ—a mata kai tayi domin kuwa idanun ta har yaji-yaji suke mata tsabar baccin da ya cika su ,
Sauke sassanyan numfashi tayi , tare da share guntun hawayen da ya cika mata gurbin ido nisawa tayi tana tunanin ƙalubalen da suke a farkon sa yanzu wanda basu da sani akan iyakar sa ,karshen sa babu abun da yafi tsaya mata a zuci irin tausayin ƙanwar ta a yin rayuwa cikin wannan sansanin da ta lura kowa kan sa ya sani kan sa yake so "rayuwar daga ƙawri sai gwaiwa ", zuciyoyin mutane cike take da mugunta da son kai .. Yaa Allah ga ni ga miskiniyar kanwata Allah ka taimake mu .
        *MaraÉ—i jamhuriyar niger*Â
A karo na biyar ta kama ta sauko daga kan murfin sunduƙin yin "bahaya"( Toilet- Toilette ) da yake cikin banɗakin ta ," kai kawo ta shiga yi tare da duban agogon fuskar wayar ta "
Yau har karfe biyu da mintuna arba'in biyamuradi bai dawo ba kamar yadda ya saba fita sha biyu da rabi na dare ya kuma dawo karfe biyun dare ,"
Meye ya tsayar da shi ? Jin motsi tayi kamar an taÉ“a kofar sirrin da take bangaren biyamuradin wacce kuma da ita yake amfani wurin fita da shigar sa gidan a dai-dai wannan lokutan da ba wanda ya taÉ“a sanin yana fita daga Allah sai shi sai ita ,Â
Cikin sauri ta sake ɗarewa kan sunduƙin tayi ƴar ɗage ta leƙa ta ɗan siririn huɗar da aka yi ta a can saman banɗakin domin ado wanda aka liƙa kwan lantarki a jiki, sai dai a halin yanzu babu ƙwan lantarkin sai dai huɗar da ta fito sarari ake iya ganin abun da ke waje ta wurin ,
Tar ta hango shi a cikin hasken lantarkin da ya ƙawata lambun bayan ɗakunan sa ," yana layi tare da tamɓele jikin farar rigar sa da shuɗin wandon jins ɗin sa dumu-dumu da abun da bata iya tantance shi daga inda take ,"
Ji tayi ruwan hawaye ya silmiyo daga gurbin idanun ta da gudu sun fara tsere akan siriryar fuskar ta ,"
Wani faɗuwar ƴan bori da yayi rigijib shi yasa ta kusa zamewa ta silmiyo daga kan toilet ɗin , da sauri ta ɗiro cikin gudu-gudu ta bullo ɗakin ta tare da fitowa cikin parlour kai tsaye ta nufi kofa ta kama mariƙin kofar ta murɗa , zuciyar ta tana zafi tare da ingiza ta , idanun ta suna hango mata faɗuwar da abun kaunar ta yayi .
Sai dai turus ta jaa ta tsaya lokacin ta tuno da fitar ta a wannan lokacin zuwa bangaren biyamuradi zai jawo , me zata cewa masu tsaron gidan ? Wanda ta san basu san halin da yake ciki ba , basu taba sani ba , idan kuwa har ta fita war haka dole su sani .
Hakan yana nufin fallasuwar mummunar fuskar masoyin ta , hakan yana nufin kunyatar masoyin ta , hakan yana nufin dasuwar bakin ciki cikin zuciyar uwar goyon ta , hakan yana nufin samar da wanzazjen bakin ciki cikin zuciyar uban goyon ta kuma kawun ta , hakan yana nufin tozartuwar Æ´an uwan ta ,hakan kuma yana dai-dai da zubewar girma da mutuncin masarautar su baki É—aya .
Kamar walƙiya ta juya ta koma da sassarfa ta shiga ɗakin ta gami da murza mukulli lokaci guda ta nufi gadon ta gami da fadawa rubda ciki ta sanya kanta tsakanin filo gami da fashewa da wani irin kukan da ya tuƙo tun daga karkashin zuciyar ta , kuka ne irin wanda mutum yake yi idan bakin ciki yayi masa yawa .
*Sorry this is a really short chapter koh? Kar ku damu insha Allah the next one will be longer and more action packed !*
*Things are really starting to heat up now* 😜
*Please comment what you guys think of not just this chapter but every chapter . I really love hearing feedback on my work because these chapters are not easy to write .*
*#Thanks* .
*#son so*
*#mafari Yanzu muka fara*
[6/24, 9:58 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association
*MAFARI.......*
( _Hargitsin Rayuwa )_
*umm'muaz*
7
Juyi ya sake yi a karo na barkatai bisa makeken gadon nasa na alfarma, tare da runtse idanu yana mai sake jin yadda kan sa yayi masa mugun nawi har baya iya buɗe idanun sa sosai , ɗan ƙaramin tsaki ya jaa da yayi sanadin juyowar Tafeedah wanda yake zaune bisa doguwar ƙawatatciyar kujerar da take gaba ƙadan da gadon .
Cikin takaici yake duban biyamuradi yousouf ɗin , kafin ya ɗan yi gyaran murya ! "cikin kowanne daƙiƙa ɗaya da yake wucewa yana sake nisanta ka da lokacin sauke farillah " tafeedan ya furta kalmomin masu nuni da tunasarwa , cikin nuna halin ko in kula ga biyamuradi yousouf , wanda koh kafin tafeedah ya idasa bayanin sa ya buɗe idanun sa tarwai da jijiyoyin cikin suka yi jaa , kammala bayanin nasa ya zo dai-dai da miƙewar sa zumbur daga kan gadon .
Bai yi wani jinkiri ba ya fara taku cikin sassarfa lokaci É—aya yana sauke idanun sa akan tagar É—akin sa wanda hasken rana ya riga ya hudo ta tsakanin labulen .
Bayan tsawon mintoci fiye da talatin da biyamuradi youssouf ya É—auka yana addu'a da neman gafarar mahaliccin sa bayan ya idar da sallah ,
sadda kansa ƙasa yayi yana me jin kunyar ɗago kansa ya dubi aminin nasa wanda ya tabbatar idanun sa a kafe suke a kan sa , yayin da sashi guda na zuciyar sa yana me son tuno da wani abu .