← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 269

Sashe 35

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da raɓe-raɓe ta fito daga banɗakin tana tafe tana sake sauke siket ɗin ƙasa-kasa sakamakon tsagun sa da yake har ya zarta gwuiwar ta ,

Wurin karɓar burkutun suka haɗu ita da yagana da tun safe madam saly ta sata gyara mata cikin ɗakin ta ,"amma tsabar shirgin da yake cikin ɗakin bata samu damar kammala gyaran ba sai yanzu ,"

Kallon kallo suka yi da ita da yagana wacce ita ma take tsuke cikin sabuwar shigar da madam saly ta bata na wani chasasshen wondon jins da yake a ɓarƙe ta wurin cinyoyin sa da wata ƴar ɗangalalliyar riga mai siririn hannu ," fuskar yagana ta kalla kawai ta fahimci ita ma tirsasa ta madam saly tayi ,ta sa ta sanya kayan a dole kamar yadda tayi mata ,"

Ba wacce tace ga ƴar uwar ta ƙala suka ƙarbi manyan farantan silver da larki da hema suka ciccika musu ruwan burkutu a kofuna tare da jerawa akan farantan ,"

Tana shigowa Æ´ar rumfar ta doshi gurin da É—azu wasu mutane biyu suka bukaci ta kawo musu burkutun dayawa ,"

Turus ta yi lokacin da ta tadda kujerun da ta bar su akai wayam babu kowa ,"

ÆŠan waiwayawa tayi tana dube-duben wurin da zata hango su ,ga zaton ta kou sun sauya waje ne ,"

Sai dai jajayen idanun mazan da taci karo da su suna kallon ta ya sa nan take ta diririce saura kiris ta saki farantin hannun ta ,"fiye da rabin maxan wurin kallon farar doguwar yarinyar da take sanye cikin jaan yadin da ya sake fidda kyau tare da hasken fatar ta suke," giyar da suka shaa suka yi tatil tana sake ƙawata musu tare da girmama musu sassan halittar jikin ta daga yar ƙanƙanuwar yarinya zuwa cikakkiyar babbar budurwa ," nan take suka fara kawo mata wawura da chafka cikin tamɓelen su na mashaya," 

Zilliya da zamiya ta haɗa Allah ya bata ikon tsalleke farmaƙin da suke kawo mata , " dan haka gudu-gudu ta maida tiren burkutun tare da shaida wa larki, masu neman burkutun sun tafi .

Ganin lokacin tashin su ya riga yayi "karfe biyar tayi " ya sa ita da yagana suka nufi ainahin cikin gidan inda anan É—aki da falo gami da banÉ—akin madam saly yake ,"

Suna isa kamar kullum iwar haka suka tadda cikin falon nata a cike da manyan ƴan matan da suke ji da kan su ire-iren su samy baby ," sai karta suke da cha-cha suna yi suna haɗiyar ƙwayoyi tare da kora ruwan maganin mura da yake mahaɗin ƙwayar da suke sha ,"

Madam saly tana daga gefe zaune tsakanin wasu manyan Alhazawa biyu da alama wata magana mai muhimmanci suke yi ,"

Ɗan rakuɓewa suka yi daga bakin kofar a durkushe sannan suka sanar da madam saly lokacin tafiyar su gida yayi ,"

  Kallon hadarin kaji madam saly ta watsa musu kafin ta balbale su da masifar basa ganin tana tare da baƙi ne ? Su waɗanne irin wawaye ne ?

Hakuri suka bata tare da cigaba da tsugunno nan bakin kofar suna jiran ta ta kammala da bakin nata ,"

Sai da aka kwashe fiye da mintuna arba'in har duhu ya É—an fara shigowa karfe shidda ta gabato , zuwa lokacin kuwa har kafafuwan su sun sage duk sun muzanta tsabar gajiya .,"

Sai da suka kammala maganganun da su basa iya jin me suke faÉ—i daga inda suke a sakamakon hayaniyar da take sake cika illahirin da'irar wajen ," basu ankara ba suka ji ta watso musu kuÉ—in aikin nasu ,"

  Ga shi nan ,' ku tabbatar gobe kun zo akan lokaci sannan ku tabbatar baku dawo min nan wajen da waɗannan shegun tsunmokaran kayan naku ba ,"  idan kuwa kuka yadda kuka doso min nan wajen da wannan shigar taku uwa masu kwana akan bola toh kuwa a bakin aikin ku ," ni bana son ƙazanta ,"ta karashe zancen tana jawo wata jakar bagco ta tura musu a gaban su ," ga kaya nan kowaccen ku shiga bibbiyu da su nake so na dunga ganin ku ," kun ji koh baku ji ba ???

  Cikin sauri su ka amsa da toh !

Sauri-sauri suka haura tudu tare da barin unguwar suka tadda falmata wacce har ta fara gundura da jiran su tare da fara jin tsoron rashin dawowar su har zuwa yanzu da take jin hayaniya ta ragu a bakin kasuwar alamar an watse domin tun É—azu baba modu ,"mutumin da take zama a gefen rumfar sa ," ya tattara kayan sa tare da sauke rumfar ta sa yayi mata sallama ya wuce gida ,"

Ajiyar zuciya ta saki a take fuskar ta ta yalwatu da murmushi sakamakon jin muryoyin su yakaka ,"
   Yakaka yau kun daɗe a wajen aikin da fatan dai lafiya ? Dan har na fara tsorata .

Kamo hannun ta yakaka tayi tare da sarƙafe yatsun su cikin na juna,

  Lafiya lau falmata uwarɗakin mu ce yau tayi baƙi shiyasa bata sallame mu ba da wuri , kin ci abincin rana dai koh falmata ?

  Naci gƴaɗar naira ashirin yakaka ," ta furta hakan tare da miƙa mata ɗaurin bakar leɗar da take tara kuɗin barar ta a ciki  ,"

    Wannan karon yagana ce tace ,"
   Gyaɗar naira ashirin ba abinci bace falmata ina ma laifin ki sayi koh ƴar awarar hamsin ,"ki daina zama da yunwa kullum muna faɗa miki ,ai yunwa tana daga cikin dalilin da yasa muka fito nema , toh me yasa zaki sake zama tare da yunwar bayan kuma akwai kuɗin sayan abincin a tare da ke ,"

   Shiru falmata tayi ba tare da tace ƙala ba cikin ran ta kuwa tana sake kuɗurce niyyar cigaba da tara kuɗin barar ta , har sai ta samarwa da yakaka iya adadin kuɗin da zai isa ta jaa jarin kowacce irin ƙaramar sana'a ce da zasu iya dogara da ita ba tare da yakaka taje tayi aikatau ba ,"

Yakaka kuwa da ita ma bata ce kome É—in ba idanun ta ne yake bisa kan wata mata da take soya doya da kwai daga gefen bakin tashar ," sakin hannun falmatan tayi ba tare da ta amsa tambayar da falmatan take yi mata ba na "ina zata" ?

Ta nufi me sayar da doyar , ta miƙa naira ɗari daga cikin kuɗin aikin ta ɗari uku ,"ta ce a bata doya ,"

Kamo hannun falmatan tayi tare da zaunar da ita akan wani É—an fasasshen buluk ta tsugunna ta buÉ—e ledar doyar tare da É—aukar yanka É—aya ta nufi bakin ta da shi
,"buɗe bakin ki kici zaman ki tare da yunwa barazana ce ga kwanciyar hankalina falmata , babu amfanin wuni da nake ina aikayau idan har ke zaki wuni tare da yunwa , alhalin kina zaune a bakin hanya cikin rana kina bara , na kasa baki kulawar da ta dace , rashin amfanina zai yawaita a gare ki falmata idan har ya zama na kara miki da yunwa daga yau kar ki sake zama da yunwa duk kuɗin da aka baki na sadaka ki daina ajiye ko sisi duk ki sayi abinci ki ci , ki  ƙara girma ki zama ƙatuwa ko bakya so idan mama ta gan ki ta ji daɗi tare da yaba min akan na kular mata da falmata mafi soyuwa agare ta cikin ƴaƴa ??",

Tun da ta fara maganar take taunar doyar da ta sanya mata cikin baki tana murmushi , kammala maganar ta ya zo dai-dai da fitowar Æ´ar siririyar dariyar da tayi jin an ambaci kalma mafi daÉ—in sauraro agare ta watau " dawowar mahaifiyar su"

     Nagode yakaka a kullum ina alfahari da yawan ƙaunar ki gareni ina kuma rokon Allah nima ya bani damar da zan nuna miki kulawa koh da bata kai yawan wacce kike min ba ,Allah ya bayyana mana mama tare da su baana cikin ƙoshin lafiya ,"
  Su duka suka amsa da ameen har yagana da take kallon su cikin sha'awar yawan kaunar da suke yiwa junan su ,"

A gijiye likis suka dawo sansanin nasu amma hakan bai sa ,"fanna da ajus sun tsahirta musu ba domin tamkar jira suke su sanyo kafafun su cikin camp ɗin su tare su da lodin aiyukan su da ƙyuiya tare da sanin cewa akwai waɗanda suka maida bayun su ya sanya suka ƙi motsawa suyi aikin ,"

Da É—ibo ruwa da suka tadda an tada injin yamma kenan suka fara , kafin yakaka ta É—ora da wankin kayan yaran fanne na kashi da fitsari , ita kuma falmata ta tafi aiken da ajus tayi mata wurin saurayin ta wanda shi ma a cikin sansanin nasu dai yake amma yana ta bangaren maza da yake chan-ciki inda tantunan maza yake ,"

Wannan shine karo na huɗu da ajus take aiken falmata ta karbo mata kuɗi koh kuwa ta tambayo mata saurayin nata kou zasu samu damar haduwa a wannan ranar idan dare yayi ," wanda ita kuma sam falmata bata son zuwa wurin tantunan samarin saboda wani da bata kai ga sanin sa ba da yake biyo ta a baya ta tsakankanin manyan bishiyun darbejiyar yana taɓa mata jiki ," yana faɗin wai tsarin jikin ta tun tana ƙarama yana da kyau ,"

Sai dai tsoron ajus ya hana falmata tayi wani yunƙuri na samarwa kanta damar kaucewa zuwa aikin ,
Chapter 35 · 0% Book details