← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 197 OF 269

Sashe 197

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gefe guda kuma yana jinjina Yakanah irin tata da bata taɓa furta masa kalmar so a gaban sa ba ko sau ɗaya , ta kuma yi ƙoƙarin dannewa ta ɓoye hatta ga shi kansa bata yadda cikin saninta ta nuna abunda ke binne cikin ranta ba , bare kuma ga ƙaunarta da yasan abadan baza ta taɓa bari ta fahimata  , daga ƙasan ransa ya furta "Madallah da ƙarƙƙarfar kyakkyawar zuciyar da take iya danne tasirin So , ƙwarai ita ɗin ai jaruma ce . "

Ƙarfe uku na ranar ta yi masa a cikin Masarautar su inda ya tafi kai tsaye ga fada ya kai gaisuwa gurin Maimartaba wanda ya amsa masa fuskarsa ba yabo babu fallasa , sai dai saɓanin baya da idan har ya shigo fada ƙirarin da manyan fadawa da kansu ke yi masa har ya tashi , yau dai shiru babu wanda ya kambama shi da ƙirarin sai fa dogarai da suke tsaye daga bakin-fada .

Shiru yayi kansa a sunkui yana jiran Maimartaba yayi masa umarnin dawowa daga gefensa kusa kamar yadda ya saba a koyaushe , sai dai har ya kusan mintoci ishirin a zaune maimartaba bai sake duban sa ba , dan haka ya miƙe yana mai sallama da Maimartaba da sauran jama'a da suka amsa a sama-sama ,

Idanunsa suka kai inda yake mazauninsa ada kusa da ƙafafun Maimartaba , karaf suka haɗa ido da Mammadou da yake zaune a gurbin sa , wanda yake jifan sa da wani ɗan guntun murmushin ƙeta , ɗauke kansa yana ƙarasa barin Fadar .

A sanyaye ya taka yana yana nufar ciki sashin Hajiya Umma , a hanya babu abunda ya sauya na yadda bayu ke zubewa gaishe sa , sai dai yana lure da wani irin kallo da wasun su ke binsa da shi wasu kuma yana iya jiyo ƙus-ƙus ɗin su daga ya gota .

Ita ɗaya ya tarar da ita a falonta na ƙurya da yawanci sai zata yi ganawa ta sirri take shigarsa ,

Zama yayi a gabanta yana mai sunkui da kai cike da ladabin da yake halayyar sa ya gaishe ta , muryarta babu amo sosai ta amsa gaisuwar sa ,

Shiru ya É—an gitta kafin da murya mai kaushi tace da shi ,

    " Ina kouma itta ɗiyar da kake amren ?

Shiru yayi kaÉ—an kafin ya ce
     " sun tai ga ƙasar su baki ɗaya ,

Sake tsare shi da ido tayi , duk kuwa da ta ɗan yi farin-ciki da cewa da yayi "sun koma ƙasar su , sai ta ɗora da cewa  " ka sau amren ta ko kuwa ?

   Shiru yayi cikin fargaba , yana tsoron kadda ta tilasta shi ya saki Fatima , wani sashi na zuciyar sa ya ji yana gargaɗin sa daga sake yin ƙarya ,

wani busasshen yawu ya haɗiye , ya ɗago da kansa ya dube ta , a hankali ya mayar da kansa ƙasa kafin yace ,
    "Ban sau amrenta ba sun tai gida ne kafin al'amura su dai-daita anan ,

"Youssouf ,
   Hajiya Umma ta ƙira sunan sa , a tsorace ya amsa "Na'am Umma , zuciyarsa tana mai tsananta bugu yauce rana ta farko a iyakacin sanin sa da ta taɓa ƙiran sunan sa kai tsaye .

  " na maka oumarni ka sau amren ɗiyar nan ka aika mata da shikan ta can zouwa ga ƙasar su , muddin kana ƙamnar da na yafe ma kouma Mahaifinka shi maka afouwa , idan kouwa ka ƙi bin umarni na Youssoufa , shiru tayi bata ƙarasa ba ,
   sai dai ya fahimcin munin abunda ka iya biyo baya ganin yadda ɓacin rai ya ƙara hauhawa a kan fuskar ta bayan ta kawar da kai daga barin duban sa , 

  Gumi ne ya shiga keto masa kota'ina cikin jikin sa , ya sanya hannun sa yana share zufar goshinsa ,
   Muryarsa can ciki yace , " Na amshi oumarnin ki Umma, ki yafe min bissa ga kuskuren da na aikata .

Muryar ta da ɗan sassauci tace , " Laifin ka ga Allah kayi ka nemi Yafiyar sa , doumin shi mai yawan afouwa ne ga bayinsa ,  sannan ka kyautata tuban ka , ni kam abou ɗai nake so kayi shine sakin auren ɗiyar nan idan kayi hakka shikenan .

  Shiru yayi baice kome ba , saboda zallar tashin hankalin da yake ciki , duk wata ƙafa ta isar da saƙo a jikinsa jinya take da amsar umarnin Hajiya Umma .

  Ganin yadda ya zamto tamkar wanda aka zarewa lakka a gabanta yasa tayi gyaran murya tana mai ƙarfafa zuciyarta daga tausayi irin na tsakanin ɗa da mahaifiya daya soma mamayarta , musamman kasancewarsa mafi soyuwa a gareta cikin 'ya'ya ,
    " ka tashi ka tai ga matanka bayan ka tanadi kyawawan kalmomin da za ka yi amfani da su wajen tausasa zuciyar su doumin laifin ka mai nawi ne a wajen su .

Kamar jira yake tace ya tafi , sai ya miƙe a hankali bayan ya mata bankwana ya fito daga falon , baya sanin takamaimai ina yake jefa ƙafarsa ya nufi shiyar gidan sa ,

Sashin Siyama ya tasarwa ba tare da ya haƙiƙance meye zai je ya sanar da ita ba ,

Da shigar sa Yumna ta taso da gudunta daga inda take wasa a tsakiyar falon da tarin kayan wasanta ,

  Da sauri ya sunkuya ya ɗauke ta yana matse ta a cikin jikin sa kewar Mama marar adadi na taso masa ,

   "Papa ,
   ta ƙira shi da ƴar muryar ta ,
"Yumna , ya amsa yana ɗora idanunsa akan Siyama da ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take kishingiɗe Rakiya na mata tausar ƙafafunta ,

Da sauri Rakiya ta miƙa gaisuwar ta kafin ta bar falon zuwa can waje sashin su na ma'aikata ,

A hankali Siyama ta tako gaban sa bayan ta ƙirkiro wani guntun murmushi akan furskar ta ,

"Sannu da zouwa Biyamuradi,  da fatan ka iske mou lafiya ?
  Tana ƙarasowa ta kama hannun sa guda , kafin ta cigaba da cewa ,
    " Mu tai kayi wanka Baban Yumna kafin a samar da abinda zaka taɓa ,

Yanayin rashin kuzari bai bar shi ba ya bi bayanta zuwa sama É—akinsa ,

Bayan ya yi wanka ya shirya , cigaba yayi da zama akan kujerar ɗakin ya zurfafa cikin tunanin umarnin Hajiya umma , da kowacce daƙiƙa guda tashin hankalinsa daɗuwa yake , gefe guda ga rashin sanin takamaimai halin da ita kanta Fatima ke ciki tare da ɗiyansa dake maƙale a marar ta ,

   Ƙarar wayar sa ya sanya shi janye tagumin da yayi ya ɗau wayar ganin mai ƙiran nasa daya daga cikin manyan kwamandojin sojin su ne na yankin Diffa ,

Magana suka sake yi kan tsaron da zasu daɗa a tsakanin boda saboda motar da take ɗauke da matarsa da zasu bi ta Boda zuwa Nigeria , bayan ya gama wayar da bai ɗau lokaci yana yi ba ya ajiye wayar a gefe yana baya da kan shi ya ɗora kan bisa  allon kujerar ya ɗora dogayen ƙafafunsa akan ɗan teburin gilashi da yake gaban sa ,

Idanun sa ya runtse yana jin yadda kansa  ya ke sara masa musamman ta goshin sa ,

   Siyama wacce ta ji shirun sa yayi yawa bayan ga abinci ta haɗa masa a shiyar cin abincin su , sai ta miƙe ta hau saman , cikin ranta kuwa ƙoƙari take tayi aiki da shawarwarin da Rakiya ta bata na danne kishinta daga barin bayyana shi a sarari ,

Tana murɗa ƙofar ɗakin ta hango shi a kujerar ya dafe kan sa da hannunsa guda , wani irin yanayi na zallar tausayi da ake samu ga abunda ake ƙauna ta gaskiya , shine ya tsigar mata , babu shakka a tun shigowarsa ta fahimci tsananin tashin hankalin da yake ciki .

Bai ji shigowarta ba har zuwa zaman ta a gefen sa , sai da ya ji hannunta mai tsananin taushi ta É—ora akan nashi hannun da ya dafe goshinsa da shi ta janye shi ,

  "Baban Mama , ta ƙira sa , ɗas ! Zuciyarsa ta buga da jin sunan Mama da ta masa inkiya da shi da Falmata kaɗai ke ƙiransa da sunan ,  sai ya dawo da ganin sa kanta ,bayan ya gyara zamansa yana jin wani irin yanayi mai tasari matuƙa ,

   "Baban Mama ina miƙa ta'aziyyata kan rashin da muka yi na ɗiyar mou , Allah shi jikan Mama shi sa ta ceto mou .

Sai tayi shiru tana neman dai-daita nutsuwar zuciyar ta daga tarin baƙin-cikin da yake bijiro mata na zallar kishin Falmata , ta ɗora da cewa ,

   " Ina ƙamnata Fatima ? Da fatan ka baro ta lahia ?

Da wani irin yanayi ya matse hannunta dake cikin nasa , cikin muryar dake cike da rauni yace
    " nagoude sai dai a halin yanzou Fatima ta gudou ta barni zuwa kan hanya mai matuƙar haɗari , Hajiya Umma kuma ta min oumarni na sau amren Fatima , ki min addu'a Siyama lamura agareni sun tsaurara , kowa ba shi fahimta ta bisa jarabawa ta rayuwa .

Ƙwalla ta ji sun tara mata a ido , tunda take bata taɓa ganin Biyamuradi cikin halin ɗimuwa tare da rauni makamancin haka ba , sai fa yau ta dalilin ɗiya Mace , babu shakka wagga ɗiya Fatima ta kai ayi gangamin tafiya kallon ta .

Gagara cewa kome tayi illa kanta da ta kwantar bisa ɓarin jikinsa , cikin tausayin kai tace , " kayi haƙouri da ikon Allah lamura zasu dai-daita maka a tsakanin hakka nayi Alƙawarin taya ka da addu'a , Allah shi dawo maka da Fatima-zahra .

Hannunsa duk biyu ya sa yana rungumeta tsam a jikin sa , ransa cike taf da ƙauna ta musamman gami da ƙarin ganin ƙimar ta a idanunsa , babu shakka shi masoyi na gaskiya abun riƙo da hannu biyu ne .
Chapter 197 · 0% Book details