← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 183 OF 269

Sashe 183

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A duƙe ta ƙarasa ɗakin saboda mararta da take ji ta riƙe , da taimakon hasken lantarki ta hango Mama a ƙasa ta faɗo daga kan ɗan gadon ta da yake dakin ,

Da sauri ta ƙarasa ta ɗagota tare da rungume ta a jikinta, tana tattaɓa jikin da ta ji yayi zafi rau , muryar ta na karkawa tace ,

" Mama meyasa kika faɗo daga gado ? Ina ne yake yi miki ciwo faɗa min , ? Kai ne ko ƙafar ki ko hannu ? Ko Bayan ki ne ??

Mama wacce take wani irin nishi ta riƙe hannun Falmata tare da ɗorawa akan cikinta ,ƴar muryar ta da kyar take fita tace ,

"ciki na ne ,Mama cikina yana ciwo sosai , ki bani magani zan sha ,ina so nayi bacci Mama ,

Wasu sabbin hawayen ne suka silmiyo daga gurbin idanun Falmata ,

"sannu Mama ,sannu kin ji zan baki magani yanzu ,

Bata amsa ba sai nishi da ta cigaba da yi , a hankali Falmata ta dafa cikin nata ta ji yadda ya kumbura yayi ƙem-ƙem ko numfashi da kyar take fitarwa, wani irin tausayi ne ya kamata tare da tashin hankali a lokaci guda ta nemi ciwon marar da take ji ta rasa ,

Tana dafe da cikin Mama ta fara yin addu'ar samun lafawar ciwo kowanne iri ne ,

Tashin hankalin da zuciyar ta ke ciki a lokacin yana neman kayar da ita , saboda rikicewa da jikin Mama yake neman yi da ƙarin ƙarfin nishinta ta fara ƙiran Baban ta ,

"Papa , Papa ,

Youssouf wanda shigowar sa kenan falon jikin sa a sanyaye ya zauna a kan kujera zuciyar sa cike da tashin hankali kan iƙirarin Yakaka na ya saki Falmata ko kuwa ta je ga iyayensa  , sam bai yi zaton abubuwa zasu rinchaɓe masa ya irin haka ba ,

Yasan cewa shi mai lefi ne a wajenta amma ko meyasa baza ta saurara su bi kome a sannu ba ?

Ƙiran sunan sa da Mama take yi ya sa ya miƙe ya nufi ɗakin zuciyar sa ɗauke da sabon zullumi kan tashin ciwon ta ,

A kiɗime ya ƙarasa kan su ya tsugunna ta bayan Falmata yana zagaye su duk biyun da hannuwansa da ya kai ya ɗora a cikin Mama inda ya ga Falmata ta riƙe ,

" Meye ya same ta ? Ciwon ciki take yi ,

"Papa ,

Mama ta ƙira sunan sa tana ƙokarin buɗe ido ,

" na'am princesse ina yake miki ciwo ?

'papa ciki na ka bani magani ina so na kwanta ,

"Mama ai a kwance kike , bari na kawo magani kisha kafin mu tafi hospitalisé, 

"Fatima yaushe Mama ta fara ciwon ciki ?

Ya tambaye ta yana kallon fuskarta ,

Sunkui da kai tayi tana kaucewa ganin Fuskar sa , muryar ta a É—an dishe tace "Yanzu ne ,

Bayan ya kawo maganin ciwon ciki ya bata ta sha , ya janyeta daga jikin Falmata ya É—ora ta akan gado , " Fatima kin yi sallah kou ?

Girgiza kai tayi tana miƙewa ,

'kiyi sallah mu tai da Mama hospitalisé ,

Bata amsa ba ta ɗau hijabinta ta zura tana barin ɗakin da take jin sa a ƙuntace tunda shigowar sa ,

Ta kama hanyar da zata sada ta da ciki sashinta , sannu-sannu take tafiya tamkar wacce aka zarewa laka ,

damuwa yayi mata yawa bata taɓa zaton zuwan wannan ranar ba , saki a tsakaninta da Baban Mama ?

Da kowanne daƙiƙa guda tunawa take da kalaman Yakaka , da Baban Mama taƙi yarda wani sashin zuciyar ta da yake bijiro mata da rashin kyautawar Yakaka tare da son kai da take ganin ta nuna ƙuru-ƙuru ya rinjayeta ,

Ƙoƙari take ta haɗiye tashin hankalinta ta haƙurƙurtar da ranta ta kuma ƙarbi duk wani hukuncin da su biyun da a yau duniya bata da kamar su zasu kai ga yankewa akanta ,

So take ta rufe ta binne duk wani sirrin dake zuciyar ta a can ƙasan ranta .

Sai dai zuciyarta rawa take tana tantamar anya zata iya ??

Hannu ta sa ta tura ƙofar falonta ta shiga , tamkar baƙuwa haka take sanɗa a falon , aiyanawa take nan da ɗan wani lokaci kaɗan kome na gidan zai tashi daga matsayin mallakinta , to ya koma na wa ??

Taƙi yadda ta hasaso ƙarshen lamarin saboda bata jin zuciyar ta zata iya jurar yadda ƙarshen kome zai zama bata son tuno da makomar Rayuwarta .

Har ta nufi ɗaƙin ta sai kuma ta dawo da baya ta yi ɗakin da Yakaka take ta ɗan ƙwanƙwasa ƙofar ,

Yakaka wacce take zaune akan sallayar da ta idar da sallah tana lazumi ta tashi ta buɗe mata ƙofar ,

" Falmata kin tashi ?

  "un bari nayi sallah , ta amsa mata tana ratsawa ta gefenta ta wuce banɗaki ,

Bayan ta idar da sallah ta É—aga hannuwanta duk biyu tana addu'a ,

Ta kwashe fiye da mintoci sha biyar tana addu'o'i , har zuwa lokacin da zuciyar ta tayi rauni gaba É—aya hawaye ya taho mata , sai ta fashe da kuka mai sauti ,

Yakaka wacce take azkar ta tsahirta , a hankali ta É—ago kai tana kallon ta , sai ta tashi daga inda take ta dawo kusa da ita ,

Dafata tayi fuskar ta na bayyana damuwa tace mata
  'Falmata meyasa kike kuka ? Wani abu aka yi miki ? Ko baki da lafiya ne ?  Ki daina kuka Falmata ki faɗa min abunda ke damun ki kin ji ?

Idanunta suna zubar hawaye ta riƙe hannun Yakaka , muryarta ɗauke da sautin kuka tace ,

" Mama bata da lafiya Yakaka , Tunda ta tashi tana da ciwo har turai mun je saboda lafiyar Mama amma ba'a dace ba , yanzu ma bata da lafiya zamu tafi da ita asibiti , ki mata addu'a Yakaka .

Wani irin tashin Hankali Yakaka ta shiga , zuciyarta na tsananta bugu tace ,

"Mama tana da ciwo tunda na haifeta ? Aina ciwon yake ?

" a cikin jinin ta , idan ciwon ya tashi tana shan wahala sosai Mama abun tausayi ce ,

Shiru Yakaka tayi cike da tausayin É—iyar ta ,

A hankali tace" kije ki shirya ku tafi Falmata , Allah ya bata lafiya , Allah ya warkar da ita babu ciwon da bashi da Magani  ,

Miƙewa Falmata tayi ta fita zuwa ɗakinta , tana fita kukan ta ya sake dawowa sabo , can cikin ranta neman hanya take da zasu yi magana da Yakaka , so take ta tambayeta meyasa ta ji suna hayaniya da Baban Mama ? Ba tare da ta nuna mata ta san zancen da suka tattauna ba , a sanin ta Yakaka kaifi ɗaya ce wataƙila ta fayyace mata dalilinta ,

Sai dai rashin samun ƙafar maganar da Yakaka ya sa tayi shiru da tarin damuwarta da ciwon Mama ya zo ya ninka mata ,

Bayan fitar ta kukan da Yakaka take dannewa ya taho mata, nadama marar iyaka ta sake rufe ta ,

"Ashe Mama ba ma mai lafiya bace amma ta tsallake ta tafi ta barta ? Haka ta dunga rayuwa da ciwo tun tana jaririyar ta ? Babu tausayi da kulawarta a matsayinta na uwa a gareta ? Ita kuwa anya Mama zata yafe mata idan ta girma labari ya iske mata ? Alƙawartawa kanta take yi tana sake jaddadawa bazata sake yin nesa da ɗiyar ta ba kome runtsi .

Kasa zama a É—akin tayi ta fito falon da babu kowa sai kwarafniyar Hajja daga cikin kitchen ,

Zama tayi akan kujera tayi jugum cikin allhini ,

A sukwane ya turo ƙofar ya shigo yana saɓe da Mama wacce tayi luruf , bai lura da Yakaka ba , ya ɗaga sauti dake bayyana tashin hankalin sa ,

"Fatima ki fito mu tai asibiti jikin Mama ya matsanta kada ta shiga hatsari ,

Miƙewa tsaye Yakaka tayi tashin hankali bayyane bisa fuskarta , jikinta har rawa yake ,

Yi tayi kamar zata taka taje inda suke sai kuma ta jaa ta tsaya , idanunta baki É—aya akan Mama , ba ko dubi fuskar Youssouf ba ,

Muryar sa ya sa Hajja fitowa da take kitchen tana aiki , turus tayi tana raba ganinta tsakanin Yakaka da Youssouf ,

"Babban soja barka da asuba ,

"Barka Hajja yaya hidima ? Mama batta lafiya yanzou zamou tai da itta asibiti ,

Take fuskar Hajja ta sauya daga mamakin da take yi zuwa Alhini ,

"Allah sarki kai wannan yarinya kina shan wahala , sannu Mama Allah ya baki lafiya , Babban soja Allah shi baku ladan jinya da hidima da ita ,

"Amin Hajja ,Amin

Ya furta dai-dai fitowar Falmata cikin hanzari  , idanunta hawaye shar-shar suna zuba , da kyar take ganin gabanta ,

"Hajja ina kwana , tace cikin muryar kuka ,

Cike da tausayawa Hajja ta amsa ,

"Sannun Falmata bari kuka haka nan , Allah dai ya bawa Mama lafiya kin ji ? Ai ke kece uwar Mama duniya da lahira .

Tana ƙarasowa Youssouf ya riƙe hannunta suka kama hanyar barin Falon ,

Sai dai taku biyu suka yi , Falmata ta waiga ga Yakaka wacce take tsaye idanunta cike da ƙwallar son sanin halin da Mama take ciki ,

Inda take hango alamar Yakaka ta nufa , tana zuwa ta lalubo hannun ta ,

" zo muje asibitin tare Mamar Mama ,

Babu musu Yakaka ta biyo ta , ganin haka ya sa Youssouf nufar waje bai ce ƙala ba ,

" Hajja mun tafi ,

Yakaka tace ,

bata amsa ba har suka ƙarasa barin falon tana bin Yakaka da kallon mamaki , nisawa tayi bayan wucewar su ,
    "o ni Hauwa'u naga abunda yafi ƙarfina , ji bi dan Allah yadda ta bi su ƙobare-ƙobare babu ko 'yar kara ? Geme-geme da ita ta shiga tsakanin su ,   Da ta san tana son ƴar tayi tafiyarta dandi ta bar ta ?? Tawa ta sameni nikam sai nayi da gaske zan hana yin ɓatatciya a gidan nan ,

***
Chapter 183 · 0% Book details