← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 269

Sashe 68

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Bayan awa ɗaya ya kammala ya ɗaura mata jinin da aka kawo leda ɗaya bayan yayi mata allurai ,
    Sai da ya sake jaddadawa nurses ɗin da suka karɓi aiki akan su kula da ita Ƙanwar sa ce ,  bayan yayi bankwana da likitan da ya ƙarbe shi a bakin aiki ya shigar masa da duk wasu bayanai akan marasa lafiyan da ya duba ciki har da falmata da ya roƙi Alfarma a lura da ita da kyau , abokin aikin nasa ya amsa da zai kula da ita sosai .
       Cikin takun da yake nuna tsabar gajiyar da yayi ya fito daga ɗakin , yana goge ruwan hannuwan sa da ya wanke da farin ƙyalle .
       Tana hango fitowar shi ta miƙe daga inda take durƙushe a jikin bango ta nufo shi ,"
        Cikin nazari ya tsaida idanun sa akan ta tana tahowa yana son tabbatar da zargin sa akan alamomin masu juna biyu da yake gani tare da ita alhalin shi a budurwa ya san ta .

Dakta ta farka ? Tana magana ? Jinin ya daina zuba daga jikin ta ? Ko na shiga na gan ta ??
      Bin fuskar ta da tayi jazur da kallo yake yana ganin yadda fatar bakin ta ta bushe idanun ta suka kumbura,

Bai amsa mata tambayoyin ba ,  yace mata

   Zo muje !

Ta bishi a baya tana waiwayen É—akin da falmata take ciki , so take tayi gaddamar bin sa sai dai ta kasa ,

A bakin wani É—an shagon da ake sayar da kayan sanyi da kayan fulawa irin su Biscuits, cake , meat pie , donut da sauran su , suka tsaya

   Duban sa ya mayar kan fuskar ta cikin kulawa yace me zaki ci marar nawi sosai ? Zaki sha Hollondia yogurt  ? Ko juice kika fi so ? Cake zaki ci koh meat pie ?

  Wani jirkitatcen kallo ta yi masa , falmata tana cikin yanayi irin wannan har shi yana tunanin zata iya cin wani abu ? Ai ita ko ruwa baza ta iya sha ba idan ba ta ga farkawar falmata cikin ƙoshin lafiya ba .

  Sunkui da kan ta tayi daga kallon fuskar sa ,' cikin siririyar murya tace
    Bana cin kome bana jin yunwa , dakta dan Allah ya jikin falmata ? Ta samu sauki , ka kai ni na gan ta dan Allah ,
    Bai amsa mata ba sai ya maida ganin sa kan mai shagon da yake tsaye  ta cikin ɗan shagon sa yana kallon su .

    Bamu hollondia yogurt babbar roba ɗaya da Chii exotics babba ɗaya , meat pie guda uku , tare da ruwan roba guda ɗaya .

    Suna tsaye ya haɗa a leda ya miko musu , dakta hamza ya karɓa gami da miƙa kuɗi aka bashi chanjin sa ,

A takaice yace mata
  Mu tafi ! Yana mai yin gaba
  Cikin ƙosawa ta bi shi a baya .

Wurin da motar sa take ajiye a wajen tsayuwa na musamman ya ƙarasa , gami da buɗe motar ya shiga
  Ita ma yayi mata umarni da ta shiga bayan ya buɗe mata ɗayan bangaren ,"
  Ta shiga ta zauna gami da mayar da kan ta jikin murfin motar ta kwantar tana jin wani irin yanayi marar daɗi yana taso mata , sam ita bata son takurar da yake yi mata a koyaushe idan suka haɗu ,!

   Ledar da kayan da ya sayo suke ciki ya ɗora mata akan cinyar ta .
    Bana son musu ko doguwar magana ki cinye kuma ki shanye duk abinda yake cikin ledar nan , ƙanwar ki na mata aiki na bata magunguna yanzu haka bacci take daga ta tashi zaki ganta insha Allah baza ta ɗauki lokaci mai tsawo ba zata warke, idan har kun zauna an bata kulawar da ta dace baku gudu ba !

Sanyin kayan da suke bisa cinyar ta suka haÉ—u da jin daÉ—in cewar falmata tana raye an yi mata aiki har ma tana bacci suka tayar mata da kishirwar da ta jima tana ji ,
   Ba tace kome ba , ta buɗe ledar gami da ɗaukar gorar ruwan ta kunce bakin ta kafa kai ta fara sha bayan ta muskuɗa ta juya tana fuskantar murfin motar ta bashi baya ,"

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin farin cikin sake ganin ta yana ratsa shi , ya zubawa bayan hijabin ta ido da duk jinin falmata ya ɓata , '

   A garin yaya harsashi ya same ta ?
  Ya jefa mata tambayar lokacin da ya ga ta gama shan ruwan ,"

Muna cikin rumfa ne a bakin kasuwa

Bakin kasuwa ? ya maimaita
   Me kuke a bakin kasuwa a wannan yanayin da gari yake ciki na hargitsi ?

Daman anan muke zama
   Ta amsa masa

Kamar yaya ? Yaushe kuka dawo garin ?

   Ɗagowa tayi ta dube shi
Daman muna gari , a bakin kasuwa muke kwana a cikin rumfar mai shago !

  Ji yayi kan sa ya wani irin juyawa , take alamun da ya gani na masu ciki a tattare da ita ya faɗo masa cikin rai ! Shi ƙwararren likita ne wanda ya san aikin sa ya kuma faɗaɗa tare da zurfafa bincike cikin duk wani ilmi da ya shafi lafiyar ɗan adam , ba sai wani ya faɗa masa ba ba kuma sai yayi gwaji ba babu shakka cikin kallon tsanaki da yayi wa yarinyar ya fahimci tana da juna biyu , toh amma ta yaya haka ta faru ?
Wani mummunan tashin hankali ya ziyarce shi lokacin da yayi hasashen abun da ya faru ga rayuwar yarinyar , da ta yadda aka yi ta samu cikin

  Tare da waye kuke kwana a bakin kasuwa ya tambaye ta yana tsare ta da kallon tuhuma .

   Mu kaɗai ni da falmata !

Bai san lokacin da ya birkito da ita tana fuskantar shi ba ,"
     Wacce irin rayuwa kuke yi a bakin kasuwar ? Baki da lafiya faɗa min waye yayi miki ciki ?

     a tsorace ta ɗago kan ta tana kallon sa , yadda taga jijiyoyin kan sa sun tashi idanun sa sun kaɗa sun yi jaa ya sa ta matuƙar razana ,"

Nan take hawaye suka ɓalle a idanun ta , ta sake maƙure kan ta da jikin kofar motar

   Sakin hijabin ta yayi tare da yin baya da kan sa ya ɗora a jikin kujerar da yake zaune bisa ya runtse idanun sa , tunani iri-iri suka rikito masa ,
        Wani ƙazamin ɗan iskan ya riga ya bata rayuwar yarinyar tun a ƙaracin shekarun ta , mutanen  duniya mafi yawan su azzalumai ne , sun cutar da rayuwar yarinyar saboda rashin galihun ta , ji yayi zuciyar sa ta raurawa idanun sa sun kawo ruwa ," wani irin tausayin ta da ya danne tasirin bacin ran sa da zafin kishin da yake ji ,ya mamaye ruhin sa ,
Allah sarki talaka !
  Ya furta a cikin ran sa ,
    Murya ƙasa ƙasa yace
Ki koma ki zauna a inda mutane suke jiran Æ´an uwan su marasa lafiya , zan je na dawo ki tabbatar kin ci abinci , kar ki zauna da yunwa ,
    Kamar jira take yayi mata umarni ta ɓalle murfin motar ta fita , hankalin ta gaba ɗaya yayi kan falmata , bata damu ba sam da  sauyin yanayin da ta gani tare da shi da damuwar da ta bayyana a gare shi , bare har tayi wani dogon nazari akan hakan ,"
      Gyara zaman hijabin ta tayi tare da sake riƙo ledar hannun ta da kyau ,ta kama tafiya ,"cikin ran ta tana aiyana baza ta sha wannan kayan daɗin ba falmata zata ajiyewa tana farkawa ta bata ta ci ta sha !

 
Tuƙi yake yi akan hanyar sa ta komawar sa gida amma rabin hankalin sa bai tare da shi , yana ga tunanin halin da yarinyar ta tsinci kan ta a ciki , ba zai yiwa kan sa ƙarya ba tun da jimawa ya fahimci ya faɗa tsundum cikin so da ƙaunar yarinyar da ko a mafarki idan aka ce masa shi zai so mace irin ta zai ce ƙarya ne , toh amma tun da ya gagara kaucewa faɗawa a soyayyar ta , sai ya ɗauki hakan a matsayin kaddarar sa ce watakila matar auren sa ce ubangiji ya turo masa ita a haka , dan haka sai ya shiga neman hanyar da zai yi ya gyara ta ta zamto irin macen da shi yake son ta kasance matar aure a gare shi , karatu yake da nufin sa ta a farko bayan ya kai ta gidan su wurin mahaifin sa , tayi karatu mai ɗan zurfi zuwa ko da matakin diploma ne sai ya aure ta ,

Toh sai kuma ƙwatsam ta ɓace masa , ya sha wahalar neman ta bata nan ! , har ya fara dangana da rashin ta sai kuma ta ɓullo da wani al'amari mai girma a tare da ita ,"ciki ba tare da tayi aure ba , baya tunanin ko uban cikin jikin nata ta san shi ," Al'amarin ba ƙaramin firgita shi yayi ba ya taɓa ran sa fiye da zato , saboda soyayyar gaskiya yake yi mata ,"

A tun bayan barin ta da yayi yanzu ya kamo hanyar sa yake bincikar kan sa tare da ƙwanƙwasar zuciyar sa ko Allah zai sa ya ji wani sauyi na daga soyayyar da yake mata ta zuwa wani yanayi na ƙi ko kaɗan ne a saboda girman bakon al'amarin da yake tare da ita marar kyau ?
Wanda zai yi amfani da hakan wurin yakice ta daga cikin ran sa baki É—aya ya shafe babin rayuwar ta daga ran sa ?
Chapter 68 · 0% Book details