← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 269

Sashe 104

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Turus !
Biyamuradi Youssouf yayi yana bin fuskar ta da kallo , ƙwarai ya shaida waɗannan idanuwan nata masu girma , ita ce wannan ƴar yarinyar da ta nemi yi masa faleƙe lokacin da ya fara tako kafafun sa cikin wannan gidan , biki , a watanni baya , ashe rashin sani shi yafi dare duhu , ashe ya tako har gidan da take lokacin da yake bulayin neman ta ? Allah ya raba ganawa a tsakanin su ,

Wani tsoro ne ya ji yana taso masa daga ƙarƙashin ran sa , tsoron kar ƙanwar ta ta san kome ? Kar ta tona asirin da shi da yakaka suka binne ,! Kar ta furta kalmar da zai shata layi tsakanin sa da mallakar ƴar sa , dan haka cikin sarƙewar harce yace ,

    Du-duba kin ka ce baki shaida ni ba ?  Baki gane ni ba ?
  
  Cikin hargagin kuka tace waye kai ?  ni ban san muryar ka ba , aina ka san mu ?  Ni da yakaka bamu da kowa a duniya kowann mu sun mutu , sai mu biyu a karshe Yakaka ma ta mutu ta bar ni tare da baby , bamu da kowa ni da baby , Baba wallahi ƙarya yake yana so ya ƙwace min baby dan Allah ku hana shi taɓa ta ,

  Wani kallon yatsutsu hajja mai wurya da daman cike take da halin ƙwalafaci da rashin yardar da falmata take gwadawa kowa akan baby mama , tace
   Ji min karfin hali ?? Ji min abun mamaki ƙurege da faɗa wa zomo daɗin ƙanzo , yanzu ke saboda Allah yarinyar nan un un un Falmata kike da suna ko wa ?? Yanzu ke uba zaki hanawa ɗaukar ƴar sa ?? Ina kika taɓa jin anyi haka ? Ina kika taɓa jin ɗa ya zama ɗan mace da dangin ta ita kaɗai ?? A rashin yardar taki da kowa kuma har da uban ƴar ?? Ni dalla bani ƴa na miƙata ga uban ta , har akwai martabar da ta zarta ta mahaifi ga ɗan sa , ?

  Kukan da falmata ta fashe da shi wanda ya ja ƴar jaririyar ma ta tsanyara kuka shi ya sa Youssouf zabura akan kafafun sa ya miƙe ya tsaye ,

    Kyale matta ɗiyar , batta ta cigaba da riƙon ta ,

Fatima zahra, yi shiru abun ki babu mai raba ki da É—iyar nan , É—iya ai taki ce , ki daina kuka kin ga ita ma kuka take ,

    Lallashin ƴar ta shiga yi tana yi tana share hawayen ta , '

Duban sa ya maida kan prof da yake yawo da idanun sa a kan su, cikin ruÉ—ani yana son fahimtar mai gaskiya a tsakanin su ,"

Baba Fatima ta samou watta larura ne ?
  Ya furta hakan da sigar tambaya cikin son cire zargin da ya fara hangowa a idanun prof ɗin ,

  Bata da wata larura bayan wacce muka gan ta da ita ta rashin gani , sai dai ko rashin ƴar uwar ta ya sa ta a ruɗani ,!

Hamdala Youssouf yayi a cikin ran sa , ashe ma makauniya ce , idan haka ne kome zai zo masa da sauƙi ,

Babu shakka ta shiga É—imuwa da yassa ta gaza gane ni , a bar ta kar ayi mata zancen kome har zouwa lokacin da zan dawo bayan kammaluwar aiki na ,

  Toh babu damuwa Allah ya kai mu lokacin ,
   Fatima ku koma ciki tunda dai kin ƙi a bashi ƴar ,

  Falmata da bata saurarar zantukan su ta himmatu wurin rarrashin ɗiyar da take gaba da sauran mutanen da suke wajen a wurin ta ,
cimak!  ta miƙe tsaye ,  riƙe da jaririyar da take ƙoƙarin komawa baccin ta ,
    Hajja mayar da ni ciki
Tace ga hajja mai wurya wacce take ta faman kyeɓe baki ,
   Yanzu Allah baza ki bada ƴar nan ba Baban ta ya gan ta falmata ?

   Da sauri Youssouf da har lokacin bai zauna ba yace , ƙƴale mata ɗiyar nan Babaa , batta ta cigaba da riƙon ta , ita ma ɗiyar ai tata ce ,"
  
  Ta gaban sa suka zo giftawa , yana bin su da kallon ƙwalafacin son ya ga ko ƴar fuskar ƴar ta sa,  yadda falmata ta kumburo fuska ta haɗe girar sama da ta ƙasa yaso bashi dariya ,ita a dole kar a taɓa mata ƴar ta ,

  ƙwarai sai ya ji ta burge shi , yadda ta jajirce take ƙoƙarin bada kariya ga ɗiyar sa ya motso shauƙi daga ƙasan ran sa , ashe ba shi kaɗai bane yake jarumi akan ƴar ta sa , ashe ba shi kaɗai bane yake Ƙoƙarin bata kariya , ashe bayan shi ƴar sa tana da wata ƴar ƙaramar katangar da take kare da ita , da idan ta bunƙasa zata iya zama dangar dutse da babu saran da ya isa ya samu na bayan ta , madallah da ke FATIMA ZAHRA .

A gurguje Youssouf yayiwa Prof sallama da zummar dawowa nan da ƙasa da kwanaki arba'in lokacin da zai kammala aikin sa , zai dawo tafiya da ƴar sa ,

    Zaro damin kuɗi yayi daga Aljihun sa ya ajiye a gaban prof ,

  Baba ga wannan a ƙara cikin hidimar gida madallah nagode da karamcin ku ina nan dawowa ba da jimawa ba !

Kul ,
  Ɗauki kuɗin ka , bazan karba ba , hidimar fatima da jaririya zai cigaba daga aljihuna kamar yadda yake a tun farkon zuwan su har sai lokacin da riƙon su ya bar hannun na , dan haka ka ɗauki kuɗin ka , Nagode

  Ganin ba fuska ya sa Youssouf ɗaukar kuɗin sa , godiya mai tarin yawa yayi masa kafin ya miƙe yana barin gidan
   Cikin ran sa da addu'ar Allah ya sa har ya dawo yarinyar nan da aka ƙira da suna fatima bata ɓata masa shiri ba , sai dai yana jin bama zata iya ba saboda ganin sa yafi kowa iko da ɗiyar sa nan duniya !

******
Abuja

Cikin sati biyu duk wani shirin makaranta ya kammala ga Yakaka , inda samy baby ta zaɓar mata ,"Eyes Scholars School ,"wacce take makarantar boko da take chakuɗe da arabi tsantsa, a matsayin makarantar da take so yakaka ta dunga karatu ,

Duk da cewa Alhaji Gali attajiri ne kuma fitatcen É—an kwangila amma sai da aka samu tsaiko gurin É—aukar yakaka a makarantar , domin a cewar hukumar makarantar yakaka bata chanchanta da shiga ajin gaba da primary ba bayan interview É—in da aka mata kamar yadda samy baby ta so a sanya ta , hukumar makarantar ta tabbatar musu da cewa ko É—aliban su Æ´an primary school sun wuce yakaka a matakin karatu ,

Bayan kai kawo da Alhaji Gali da shi ke É—auke da nawin kome na dangane da karatun yakaka , ya dunga yi

Kuɗi da Alfarma suka yi aikin su inda hukumar makaranta ta amince da shigowar yakaka cikin jerin ɗaliban su ƴan matakin ajin farko na secondry school jss1 , tare da sharaɗin Alhaji Gali zai ɗauki mai yiwa yakaka ,"extra lesson",koyarwa na mussaman daga cikin malaman su na makarantar da kuma zai dunga biyan malamar a duk wata , domin a cewar su chakuɗa irin yakaka da bata san kome ba tare da sauran ɗaliban su zai iya kawo naƙasu ga karatun sauran ɗaliban su da suke aji guda da ita wanda a ƙarshe zai tado da ƙorafi daga iyayen yaran da zai iya kaiwa ga duƙushe tasirin ingancin makaranta a idanun jama'a ,

Ba tare da ƙorafin kome ba Alhaji Gali ya amincewa sharaɗin su , ganin sa ai duk abunda yayiwa samy baby bai faɗi ba , tana biyan sa dan haka bashi da asara ,

Nan take ya lale ya biya kuɗin malamar da zata dunga yin extra lesson ɗin inda aka zaɓar mata wata yarinyar mace da ashekaru zata haifi yakakar , tana tsakanin shekaru 36-38 , malama maryam ita ke ɗaukar su yakaka fannin I.R.K , ( Isalamic Religion knowledge )  abunda kuwa ya sa hukumar makaranta ta zaɓe ta shine domin zamantowar ta jajirtatciyar malama da ta kware a harkar koyarwa , duk da cewa fannin addini take koyarwa amma sun san zata iya koyar da yakaka English da Arabic sosai ta yadda gaba zata fara gane karatu da kan ta , bugu da ƙari gani da suka yi location ɗin gidan ta da na su yakaka duk ɗaya ne , dan haka suka ɗora mata wannan nawin ,

Babu musu malama maryam ta ƙarbi form ta cike a matsayin ta na malamar da zata dunga extra lesson na musamman ga sabuwar ɗaliba yakaka , ranta cike taf da farin cikin samun wannan damar na amsar wani ƙarin kuɗi akan albashin ta na kowanne wata wanda kusan da shi rayuwar su ita da ƴaƴan ta da mijin ta suka dogara , zuciyar ta cike da burin zage ƙwanji ta koyar da yakaka da dukkanin iyawar ta har sai watarana anyi mamaki , .

Ga bangaren yakaka bata jin kowanne  irin yanayi dangane da sabuwar rayuwar ta na jin daɗi ko akasin sa , iyaka ta san har zuwa yanzu da take samun wajen sati uku a sabuwar rayuwar ta , kewa tare da so gami da tausayin rayukan nan biyu da ta bari a bayan ta yana nuƙurƙusar zuciyar ta tare da yiwa walwalar ta kisan mummike ,

Ko yaushe kewar falmata ta dame ta takan zauna tayi kuka iya kuka , tana son sanin a wanne hali suke ciki ita da Æ´ar jaririyar da ta bari ? Tana son jin tashin muryar falmata ,
Chapter 104 · 0% Book details