← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 269

Sashe 96

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kalma-bayan-kalma kalaman samy baby ke yin dawurwura cikin kunnuwa suna zarcewa ga kwakwalar yakaka , sai dai fassarar su sun gagari ƙarfin tunanin yakaka ,
   Meye tace ne ? Me take nufi wai ? Anty samy tace ni wawiya ce jahila amma ai bata ce ni mahaukaciya bace , alhalin kuma ni nasan na haukace ne ,"
   Zamewa tayi ta kwanta a tsakanin kujerun gurin tare da curewa ta duƙunkune cikin hijabin jikin ta , fata take a mata wani mummunan mari , ina ma fankar da take juyawa a sama zata faɗo ta daki kanta ko zata samu ta farka daga mummunan mafarkin ido biyun da take ,"
    Wai Anty samy duk daman ƙarya take mata , wai Anty samy yaudarar ta tayi , wai daman ashe Bature kam silum ya jefar ta ne ba tare da ya taɓa neman ta ba , ashe ya manta da ita , ita ke dakon soyayyar sa , wai ashe ashe an raba ta ne da Doctor hamza mai taimkon su ita da ƙanwar ta , tuno da shi tayi da tashin hankali tare da tausayin da ta hango ɓaro-ɓaro cikin ƙwayar idon sa lokacin da take cikin magagin ciwon naƙuda , ajiyar zuciya ta fara saki da sauri da sauri tana jin yadda tsokar jikin ta take ƙarƙarwa sakamakon wani mugun sanyi da taji yana lulluɓar ta ,"
    ME NAYI WA ANTY SAMY DA TA JEFA RAYUWA TA A WANNAN MASIFAR ?? Tambayar da ke yawo cikin zuciyar ta kenan lokacin da take rufe fatar idanun ta da ko ɗiris babu ɗigon ƙwalla , "wani tashin hankali yafi gaban kuka ,"

      Sai yamma liƙis samy baby ts fito ta sha wankan ta ta haɗe cikin wata diguwar rigar roba mai bin jiki , kasantuwar ta ƴar chas-chas sai tayi kyau a cikin kayan ," bata ga yakaka a falo ba dan haka sai ta leƙa ɗakin da ta mallaka mata nan ma har cikin banɗaki ta leƙa babu alamun ta shiga cikin sa dan haka ta fito da sauri da nufin leƙa waje ko dai ta fita ɗin ne da gaske ???
     Cin karo tayi da ita kwance a inda ta bar ta tun safe , ta Ƙudundune daga kan ta har ƙafafun ta , wani irin tausayin yarinyar ta ji ya taso mata , ita da kan ta ɗazu ta jima bata yi bacci ba da ta kwanta tana ta saƙawa da warwarewa , ganin laifin kan ta take , akan ƙaryar da tayi mata ta zo da ita ba tare da Aminccewar ta ba yayin da wani sashi marar  ƙarfi kuMa ke ganin ai daidai tayi taimako tayi kamata yayi ta Gode mata ,

Sunkuyawa tayi tana tashin ta a hankali ,"
   Yakaka , wacce daman ba bacci take ba ta janye hijabin ta ɗago kan ta tana fatan ta buɗe ido ta ga kome mafarki ne , ta gan ta a ɗakin su da Doctor hamza ya mallaka musu , tare da ƙanwar ta , baby mama kuma tana fatan taji motsin ta a cikin cikin ta ,

  Ganin samy baby ce ke tashin ta cikin gidan da ta tabbatar nan ƙaddara ta jeho ta rayuwa cikin sa , yasa ta ji zuciyar ta na yadda da abunda tunanin ta ke tabbatar mata cewa ba mafarki bane , kome ya faru ne a zahiri , ita yakaka a duniyar da take yanzu ita kaɗai ce jal , babu Falmata babu abunda ke cikin ta babu kuma Doctor Hamza mai taimakon su , duk tayi musu bara'a ta tsallake su bisa jagorar wawancin ta tare da jahilci da suka biyo ta kan mummunar rufa-rufa tare da gadar zaren da samy baby tayi mata , da taimakon ta ta aikata babban kuskuren da baza ta taɓa yafewa kan ta ba ,"

   Kallon samy baby take kamar yadda ita ma samy baby ke bin ta da kallon tausayi ,   
yakaka ki tashi haka Dan Allah ki je ki ci abinci kiyi wanka ki gasa jikin ki , kin san fa jego kike ina miki tsoron kar jikin ki ya lalace ,
   Toh
tace tana mai yunƙurawa ta mike , da sauri  samy baby ta kama ta kai tsaye banɗaki ta kai ta tare da sake haɗa mata ruwa mai zafi tace tayi wannan sosai ,"
  Toh
    ta sake amsa mata ," cikin daɗin ran fara samun haɗin kan yakaka samy baby ta nufi ɗan kitchen ɗin da taje da shi a gidan domin dafawa yakaka ɗan wani abu mai sauƙin dahuwa da zata iya ci ,
   Nan da nan ta dafa mata indomie ruwa-ruwa da soyayyen ƙwai guda biyar ta haɗo da ruwa ta kai mata ɗakin , nan ta tarar da ita zaune akan tiles ɗin ɗakin ta har lau tayi wanka ta maida kayan jikin ta da hijabin da ta cire
    Yakaka kul ki daina zama haka a ƙasa jego kike ba'a son mai jego tana zaman ƙasa tashi ki koma bakin gadon ga abinci ki ci , zan kawo miki wani kaya ki sauya kafin ki warware muje ayi miki sabbin ɗinki kin ji ?   Toh
Tace tana miƙewa ta zauna a bakin gadon kamar yadda tace .

   Wasa-wasa cikin sati guda da samy baby tayi tana gida kullum tana kula da yakakar , ta lura tamkar yarinyar ta koma shiru-shiru , wacce ta samu taɓin hankali bata un bata un'un kome tace mata kawai "toh" take cewa
   Hirar duniya wacce take bukatar bada amsa samy baby tayi wa yakaka amma yakaka taƙi cewa uffan , iyakaci idan ta bata umarnin yin abu take zata yi babu gardama,

   Ranar da ta cika sati da kawo ta gidan ta shiga ɗakin yakakar da safe , cikin ran ta tana aiyana idan har ta tabbatar yarinyar nan ta samu matsalar taɓin hankali ne , sauri zata yi tasan yadda tayi ta maida ta inda ta ɗauko ta , ah to ita ina zata iya rainon mahaukaciya ? 

   Zaune ta tadda yakakar tayi jigum tana kallon windown ɗakin ,"
   yaks ya kike jin jikin ki yau ?
samy beby ta tambaye ta ba dan tana sanya ran samun amsar yakaka ba , ga mamakin ta sai ta ga yakakar ta juyo da kallon ta kan ta , cikin wata muryar dake fitowa da sauti marar amo tace
    ANTY SAMY KI KAINI MAKARANTA , KI SAKA NI A MAKARANTA INA SO NAYI KARATU INA SO NA SAMU ILMI.
Wata irin dariyar murna samy baby tayi tana mai zama gefen gadon ta riƙo hannayen yakaka ,
   Yaks , yaks ko kefa ? Kin fara fahimta ta ko yaks ? A yau yau zan sanya a fara nemar miki makarantar da za'a sanya ki , nayi alƙawarin karatu sai kin gaji yaks , Ilmi ai shine gishirin rayuwa bari ki ga ina wayata ?  Bari naje na ƙira Alhaji Gali , makaranta sai wacce kika zaɓa yaks , tace tana ƙarasa barin ɗakin har da ɗan gudun ta ,

Da ido yakaka ta bita cikin ran ta tana sake É—aura É—amarar goge kalmar JAHILCI daga gare ta da tafi bada tabbacin kome da ta aikatawa kan ta da wanda wasu mutane suka wanzu suna aikata mata , ya faru ne ta dalilin

Jahilcin ta , Kalmar wauta kuwa a cikin satin ta fara nesanta kan ta da ita , domin a ɗamarar ƴakin da ta ɗaura bata da buƙatar tafiyar tare da wannan kalmar ta wawanci da aka danganta ta da ita , "

Bata sani ba ko zata iya , ko burin ta zai kai ga cika , ko watarana zata cimma manufar da ta lulluɓe cikin ranta a tsawon sati guda da ta wanzu babu dare ba rana tana saƙawa tare da kuncewa cikin ran ta , tana matse zuciyar ta tana ƙwanƙwasar ƙwaƙwalwar ta har ta samawa kan ta mafitar da take ganin zata iya kaiwa gaci ta hanyar ta ,

bata sani ba shawarar zata kai ta inda take so ko kuwa zata ɗora ta ne kan wani kuskuren , bata sani ba ta raba kan ta ne da kalmar wawanci ko kuwa ta sake tafiya ne bisa jagorancin wani wawancin ? Ko ma meye ta bar kome ta janye hankalin ta daga kan kowa da kome ta ɗaura ɗamarar yin YAƘI DA JAHILCI ."

  Maraɗi Niger

Tafeeda ne zaune a gaban hajiya umma ya tanƙwashe ƙafafun sa babu kowa a falon ta na ciki daga shi sai ita ,
     Ka tafi zouwa nigeria ka zo min da bayani mai gamsarwa a game da abokin ka. Tabbas yana cikin wani yanayi wanda yake boyewa daga gare mu , kayi gaggawar taryar sa a chan a magance matsalar tun kafin ya samu isowa da ita zouwa cikin gidan nan , kasan dai duk wata matsalar da ta shafi yarima idan har ta shigo gidan nan ta shafi mutanen cikin masarauta ne baki ɗaya ," 

Toh ranki ya dade cikin yardar ubangiji a gobe zan fara neman iznin tafiya daga shugaba na wurin aiki , zouwa ƙarshen sati na kan iya samun iznin tafiya , ki kwantar da hankalin ki , babu abunda zai faru ga Biyamuradin maraɗi

Allahu shi sa haka , haka muke fata , Allah shi muku Albarka baki ɗaya ya kare ku daga faɗawa tarkon Maƙiya , kana iya komawa yaro na ,"

Ameen Ameen yake amsawa , ya miƙe kan sa a sunkuye yana faɗin ki tashi lafiya ranki shi daɗe ,"
Chapter 96 · 0% Book details