Sashe 25
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe huÉ—u jirgin su na sojoji ya ajiye su a cikin garin maiduguri inda zasu kwana zuwa washegari su wuce inda suka nufa ,"
Tun isar sa babbar hedkwatar soji na birnin na maiduguri , hankalin sa ya tashi da ganin irin taron mutane maza da aka gaggarƙame cikin ɗakunan horo , a galabaice matuka , cikin azabobi da horo mai tsanani wanda a gaban idanun sa ma yaga an fidda gawarwakin jama'a daga cikin ɗakin horon da azaba ta kashe su ,"
Duk da cewa a matsayin sa na babban soja hakan ba bakon abu bane ,toh amma zuciyar sa ta taɓu da yaji daga bakin wani sojan nigeria cewa waɗannan mutanen , mutane ne waɗanda aka kama akan zargin suna da hannu wurin tada tarzomar boko haram da ba'a kai ga tabbatar da laifukan nasu ba ,sune a jibge a garƙame cikin horarwa da azabtarwa , yunwa da ƙishirwa ,rashin isashen muhalli ta yadda wasu a tsaye suke wuni , wasu a tsugunne ,wasu a tanƙware , wanda yawan su ya tasamma dubunnai ,"
Gagara samun nutsuwar zuciya yayi bayan ya koma masaukin sa ,zuciyar sa sai kai kawo take da tunanin san samar da mafita ga waɗannan bayin Allah waɗanda a zahiri akwai zalinci cikin irin wannan ajiyar da ake musu ,kamata yayi a miƙa su ga kotun ƙasa ta yankewa kowa hukuncin sa dai-dai da shi waɗanda basu da laifi a sake su , wannan hukuncin ajiye su ana gana musu azobobin da suke kai su ga rasa rayukan su yayi tsanani da rashin dacewa ,"
Har gari ya waye bai sake marmarin fita ba sai da suka tashi barin ainahin cikin garin maidugurin zuwa bakin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno , a tare da shi da tawagar sojojin su na niger da kuma ƙarin wasu sojojin nigeria , zuciyar sa cike da tausayin al'ummar da sanadin boko haram ta ɗaiɗaice suka bar ainahin cikin garin na maiduguri .
*******
Cikin kwanaki biyar ɗin da su yakaka da falmata suka ƙara cikin sansanin su basu tsinci kome ba sai tarin wahalwalun da suka sake jikkata gangar jiki da ruhin su ,"
Domin zuwa yanzu karfi da yaji su yakaka sun zama Æ´an aikin matayen nan da aka haÉ—a su rayuwa a É—akuna É—aya da su,"
Ta bangaren yakaka matar da suke kwana tare wacce ake kira "fanne" ta maida ta baiwar ta wacce take yi mata bauta nata da na Æ´aÆ´an ta , tun daga kan wankan yaran biyu har zuwa wankin bargunan su da kullum ta Allah sai yaran sun zabga fitsari , wankin Æ´an tsirarun kayan yaran da koyaushe ba'a rasa shi da guntun kashi da fitsari wanda yakakan take shan wahala wurin wankin saboda rashin isashen ruwa da sabulun wankin ,uwa uba rainon yaran da suke kusan yini goye bisa bayan ta duk wata jigila da su take yi suna É—ane a baya , ta sauke wannan ta goye wancen ,uwar su kuwa tana chan cikin yaran mata tana zuba hira da É—inkin hular ta ,"bata chas bata ass ,
Ga falmata kuwa duk da kasancewar ta miskiniya amma hakan bai sa ajus ta É—aga mata kafa daga sanyata ayyuka ba ," tun farar safiya idan ta tashi daga kan shimfiÉ—ar da a yanzu ita kaÉ—ai ke kwana a cikin gidan sauron sakamakon irin azabar da take ganawa falmatan cikin dare ya sa ta hakure ta samawa kan ta salama daga ,zagi hantara ,hauri , mangari da mintsinin da ajus take buwayar ta da su cikin dare , ta bar kwana a gidan sauron ta komo bakin kofa tana shimfiÉ—a zanen ta tana kwanciya bisa ,"
amma duk da hakan ita ke lalubawa ta naɗe gidan sauron ta kuma ninke kayan shimfiɗun da ajus ɗin ta kwana a kai , bata bar ta haka ba kullum ita take ɗebo mata ruwan wanka a bokiti da na tsarki a buta , daga bakin famfo inda anan suke samun damar haɗuwa ita da yakaka wacce ita ma take zuwa ɗibo ruwan hidimar fanne da ƴaƴan ta , famfon baki uku ne rak da shi kuma idan aka tayar da injin bada ruwan karfe biyar na asubah zuwa karfe bakwai na safe ake rufewa sai kuma lokutan sallah da shi ma na ɗan kalilan ɗin lokaci ne sakamakon rashin man tada injin tare da rashin wutar lantarki ,"
dan haka yaƙi ne tukuru yake tashi wurin kokowar ɗibo ruwan wanda mai karfi ke ture na ƙasa da shi ya samu ya ɗiba ,"ire-iren su yakaka kuwa da kƴar da suɗin goshi da faɗawa cikin dagwalo tare da jin ciwo take samu ta cikawa falmata nata kayan ɗiban ruwan "da yakakan take tsaida ta a gefe ta hana ta shiga turmutsutsun ɗibo ruwan" ta kuma ɗibo nata , wanda mafi yawancin lokuta ake kashe injin bada ruwan akan bokitin ta ," hakan ya sa har yau da suke cika kwanaki shidda wanda yake dai-dai da kwanakin su bakwai da barin mahaifar su ,fatar jikin su bata ga ruwan wanka ba sai dai ɗaurayar kafafu da hannaye zuwa fuskokin su da suke yi da ruwan alwala ," dan haka duk suka bi suka sake hautsinewa tare da ficewa daga kamannin su ,suka zama yarkace yarkace tamkar sabbin mahaukata.
Ɗan dama-daman yagana ce wacce daman ita ta ɗan fi su wayewa da buɗewar idanu saboda ta tashi a alkaryar da take da wadatuwar wayewa , dan haka bata yadda kowacce mace ta nemi taka ta, bata yadda tayi aikin bauta ga kowa , sannan kuma abokiyar kwanan ta ma yarinya ce budurwa sa'ar ta dan haka suke yin chanjaras daga ta nemi kawo mata wargi ," damuwar ta yanayin rayuwar da take gudana ne a wurin da yanzu ta tabbatar ba gidan gwamnati bane , wuri ne na kazo na zo rayuwa ce irin ta daga ƙwari sai gwaiwa ,kowa kan sa ya sani rayuwa ce ta nafsi-nafsi ,uwa uba rashin wadatatcen abinci ,da ruwan sha ba'a maganar kayayyakin gudanar da rayuwa irin ta yau da kullum kamar su sabulan wanka da na wanki ,suturu da sauran su ,"
wanda tun zuwan su bata ga alamun za'a taimaka musu da waÉ—annan ba ," ga fatara da ta addabe ta saboda rashin koh kwandala da take matsayin mallakin ta ,"
gefe guda na zuciyar ta tana tausayawa abokan tafiyar ta da a yanzu ta fisu ƴanci , ta kuma sha zama ta gwada musu yadda zasu ƙwaci ƴancin kan su daga hannun ƴan iskan mata azzaluman da suka maishe su bayin su ,
sai dai daga yakakan har falmata babu mai kumajin iya kwatarwa kan sa ƴancin saboda rangwamen wayewar kai tare da ƙarancin shekaru ,
ɗan gwara ma falmata idan ƙumu ta ƙuma mata kai ta kan iya yin hobbasa ta nemi matsera daga hannun ajus ɗin ta hanyan yi mata batar dabo ta gudu bayan ajujuwa cikin datti da guntun najasa tayi zaman ta ,"
amma ga yakaka babu fuss , akan ga ƙwanjin ta ne kadai idan aka taba mata sanyin idaniyar ta falmata a gaban idanun ta , amma akan kan ta kam raguwa ce ta kin ƙarawa ,"
Dan haka kamar yau da suke zaune su ukun turmus a cikin rairayin da ganyayyakin bishiyar darbejiya ya lulluɓe ,yagana ta dubi fuskar yakaka da take duk jirwaye da lollori "( abun ka da farar fata )
  "Nikam yakaka wannan mawuyacin halin da muke ciki a sansanin nan namu ya isheni , domin ban hango ranar yankewar wahalar mu ba a haka muna zaune cikin rashin sanin makomar rayuwar mu ya kamata mu samarwa kan mu mafita tun kafin ta ƙure mana ,"
 dan zunkuɗa goyon yaron da ke ɗane baƙe-baƙe akan bayan ta wanda iskanci ne irin na yara ya sanya shi sanya kukan sai an goya shi domin yana yawon sa da gudun sa ko'ina ,"
  "Hmm yagana kenan toh wace mafita kike tunanin muke da ita , mu da bamu da kowa kuma bamu san ko'ina ba sai nan ɗin ? Ai ina ganin haka zamu cigaba da hakuri har zuwa lokacin da ubangiji zai sauƙaƙa mana domin nasan yana sane da mu ," ta karashe zancen tana mai kokarin maida ƙwallar da ta ciko mata a ido
   Yangana ta nisa cikin kallon sashin da falmata take wacce gaba ɗaya ta maida hankalin ta ga gefen su tamkar dai idanun ta suna kallon wani wajen , da azahiri kunnuwan ta tarwai suke tana kuma sauraran tattaunawar tasu ,kawai bakin ciki da damuwa ne suke danƙare a kahon zuciyar ta
   ",Amma ai kina ganin yadda wasu mutane dayawa a sansanin suke taɓuƙawa kansu wasu abubuwan ta hanyar kula da rayuwar su da ƴan kananun sana'o'in da suke , me zai hana muma mu yunƙura mu gwada sa'ar mu koh zamu samu damar taimskon kan mu da kan mu yakaka rayuwa a haka bazai yiwu ba ,"
Murmushin takaici yakaka tayi ganin yadda yagana ta hakikice akan batun neman sana'a
   Yagana kin manta da ruwan ciki ake jaan na rijiya ? Ita kan ta sana'ar ai sai da jari ,mu kuwa bamu da ko sisi bamu da kadara toh aina kike tunanin zamu samu jari bare a kai ga batun fara tunanin sana'ar yi
Nasan bamu da jari yakaka toh amma ai ga "kolo"(abokiyar kwanan ta ) ita ma bata da jarin amma tana bi tana neman aikin kwangilar yin ɗinkin hula ,ana biyan ta muma mai zai hana mu nemi kwangilar mu dunga yi koh zamu samu ɗan kuɗin biyan kananun buƙatu ?
Jimm yakaka tayi cikin tunani a zahiri ita bata wani iya ɗinkin hula ba sai dai tana ganin bata da wata mafitar taimakawa kan su ita da falmata idan ba ta wannan hanyar da ƙawar kirki yagana ta zo da ita ba ," dan haka ta ɗago da murmushi dai-dai lokacin da falmata ta waiwayo su tana me kafe gefen da take jin muryar yakaka da ido ,"