Sashe 37
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hasken tocila ne ya fara hasko su daga nesa kafin mutanen su ƙaraso ," tun kafin tayi magana suka yunƙuro da hanzari suna tambayar ta me ya samu ta kwancen kuma me suke anan ?
Cikin kuka take rokon su akan su taimaka su ɗauki ƙanwar ta zuwa asibiti , basu yi ƙasa a guiwa ba suka ɗauki falmatan chak tare da kai ta ɗan ƙaramin ofishin da aka tanada a matsayin ƙaramin asibitin bada taimakon gaggawa ,'
Yana zaune yana kammala shigar da wasu muhimman bayanai da suka shafi aikin sa ta computer suka faÉ—o masa duuu babu sallama bare neman izni ,"
Da ido ya bisu har suka shimfiÉ—e ta akan É—an siririn gadon da aka tanadar domin marasa lafiya ," suka yi tsaye charko-charko sun tasamma mutane ishirin a cikin ofishin a tsai-tsaye banda waÉ—an da suke daga wajen baranda da idan aka haÉ—a zasu kai rai hamsi duk Æ´an rakiya ne ,"
Cikin nazari yake kallon su ɗai-ɗaya ta cikin farin gilashin da yake manne akan fuskar sa bayan ya rufe computer gami da tokare hannuwan sa biyu akan teburin ya ɗago haɓar sa da su , cikin ranshi yana jimanta rashin hankali da gidadanci na wasu mutanen ƙauye ,"
 Â
Chan daga waje yake jiyo tashin Æ´ar siririyar muryar ta cikin kuka tana ambaton sunan "Falmata''wanda hakan ya sa da sassarfa ya nufo marar lafiyar da aka kwantar da bai kai ga sanin meye ya faru da ita ba ,"
Da taimakon hasken ƙwan lantarki fari sol da ya haske ofishin ya shaida fuskar ta duk da cewa ta ɗan kunbura a sakamakon shatin yatsu da suka kwanta tar a gefen da gefen fuskar ta ta da kuma laɓɓan ta da suka ɗan kumbura ,"amma hakan bai hana shi gane ta ba ,"
Me ya same ta ??
Ita ce tambayar da ya jefo musu a dai-dai lokacin da ya É—auko abun auna bugun numfashi ya É—aura shi a saitin kirjin ta ,' kallon-kallo aka shiga yi tsakanin mutanen da suke a cike a É—akin domin duk cikin su babu wanda ya san takamaimai meye ya faru ga falmatan
Ganin sun yi shiru ya sa shi sake cewa " ina Æ´an uwan ta ?
 Â
Mutane biyun da suka É—auko ta suka ce Æ´ar uwar ta tana waje ,"
 " Ku ƙira ta"
Da kyar ta samu hanya ta kutso cikin ɗakin idanun ta na yararin ruwan hawaye har ya jiƙe gaban hijabin ta ,
Gaban gadon da falmatan take kai ta zo ta tsaya ba tare da ta lura da wanene likitan ba ita dai babban burin ta , ta ga falmata ta motsa tsoron ta tare da taraddadin ta kar ace mata wani mummunan abu ya faru ga ƴar uwar ta ,
Tun da ta shigo yake bin ƴar siririyar fuskar ta da kallo , daga ƙarƙashin ruhin sa yana zumuɗin kallon cikin ƙwarar idanun ta ,"
Me ya same ta ? ,"
 Itace tambayar da ya jefa mata bayan yaƴi umarnin ga sauran jama'ar akan su basu wuri zai yi aikin sa , maida duban ta tayi gare shi ,"karaf suka haɗa ido ,"
Tiryan-tiryan ta shiga bashi labari , yayin da shi kuma ya duƙufa wurin bada dukkanin taimakon gaggawar da yake ganin yakamata ga falmata sai dai falmata bata motsa ba ,"
Zama yayi tare da É—aukar wayar sa kira yayi tare da bada umarnin tahowa da motar asibiti domin ya fahimci matsalar falmata ta zarce Æ´an kayan aikin da suke nan ," kallon sa ya mayar ga fuskar yakaka wacce tayi jazir sakamakon kukan da take ta faman yi ,"
  Kiyi hakuri ki daina kuka ƙanwar ki ta samu attack ne na ciwon ta a sakamakon toshe mata hanyar numfashi da aka yi wanda ya jawo huhunta ya wahalta kasantuwar daman tana ɗauke da cutar asthma amma insha Allah zata samu sauki numfashin ta zai dai-daita yanzu motar asibiti zata zo akai ta babban asibiti domin bata cikakkiyar kulawar da ta dace da masu irin ciwon ta sannan kuma jami'an kiwon lafiya mata su duba ta domin cikin bayanin ki ina zargin ta faɗa hannun ƴan ɓata gari ne,"
Tun da ya fara bayani yakaka take ƙara sautin kukan ta zuwa lokacin da ya gama mata bayani kuwa sosai take kuka har tana shiɗewa sakamakon ji da tayi falmata tana ɗauke da wata cutar da har sai an dangana ga babban asibiti ,'kuka take bilhakk .
Komawa yayi ya zauna tare da jingina da jikin kujerar sa bayan ya rintse ƙwarar idanun sa , saboda sosai kukan ta yake taɓa masa ruhi , gashi kuma bai san yaya zai yi da ita tayi shiru ba ,
Cikin abunda yake ƙasa da mintuna sha biyar motar asibitin ta iso aka shigar da falmata cikin motar tare da yakaka wacce taƙi fur ta saki jikin falmatan da zuwa yanzu numfashin ta ya fara komowa amma sama-sama ,
Suna zuwa babban asibitin gwamnatin jaha ,aka ƙarbe ta tare da shigar da ita ɗakin bada taimakon gaggawa karkashin ƙulawar dakta hamza da daman ya kasance babban likita ne shi a asibitin , zama dirshan yakaka tayi akan tiles ɗin wurin tare da dunƙulewa wuri guda ,bata ko damu da mutanen da ta zo ta tadda a wurin da su ma suka kawo marasa lafiyan su da kuma sauran mutane masu wucewa da suke mata kallon tausayawa ba ,
Bayan share zaman mintoci arba'in da Æ´an kai , wanda yakaka baza ta iya fasalta iyakacin ruÉ—ani da hargitsin rayuwar da ta shiga ba a Æ´an mintocin , dakta hamza ya fito cikin alhini da rashin kuzarin da fargaba suka haddasa mata ta É—ago idanun ta da suka kumbura tana tuhumar sa da su domin ta gaza buÉ—e baki ma tayi magana ,"
Ɗan lallausan murmushi yayi tare da yafitar ta da hannu ," a sanyaye ta miƙe tana gama hanya ta bi bayan sa zuwa cikin ainahin ɗakin ,"
Daga bakin kofar ta jaa ta tsaya lokacin da ta hango falmatan ras a zaune a bakin gadon asibitin,wata irin dariyar murna ce ta subce mata kafin ta taka da gudu ta tsalleƙe ƴar tazarar da take tsakanin su tare da rungumo falmatan wacce ita ma ta washe ƴan haƙoran tana dariya da jin sautin dariyar yakakan da take nema tun da ta farfaɗo , fuskar ta sayau da alamun rashin kuzari a tare da ita sakamakon allurorin da ta shaa har da ƙarin ruwa ,"
Falmata nah sannu , sannu sannu dan Allah me suka miki ?? Wacce irin cuta ce take damun ki falmata ciwon ki ya tsorata ni , irin tsoron da zan iya mutuwa idan ya zarta haka dan Allah falmata kar ki sake irin wannan rashin lafiyar ," gaya min ina ne yake yi miki ciwo yanzu , meye suka miki ??
Dakta hamza wanda yake tsaye ya harɗe hannunwan sa a kirji yana kallon su , karon farko da yaga wata irin tsaftatatciyar zallar ƙauna a tsakanin ƴan uwan biyu ,"shi ya amsa mata dukkan tambayoyin ta .
Cutar asthma ce take damun ta , asthma cuta ce da take kama huhun mutum ya zamana huhun mutum yana kumburi tsokar huhun tana matsewa tare da rurrufe hanyoyin da iska take shiga wanda hakan yake bada matsala wurin shiga da fitar iska / numfashin ɗan adam , alamomin cutar sun haɗa da tsananin tari musamman cikin dare zuwa wayewar gari , gwarnaki , da kuma ɗaukewar numfashi ko kuma yin ƙarancin sa , ana iya gadon cutar asthma ta iyaye , ana kuma iya samun cutar ta hanyar ƙura idan tayi yawa , ko ta hanyar shaƙar iskar gas , ko kuma tsananin sanyi , cutar asthma bata da wani maganin warkar da ita baki ɗaya sai dai akwai magungunan hana samun farmaƙi daga cutar ," sannan ya zama dole me cutar ya kiyaye kan sa daga shaƙar ƙura ,shaƙar iskar gas ,zama cikin wurin da yake da tsananin sanyi ko kuwa shan abu mai matsanancin sanyi domin bawa kansa kariya daga samun farmaƙin ciwon ,"
Numfasawa yayi yana me gauraye idanun sa cikin na yakaka wacce tayi kasaƙe tana sauraran sa idanun ta tar akan fuskar sa , lumshe idanun sa ya sake yi lokacin da ya ji wani yanayin shauƙi yana fusgar sa a sakamakon kallon cikin idanun ta da hasken ƙaton farin ƙwan wutar da yake cikin ɗakin ya haska su suke wani irin sheƙi tamkar ba yanzu suka gama ambaliyar hawaye ruwan ba ,"
Sannan ƴan bata gari sun yi yunƙurin lalata ƴar uwar ki ta hanyar yi mata fyaɗe sai dai a binciken da muka gudanar basu riga sun cimma nasara ba ,Allah ya kiyaye ta sai ku kula da gaba , ga sister zahra zata sake yi muku bayani dalla-dalla , zaku kwana anan zuwa gobe da safe muga yanayin jikin nata sai mu sallame ku ,