← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 269

Sashe 172

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amnee ina son dan Allah yau ki bani labarin abunda ya faru da rayuwar ku ke da Baba da Khaalty Rahima ? Dan Allah kar ki ƙi , ki ban labarin a matsayin tukuicin dawo miki da Khaalty Rahima da nayi .

Shiru tayi na wani ɗan lokaci , kafin ta sauƙe ajiyar zuciya ,

***

"Labarin ba wani mai daÉ—i bane da kake naciyar sanin sa ,

"Kamar yadda ka sani ne mu 'Yan asalin ƙasar Chad ne daga Babban birnin N'Djamena , inda aka haife mu , iyaye da dangin mu baki ɗaya. 

"Mahaifin mu sajjan ne ( mai gadin gidan yari )  a babban alsijn na ƙasar mu , albashin sa bai cika yawa ba dan haka mai ƙaramin ƙarfi ne sosai , dangin sa duk talakawa ne ,  haka ma mahaifiyar mu ta fito daga gidan talakawa sosai , sana'ar iyayenta sarrafa gishiri daga bakin teku su kawo cikin gari su sayar ,

ni ce Babbar  'yar su sai ƙanne na maza huɗu "Salihu , Mohammed , Usman da Jamil  sai ƙaramar mu Rahimatullah .

"Rahimatullah tana shekaru biyar ni ina da goma sha shida Mahaifiyar mu ta rasu , inda ba'a ɗau lokaci ba bayan mutuwar ta Maifinmu ya sake yin aure , ya auri wata mata mai 'ya'ya huɗu daga ƙabilar N'gambaye mabiyar Adinnin Christian ƴar ainahin ɗarikar Roman Catholic .

"zuwan "Aichawa rayuwar mu shi yayi sanadiyyar faɗawar mu ƙunci domin Aicha irin mugayen matan nan ce marar imani , babu irin aikin wahalarwa da bata sanya mu , Su salihu sun zame mata masu nemo mata kuɗi , inda ni kuma na zama baiwar ta mai yin duk wasu aikin cikin gida,

hatta Rahimtullah da take ƙanƙanuwa bata tsallakewa izaya daga hannun Aicha ba .

"shi da kansa Mahaifin mu bai tsira ba daga bala'in ta dan a wasu lokutan har duka take yi masa , idan ta nemi kuɗi bai bata ba, hakan ya sa yake masifar tsoron ta ba shi da kataɓus , ya auro jaraba .

"mugun neman kuɗi irin na Aicha ya sa nima ta sama min aikin goge-goge a babban ofishin jakadancin ƙasar mu tun a wancen lokacin da ba'a cika barin 'ya'ya mata fita neman kuɗi ba ,

"karatu ma alokacin iyakata primary ban ci gaba ba . 

"da murna na fara zuwa aikin saboda ganin zan huta daga masifar Aicha da wahalar aikin gida , sai dai kuma tunanin Rahimatullah da zan dunga bari a gida ya rage min karsashi ,

" ganin cewa aikin nawa shara ne da goge-goge sai na nemi iznin na dunga zuwa da Rahimatullah tana zama a gefe ni nayi aikina , saboda nasan idsn na bar ta a gida azaba za'a dunga gana mata , cikin sa'a aka amince min .

"Tafiya ce miƙaƙƙiya a ƙafa daga unguwar mu zuwa wajen aikina , amma haka nake goyon Rahimatullah daga alfijir ya keto mu ɗau hanya , kafin lokacin da muke isa gari ya waye sosai ,

"Haka zan yi aikina Rahimatullah tana ƙiriniyar ta ,

"Rahimatullah irin yaran nan ce masu son wasa , hakan ya sa sai ina aiki ina kaffa-kaffa da ita kar ta yi musu ɓarna dan wani lokacin ma sai na neme ta na rasa ta shige ƙarƙashin tebura ko tayi wani wajen ,

"Amne ta tsagaita tana duban fuskar Khaalty Rahima wacce take murmushi ,

"Ashe Bulama ba a ƙasa ya tsinta ba gado yayi ,

  Doctor Hamza ya kitsima hakan a ransa ,

Amnee ta cigaba da cewa ,

"Na ɗau tsawon watanni shida ina aikin goge-goge a ofisoshin guda biyar kafin a rage min yawan su zuwa kula da ofishi biyu rak , na wata mata Basudaniya ( Sudanese )"Mademe Laura , da kuma na wani jakadan ƙasar Nigeria "Al-Mustafa Dilmari .

"tsakanina da su Gaisuwa msi cike da girmamawa ne idan sun iso ofis sun tarad dani a bakin aikina ,

"wata alaƙa bata taɓa gifta tsakanin mu ba sai Ranar da Rahima tayi wata mummunar ɓarna a ofishin Ambassador Mustapha , inda ta yayyaga wasu takardu masu muhimmanci da ya mance ya tafi ya bar su a ofishin sa ba tare da ya adana su ba ,

"Ranar na shiga tashin hankali domin kuwa faɗa sosai ya dunga yi min , bai tsagaita ba sai da Rahimatulla wacce take goye a bayana , saboda zamu tafi ƙiran sa ya cimmin , ta leƙo da kanta cikin harshen larabci ta ce da shi yayi haƙuri ya daina yi mana faɗa irin yadda Aichatuwa take yi mana kullum ai ita ta yaga takardun tana so ta yiwa ƴar tsanar ta kaya ,

"Ban san dalili ba sai naga ya sassauta fishin sa , a ƙarshe yace mu tafi kawai ,

"tun daga ranar sai naji tsoron sake zuwa da Rahima domin kar tayi wata ɓarna sa zata sa a kore ni daga aikin wanda albashin sa a lokacin da shi nake yi mana hidimar yau da kullum  ni da ita duk kuwa da cewa kaso uku Aichatuwa take raba albashin ta ɗau kashi biyu da rabi ta bani guntun ,

"daɓ dole nake barin ta a gida tana kuka , wani lokacin nima har ta saka ni ƙwalla , nake tafiya na bar ta ,

"ba'a yi sati guda ba wata safiya har na kammala aiki zan tafi , Ambassador Al-mustapha ya ƙira ni , zuciyata cike da tsoro na je na ɗauks batun laifin Rahima ne bai wuce ba ko kuma ni ce na sake yin wani laifin .

" ga mamakina sai naji yana tambayata ina ƙanwa ta take meyasa na daina zuwa da ita ?

" na ce masa tana nan , inajin tsoron kar ta sake ɓarna shiyasa na daina zuwa da ita ,

" sai ya umarceni da mu cigaba da zuwa tare amma na dunga lura da ita kar ta dunga yin ɓarna ,

"shikenan Tun daga ranar na cigaba da zuwa da Rahima ,

"a hankali sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin Ambassador Al-mustapha da Rahimatullah saboda 'yan kayan maƙulashe na yara da yake mata hasafin su ,

"kafin wasu watanni shaƙuwar su da Rahima ta shafeni wanda a ƙarshe cikin shekara guda tsakanin mu ya rikiɗe ya zama soyayya ce mai ƙarfi ,

"duk kuwa da tazarar matsayi da yake tsakanin mu hakanan Allah ya kulla auratayya a tsakanin mu , bayan rigin-gimu da suka taso daga dukkan ɓangarorin biyu , daga Aichatuwa , da bangaren iyaye da 'yan uwa Al-mustapha na jini , wanda suks tirje akan ba zai auri 'yar wata ƙasa ba wacce ba ƙabilar su ta kanurai ba , alhalin ga 'yar uwarsu wacce take dakon jiran sa suyi aure ,

"hakanan ɓangaren Aichatuwa wacce ta bi duk wata hanyar da zata iya bi domin ganin auren mu bai yiwu ba da Mahaifin ka , amma dayake shi aure Kaddara ce daga kaddarorin da Allah yake yi ga bayin sa .

"A ƙarshe aka ɗaura Auren mu ni da Mahaifinka tare da Amincewar kakan ku wanda ya taka har ƙasar mu ya nemawa ɗan sa aurena cikin mutuntawa , bai duba ƙasƙancin mu da shi yake babban Attajiri a ƙasar su kuma mai ilmin addini da na boko tun a wancen zamanin .

" Bayan auren mu mun zauna shekara guda a N'Djamena kafin aikin mahaifin ku ya ƙare da ƙasar mu , muka kuma fara shirin komawa ƙasar su ,

"a kuma tsukin wannan lokacin Allah ya yiwa Mahaifin mu Rasuwa sakamakon sukar sa da wuƙa da wasu ga cikin 'yan firsina suka yi a ƙoƙarin su na gudu daga gidan yari .

"Mutuwar Baban mu ta gigita mu ganin cewa duk wani gatan da muke da shi ya ƙare ,

"a ƙarshe dole muka haƙura , riƙon Rahima kachokam ya dawo hannun mu da duk wasu ɗawainiyar ta Al-Mustapha ke yi ,

"Sauran ƙannena maza suka raɓu da gidajen 'yan uwa  , ,

"Ba mu jima ba bayan nan muka koma Nigeria tare da Rahimatullah da   kuma kai a lokacin kana ɗan jariri .

"na fuskanci tsangwama da ƙiyayya iri-iri daga kakar ku , da dangin mahaifin ku da baki ɗayan su basa ƙaunar auren mu , idan aka ɗauke Salman wanda ƙani ne na uku ga mahaifin ku da shi babu ruwan sa da duk wasu lamura da suka shafe ni .

"Haka shekaru suka yi ta tafiya tare da nasarar rayuwa , matsala mafi girma da ta zama sanadin rabuwar auren mu da mahaifin ku ya samo asaline daga lokacin da Soyayya ta shiga tsakanin Salman da Rahimatullah ,

"lokacin Rahima ta gama makarantar gaba da primary , kai kuma ka shiga makarantar kwana ta gaba da primary ,

"rikicin an É—auki lokaci ana yin sa tun bayan bayyanuwar soyayyar su da suka yi shekaru biyu suna boyen ta a tsakanin su ,

"Salman ya doshi mahaifiyar su da sauran 'yan uwan sa da batun auren Rahimatullah , ƙaramin yaki aka yi a tsakanin su saboda lokacin kakan ku ya jima da rasuwa .

"Lamari yayi tsamari da yasa har kakar ku ta ƙira mahaifinku ta masa kashedi kan muddin yana son Albarkar ta , ya zama dole ya raba tsakanin ƙanwar matar sa da ƙanin sa ,

"daga lokacin shima Mahaifinku ya fara nuna adawar sa da soyayyar tsakanin Salman da Rahima domin bin umarnin Mahaifiyar su , da hakan ya kawo saɓanin a tsakanina da shi domin ni ɗari cikin ɗari nake tare da su akan lamarin soyayyar su .

"ana cikin wannan hatsaniyar uwar matar da aka so aurawa Mahaifin ku wacce take ƙanwar kakan ku ce ta zo da wani lamari mai yanayi da tsafi ko kuwa chanfi  , kan cewa muddin ba'a yi gaggawar raba tsakanin Salman da Rahima ba to babu makawa guda a tsakanin su zai mutu , domin Malamin ta yace babu aure a tsakanin su , '

"Maganar bata ɗaga min hankali ba sai da naga kamar Mahaifinku ya yarda da batun inda har ya fara maganar ko dai Rahimatullah zata koma N'Djamena na ɗan wani lokaci , idan kome ya lafa ta dawo ,ranar nayi kukan Maraicin mu da rashin gatan mu  ,
Chapter 172 · 0% Book details