← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 269

Sashe 16

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yakaka yakaka ," da sauri yakaka wacce ta maida hankalin ta gaba ɗaya ga mutanen da suke kai kawo a wurin tana nazarin su,"cikin ranta tana hango musu irin rayuwar rashin sakewar da zasu yi ita da ƙanwar ta a cikin waɗannan ɗaruruwan mutanen da basu taɓa sanin koh ɗaya daga cikin su ba ,sanin da tayi su ɗin ba mutane ne waɗan da suka saba da shiga cikin jama'a ba , hasalima su ko a garin su a ƙebe da su da mahaifiyar suke , basa shiga cikin taron jama'a saboda wasu dalilai ,"

Da sauri ta juya gami da miƙewa tsaye hankali a tashe take duban yagana wacce ta ƙaraso gaban ta yanzu tana ta haki a sakamakon ɗan gudun da tayi ," yagana lafiya ta furta hakan hannun ta ɗaya dafe da kirjin ta ?
Lafiya lau yakaka Albishirin ku , ?
Da sauri falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye ,"
Da sauri kuma cikin zumiÉ—i tace goro ? ta zarce da cewa...kin ga maman mu ne ?

Ɗan kallon ta da gefen ido yagana tayi cikin ran ta kuwa tausayin su ne ya kawo mata ,! ," Falmata kin manta ni ban san mama ba ?,"ta ɗora da sake faɗaɗa fara'ar ta tace ,"wai yau gwamna ne zai zo wannan sansanin , Yakaka-falmata mu yau mun shigo maiduguri a sa'a ,wallahi yau zamu ga gwamna ta ƙarasa zancen tare da yin ɗan tsallen murna,"

Ɗan guntun tsaki falmata tayi ,' kana cikin sanyi jiki ta silale tare da lalubar inda ta tashi ta sake zama tare da rafka tagumi hannu bi-biyu , sam a gareta wannan ba Albishir ba ne ," toh ita ina ruwan ta da wani ganin gwamna ? Tukun da wanne idanun zata ga gwamnan ? Sannan koh da tana gani ma a halin da take ciki a yanzu bata jin ganin gwamna zai iya ƙarar da ita wani abu da ya shafi farin ciki da har za'a yi mata albishir a kan sa ,' a halin yanzu jin ɗumin mahaifiyar ta tare da sauraron gwalatun maganar ta ,irin ta kurame shine kaɗai abun da zai sanya ta farin ciki ," hawaye ne ya silalo daga gurbin idanun ta sakamakon amsa kuwwar muryar mahaifiyar ta da taji yana shawagi da yi mata gizo a kunnuwan ta ,"

Da ɗan guntun murmushi ɗauke akan fuskar yakaka ta koma ta zauna ita ma ," kai yagana saboda haka ne kike ta ihun ƙira na har kika tsinka min zuciya ?

Ɗan yaƙe yagana tayi ganin yadda ya da ƙanwar suka gwale ta ," cikin ranta tana cewe ku ai daman alamu sun nuna ba'a yi muku gwaninta

Yakaka ni kam ki kaini banÉ—aki fitsari nake ji kuma fa har yanzu ba mu yi sallar azhar ba har ga shi kamar kunnuwa na suna jiyo kiran sallar la'asar ,"
Da sauri yakaka ta sake miƙewa lokaci guda tana kai duban ta ga yagana wacce tsabar murna ta gaza tsayuwa guri guda ," yagana inane banɗakin ne ?
Ɗan diri-diri yagana tayi domin ita har ga Allah ta ma manta ina aka gwada mata banɗakin yake ,"saboda tsabar ɗoki ," amma ganin wani mutum ya fito daga wani ɗan ɗaki da yake daura da ɗakin da suka fara cin karo da shi a wurin (office ɗin mutumin nan ) hannun sa riƙe da buta ga alama kama ruwa yayi , hakan yasa yagana tayi nuni da wurin ta ɗora da faɗin ,' Kamar cewa aka yi nan baya haka yake koh ,?

Bin inda ta nuna da É—an yatsanta manuniya yakaka tayi ,"cikin shakku take kallon inda yagana ke gwada mata ," domin dai É—akin da yake gefe da É—akin (office) É—in mutumin nan da yayi musu korar kare take nunawa ,"
Yagana nan baya kika ce kuma gashi kina nuna gaba ? Anya kuwa can ne banÉ—akin ?

Yakaka kina gani dai mutum ya fito daga banɗakin hannun sa riƙe da buta kin dai gan shi ai koh ?,"

Toh muje falmata ," yakaka ta furta hakan dai-dai lokacin da take kamo hannun falmatan suka jera har bakin barandar ," mu karasa bakin kofar sai na jira ki ,"

ÆŠan turus yakaka tayi lokacin da falmata ta ce toh ina ruwan da zan yi amfani da shi yakaka ?

Bari na tambayo matan can inda ake ɗibar ruwa , ta furta hakan lokacin da take mayar da kallon ta kan wasu gungun matan da suke tsaitsaye hannuwan su riƙe da wasu manyan farantai irin na rabawa jama'ar gidan biki abinci ,

Toh ni zan shiga dan gaskiya a matse nake yakaka idan kin kawo ruwan ki ajiyemin a bakin kofar ," falmata ke furta hakan a lokacin da take laluban ƙyauren kofar ," ɗan bin ta da kallo yakaka tayi cikin ran ta fal tausayi da ƙaunar ƙanwar ta ke ƙaraƙaina ,"

falmata koh na kama ki mu shiga tare saboda koh banÉ—akin bashi da kyau sosai ," ?

Yakaka zan kula da kaina ki kawo min ruwan da sauri dan Allah kar wasu su shigo kaina ," falmata ta furta hakan a lokacin da ta tura kofar ,"

Da sassarfa yakaka ta juya ta dumfari matan nan cikin ranta tana jinjina irin karfin zuciyar falmata da kuma yadda a koyaushe take boye tsaraicin ta sosai ,bata taɓa ganin mutum a shekarun falmata da yake da kunya tare da suturce jikin sa irin ta ba ," tun falmata na da kananun shekarun da yakamata a dunga kula da ita irin su wanka ,tsarki da sauran su ," ita bata yadda , sai dai tayi da kan ta duk kuwa da naƙasar da take tare da ita ," tun mahaifiyar su na dukan falmatan idan taƙi yadda tayi mata wanka ," har ta haƙura ta kyale ta .

********

Da lalube take bin bangon banɗakin tana shaƙar wani daddaɗan kamshin da yake game da wurin ,tsam ta tsaya lokacin da ta ji ƙafar ta da koh takalmu babu ta sauka akan wani lallausan abu ,"kamar shimfiɗa ? Da sauri ta ɗan janye ƙafar ta , cikin ranta tana tunanin toh shi banɗakin birni haka yake da laushi kamar anyi shimfiɗa ?

Koh da yake ance gidan gwamnati muke ,zata iya yiwuwa ma ayi shimfiɗar a banɗakin dan jin dadi ," Fitsarin da ya sake mintsilin marar ta shi ya sa ba shiri ta ɗan ƙara gaba kaɗan ta sunkuya da nufin tsugunnawa lokacin da taji kan ta yayi karo da wani abun da bata tantance ko menene ba ," ɗan shafa goshin ta tayi lokacin da ta fara sauke larurar ta ,'cikin ranta tana mitar su mutanen birni sai a bar su yanzu me ya kawo tarkace cikin banɗaki ?

Ji tayi ana ƙokarin turo kofar da saurin ta tayi gyaran murya cikin siririyar muryar ta tace " a dakata akwai mutum ,"

Turus yayi sakamakon jin muryar mace da yayi a cikin office É—in sa ," waiwayawa yayi ya dubi É—ayan saurayin da suke tare da basu wuce sa'o'in juna ba yace ," suleiman ko kaji kamar muryar mutum a cikin office É—in nan yana dakatar da ni ? ," eh hamza naji mana muryar mace ba ,? "wanda aka kira da suleiman ke furta hakan fuskar sa É—auke da É—an siririn murmushin da ya yi kyau akan madaidaiciyar fuskar sa ,"

Ba tare da jinkiri ba hamza ya murÉ—a hannun kÆ´auren gami da danna kan sa ciki"

Jikinta babu inda baya rawa a saboda duk ta riga ta gama jin zantukan su , cikin office nake ba banɗaki ba toh inane office ɗin ? kar dai wani wuri ne na musamman wanda bai da alaƙa da banɗaki ni falmata na shiga uku yau ," shine kalaman da suke ta maimaituwa a cikin ranta lokaci guda kuma tana gyara zaman zanin ta da rigar ta har ma da adikon da ke kan ta bayan ta miƙe tsaye ,"

Ware idanun sa sosai yayi yana kallon ta tamkar dai yaga sabuwar halitta ,tun daga sama har ƙasa , wata irin zabura yayi ya jaa baya sakamakon ganin ruwan da yake kwance male-male akan tattausan shuɗin kafet ( Carpet ) ɗin ofishin daga gefen kafafun ta ,

tattare fatar goshin sa yayi tare da ƙanƙance idanun sa a lokacin da tunanin sa tare da abun da yake gani suka tabbatar masa da abun da ta aikata masa a office ɗin sa da dazu-ɗazun nan masu shara suka share kowanne lungu da saƙo tare da goge shi haɗi da feshe shi da turare a saboda manyan ɓakin da suke tafe,

Da gudu-gudu ta ƙaraso wurin hannun ta rike da zundumemiyar gorar ruwa wacce koh murfi babu , a cike taf da ruwa har yana ɗiga ," ɗan satar kallon saurayin da ta tadda a bakin kofar banɗakin tayi ," da sauri ta ɗauke kan ta sakamakon haɗa idanu da suka yi ta ga yana bin ta da wani kallon da yake nuna alamun kƴamata ,

Cikin sanyin murya da gurbatatciyar hausar ta tace kayi hakuri yanzu zata fito ɗan ƙwanƙwasa kofar tayi ," falmata ga ruwan kiyi sauri ki fito akwai mai jira ," yakaka ke furta hakan ,"

Jin ihun fashewar kukan falmata ya sanya ba shiri yakaka ta danna kanta cikin wajen da suke zaton banÉ—aki ne ,"

Suman tsaye tayi lokacin da tayi arba da kyakyawan ofishin da yake tashin kamshi ,' hasaso abun da ƙanwar ta ta aikata a ofishin ya sanya ta jin numfashin ta na mata wuyar shaƙa .

Muryar sa ta dawo da ita cikin hankalin ta wanda a farko bata lura da wanzuwar sa ba ma a wurin

Banza ƴar ƙauye dakikiya , dan ke dabba ce zaki shigo office kiyi min fitsari akan Carpet , ? Ke mahaukaciyar ina ce ? Koh a can ƙauyen ku kin taɓa cin karo da banɗaki da irin wannan tsarin ?
Chapter 16 · 0% Book details