← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 269

Sashe 108

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  subahannalahi innalillahi wa inna ilaihi raji'oon sune kalmomin da prof ke jerowa
   Rahima ƙira direba maza a kai ta asibiti ,
   Da sauri Youssouf ya waigo tare da sunkuyowa kan falmata ya tabbatar dai bata numfashi nan take ya sanya hannu a aljihun sa yana ƙiran direban sa , lokaci guda fuskar sa na bayyana ruɗanin da yake ciki yake cewa

   Daman bata da lafiya ne Baba ??
 
Prof bai amsa masa ba ,

Direban youssouf shi ya fara shigowa dan haka rahima ta fara ƙoƙarin ɗaga falmata sai dai ta kasa , saboda tayi mata nawi ,

Baby mama Youssouf ya miƙawa Rahima ,
   Lokaci guda ya sanya hannunwan sa biyu ya ɗaga falmata wacce take sume  ya fice da ita wajen motar su , direban sa ya buɗe gidan baya ya shimfiɗe ta ,

Ya karɓi baby mama daga hannun rahima tare da yi mata umarnin ta shiga su tafi ta gwada musu asibiti mafi kusa da zasu kai falmata ,

tafiyar mintoci biyar suka isa wani asibiti mai zaman kan sa , inda nan take likitoci suka rufu akan falmata suna ƙoƙarin dawo da numfashin ta dai-dai ,

Hankalin Youssouf baki ɗaya a tashe yake ya kasa zaune ya kasa tsaye , sai zirga zirga yake tsakanin kofar ɗakin da Falmata take yana rungume da baby mama , tsoron sa ɗaya kar yarinyar nan ta mutu a sanadin raba ta da yace zai yi da ƴar sa , idan haka ta faru bai san inda damuwar sa zata kai ba , "  ko kusa bai san haka take ƙaunar ƴar sa ba ,

ya kasa kintata yawan ƙaunar da ke tsakanin ta da yayar ta wanda yake da tabbacin son da take mata ne ya shafi ƴar ta , idan kuwa haka ne lalle falmata abar a tausayawa ce , ƙwarai ya kamata yayi adalci ya kuma duba anya idan ya raba ƴar sa da ita ya kyauta kuwa ?? Anya bai so kan sa dayawa ba kuwa ?

mintoci arba'in da shigar da ita É—akin suka fara jiyo gunjin kukan ta , tana surutai ,
    Da sauri Biyamuradi youssouf ya ƙarasa gaban ɗakin dai-dai da fitowar babban likitan ,

Mun samu numfashin ta ya dai-daita kamar yadda muke zaton kun sani tana da asthma , toh ta samu attack ne , yakamata a dunga kiyayewa da duk wani abu da zai iya kawo mata wahalar numfashi , yanzu ku shiga akwai wanda take son gani a tsakanin ku , nan da É—an wani lokaci kaÉ—an ma zaku iya tafiya gida ko awa É—aya haka nan gaba !

Biyamuradi youssouf ne a gaba sai Rahima biye da shi , suna shiga rahima ta ƙarasa ta rike hannun ta , tace ga ita
   Ki daina kuka haka fatima , ai ga baby nan ba'a tafi da ita ko ina ba ,

Tana ina ??
   Tace tana lalube da hannuwan ta biyu idanun ta har sun rine tsabar kuka ,

A hankali biyamuradi youssouf ya tako zuwa gaban gadon ya É—ora mata baby mama a cinyar ta tare da cewa

   Ungo ta ! karɓe ta fatima daina kuka , ke ai uwa ce a gare ta ,

  Chak ta ɗauke ta ta rungume ta tana ajiyar zuci tare da shafa bayan baby mama tana ɗan bubbugawa ,

Juyawa yayi ya fita yana jin yadda tsananin tausayin ta yake ratsa kowanne saƙo da lungu na zuciyar sa yana samun mazauni , ji yake kome yana neman kunce masa , tausayin ta kuma yana neman yin tasiri akan sa , mafita yake nema ,

Zuwa yayi ya biya kuÉ—in magungunan da aka mata ,
    Daga nan ya sake ganin likitan da ya bata taimako , ya sake yi masa bayani tare da sake jaddada masa a kula da lafiyar ta,  nan ya rubuta musu sallama zasu iya tafiya daga zarar an sake duba yanayin numfashin ta ,

A bakin ƙofa ɗakin ya tarar da rahima tana zaune ,
   Da sauri ya tura ƙofar ya shiga idanun sa suka sauƙa akan ta , har yanzu tana zaune rungume da jaririyar da take ta bacci abin ta ,

waye anan ?  Tace tana sake rungume ƴar ,

   Fatima ,
ya ƙira sunan ta muryar sa babu amo ,
   Ƙwalla ce ta sake kawo mata a ido , ita dai wannan mutumin ya fi ƙarfin ta ,

  Dan Allah , Dan Allah ka bar min ita , kar ka raba ni da ita ,

  Shiru yayi yana kallon ta , idan har yace zuciyar sa bata yi laushi ba akan tausayin yarinyar ya faɗi ƙarya ,

Fatima za ki bi ni mu tafi ??  Za ki bi ni na tafi tare da ku ke da ɗiyar ki  ?? ?

Inda take jin sautin muryar sa ta saita idanun ta tamkar tana ganin sa ,

Muryar ta ƙasa-ƙasa , ta juya tambayar kan sa ,

Za ka yadda na bi ka , ? Idan na bi ka za ka bar min baby a tare da ni ??

Idan za ki bi ni zan bar ki miki ita har abada a hannoun ki , babu mai raba ku ,!

NA YARDA ZAN BI KA ,!

****

ƙarfe huɗu suka dawo gida , numfashin falmata ya samu daidaito , tana maƙale da ƴar ta tsam , lokaci zuwa lokaci tana ɗan jijjiga ta saboda kukan yunwa da ta fara ,

Suna shigowa prof wanda tunda suka tafi yake ƙiran rahima ya ji halin da suke ciki , ya ji hankalin sa ya kwanta da ya ga falmata ta warware ,

kai tsaye falmata da rahima suka wuce cikin gida domin su haÉ—awa baby madarar ta ,

Shi kuma Biyamuradi ya shiga wajen prof ,

   Cikin nutsuwa youssouf ya yiwa prof bayanin yadda suka yi da falmata akan amincewa da tayi zata bi shi , ya ɗora da cewa

    Na ɗauki Alƙawarin zan kula da ita tamkar yadda zan kula da ɗiya ta , da yardar Allah ,
  
Gyaran murya prof yayi bayan ya gama jin sa ,
    Ɗana ka so kan ka dayawa , kuma a wannan gaɓar inada ikon yin hani , saboda yarinya amanar Allah ce a hannu na , shi ɗa na kowa ne , abunda baza ka so ya samu ɗan ka ba idan kana da ikon hanawa kar ka bari ya samu ɗan wani ,

ni a matsayina na wanda wannan yarinya take a ƙarƙashin iko na a yanzu , bazan amince maka ka ɗauke ta ka tafi da ita ko ina ba , tana matsayin ƴa mace , kai ko namiji ce bazan yadda ba bare ƴa mace , to a wanne dalili ? Ka tafi da ƴar ka wannan ƴar ka ce ,kana da iko da ita  amma fatima kam baza ta bi ka ko'ina ba !

Shiru youssouf yayi kan sa a ƙasa , shi tausayin falmata yake ji matuƙa , sannan yana da kyakkyawar niyyar sauke ƙudirin sa na tun farko da ya so cikawa akan yakaka , a yanzu da bata nan zai so ya tallafi falmata , ko da babu baby mama zata samu taimakon sa sanadin yakaka ,!

Baba ayi haƙuri a duba da kyau dai ita ɗiyar nan idan an raba su da jaririyar nan matsala ce babba zata auku , lafiyar ta abun dubawa ce ,

  Babu alamun sassauci a muryar prof ya ce idan ka ga na bar ka ,  ka tafi da fatima , to ka ɗauke ta ne ƙarƙashin amincewar shara'a

  amincewar shara'a ?

Youssouf ya maimaita

Ƙwarai ina nufin igiyar AURE ta ƙullu a tsakanim ƙu , ta zama halalin ka , ta maye gurbin ƴar uwar ta a gurin ka , to a lokacin kana da ikon da zaka tafi da ita tare da ƴar ka duk inda kake so cikin duniya ,bazan hana ba,  idan kuwa ba haka ba ka janye batun zuwa da ita ko'ina idan Allah ya kai mu gobe ka zo ka ɗau ƴar ka kamar yadda ka ce , na gama magana !

Ɗago kan sa yayi yana kallon prof tamkar  sassaƙen mutum mutumi ,

AURE ?
    AURE TSAKANIN sa da wa ? Wannan ƴar ficiciyar yarinyar ? Ƙanwar yarinyar da yayiwa ciki ?  Makauniya ƴar gudun hijira ? Marar gata marar galihu marar dangi ??

  Wani irin yanayi yake ciki akan tunowa da yayi da wacece ita , ?

Bugu ƙirjin sa ya shiga yi gumi yana tsattsafo masa har yana ɗiga daga goshin sa duk kuwa da sanyin ac da ya wadaci falon , "

  Youssouf mutum ne da yake jajirtatce mai kafiya akan cikar burin sa bai cika duban yadda gaba zata kasance ba idan yaso aiwatar da wani ƙudiri nasa , a yanzu tafiya da ƴar sa shine a gaban sa , so yake ya tsira da ƴar sa ba tare da ya bar baya da ƙura ba , ba tare da ya ci karo da wani abu da zai iya yi masa shamaƙi ba ,

raba fatima da baby mama wani abu ne da idan yayi , har abada baya jin zai iya mantawa kamar yadda ya riga ya san cewa tabbas idan ya tafi ƙasar su dawowar sa nigeria wani abu ne da yake gani da wuya ya kasance to ya dawo yayi me ?? Waye nasa a nigeria ?  Ba shi da kome a nan , bai taɓa zuwa ba sai ta dalilin aikin sa ,

Kalmomin da zuciyar sa ta riga ta amince masa da hukuncin da ya yanke sune suka jero kan su suka fito ta tsakanin laɓɓan sa ,

NA AMINCE DA AUREN TA !

a take fuskar prof ta yalwatu da haske da fara'a

   Masha Allah Masha Allah haƙar sa ta cimma ruwa ,

Ka amince zaka auri fatima ƙanwar matar ka ??

   NA AMINCE ZAN AURE TA !

Assalamu Alaikum ! Masu karatu ,

Da fatan duk kuna lafiya cikin aminci ?
Chapter 108 · 0% Book details