Sashe 100
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba'a yi wata tafiya mai nisa ba Yagana tace a tsaya ga gidan
  Tana yi musu nuni da gidan Amne ,
Su suka fara fitowa shi da Tafeda suka tasa ƙeyar yagana kai tsaye suka sanya kai cikin gidan .
  Amne tana kishingiɗe akan ƴar daddumar ta tana shan hantsi ta ga tsayuwar sojoji akan ta ,"
  Miƙewa tayi zaune tana kallon su a tsorace ,
  Wannan ce ta ɓoye su
Yagana tace haka tana nuna Amne da É—an yatsan ta ,
  Da sauri ta miƙe tsaye ,
Ranku ya daÉ—e lafiya ?
 Wanne laifi nayi dan Allah ?
Yarinyar da kin ka boye zaki fiddo mana ita yanzu mu tahi da ita ,ƙanwa ta ce ,
  Wacce yarinyar ?
 YAKAKA
Yagana ta bata amsa tana matse ido
Zuciyar Amne ta buga da ƙarfi dan razana ƙwarai ta gane yakaka yarinyar da ta mutu wurin haihuwa , ƴan gudun hijirar da ɗan ta ya taimakawa yake riƙon su a gidan su , ganin jami'an tsaro suna neman ta yasa hantar cikin ta kaɗawa ,
anya baza su harbe ta ba idan ta gaya musu ai wacce suke nema ta mutu ?? Ko su tafi da ita barikin su na soji su wahalshe ta a banza , bata da mai karbo ta , É—an ta yau-yau yayi tafiya , ya bar garin , dole tayi taka tsantsan kar ta É—aure kan ta !
Mahaifin su Hamza babban mutum ne ba abu mai sauƙi bane a tozarta shi musamman ma da ta san basu yi wani mummunan laifi ba , tana da yaƙinin idan ta sada su da shi kome zai zo da sauƙi , shi zai iya musu bayani su fahimta ,
   Ni ba nice mariƙiyar su ba riƙon kwana ɗaya jal nayi musu , a halin yanzu suna gidan mariƙin su , zan iya kai ku gidan na dawo ?
 Ta ƙare jawabin ta da sigar tambaya ,?
  Ki gouda mana gidan , idan har kin san gaskiya kin ka faɗi ,"
 Gaskiya ne wallahi , muje na kai ku ,
Babu Æata lokaci Amne ta kai su har Unguwar su Doctor Hamza ta nuna musu gidan daga nesa ,
Kuna iya komawa muhallin ku Tafeeda yace da su, Youssouf zai yi magana , ya masa alama da yayi shiru ,"
  Gudu-Gudu Yagana ta tare mai napep ta shiga ,
sansanin Æ´an gudun hijira zaka kai ni ,"
tace da shi tana waiwayen bayan ta ,
  Ta ɗan madubin gaban napep ɗin ya dube ta , wanne daga cikin sansanin ƴan gudun hijirar zan kai ki ??
  Na hanyar bulunkutu tace da shi ,
Cikin ran ta tana kitsima gara ta koma sansanin ƴan gudun hijirar inda samun ta zai yi wahala , zata ɓace a cikin dubunnan ƴan gudun hijira ƴan uwan ta domin ta san ta yarda ta bari wannan sojan ya san da haɗin bakin ta aka gudu da Yakaka har wani garin da ita kan ta ma baza ta ce ga sunan garin ba , bata da hanyar saduwa da samy baby , toh fa tasan ba abunda zai hana shi harbe ta har lahira ya kashe ta !
  Tattaki suka fara suna nufar gidan da kowanne cikin su ke yiwa kallon sani ,
  Kusan a tare suka ce da juna wannan ai gidan da munka zou biki kwanakin baya ,"
   Babu shakka shine Yarima Youssouf ya amsa ,
Maigadin gidan ne ya tare su , cikin ladabi ya gaishe ya É—ora da tambayar su ina suka nufa ?
 Suka shaida masa gurin maigidan suka zo ," nan ya shaida musu zai shiga ya sanar da shi zuwan su , har youssouf zai yi magana , Tafeeda ya sake dakatar da shi , bayan wucewar sa yace da shi ,"
  Ɗan ouwa mu bi kome a sannu , kar muyi garaje .
 Bai ce da shi kome ba , suna tsaye maigadin ya fito yayi musu iznin shiga gidan ƙarƙashin jagorancin sa ,"
Har cikin falon yayi musu jagora , prof yana zaune suka shigo bayan sun sunce ƙwafta-ƙwafatan takalman su daga waje ,
  Da kallon rashin sani yake bin su bayan sun gama taƙaitatciyar gaisuwar da ta shiga tsakanin su ,"
  Samari daga ina kuke ? Ban shaida fuskokin ku ba !
  Ɗan jim suka yi suna tattaro nutsuwar su , kafin Tafeeda da shine ya tsara kome yace
  Baba munzo neman watta ɗiya da anka ce kana riƙo sunan ta Yakaka , " wannan mijin ta ne ,
  Ya ƙarasa zancen yana nuna youssouf
  Ɗan jim prof yayi, wacece yakaka ? Ko dai yarinya ƴar gudun hijira ? ,'
Yaya kamannin ta yake ? Kuma a wanne yanayi take ,"
  Doguwa ce fara , tana da tsago a fuskar ta , sannan , sannan kuma tana É—auke da juna biyu , Â
  Youssouf ya ambata
Kaine mijin ta ? Prof yace da shi fuskar sa na nuna jimami ,"
 Ni ne baba
 Ya amsa
 , cikin zuciyar sa yana fatan tambayoyin su tsaya iyaka nan , tare da zaƙuwa da son a ƙira masa ita ya gan ta , Allah sarki ashe ma ƴar hijira ce ,
  Tunanin sa ya tsaya chak lokacin da yaji prof yace
  Yaro ina baka haƙuri tare da tunasar da kai akan cewa duk wani mai rai mamaci ne , yarinya yakaka ƴar gudun hijira ta rasu a wajen haihuwa bayan riƙon su da muka yi a gidan nan tsawon watanni bakwai , ta rasu ta bar ɗiyar da ta haifa tare da ƙanwar ta da muke riƙon su tare ...
Ji yayi wani irin yanayi mai kaifi yana ratsa zuciyar sa wanda ya zarce kaifin tsoro ko firgita , tsintar kan sa yayi a hali na shuÉ—ewar tunani na wucin gadi , jikin sa a take ya É—auki rawa , da wannan yanayin ya watsa idanun sa kan Baba prof ,"
  Yarinya yakaka ta mutu ? Ta mutu a wajen haihuwar abunda ke cikin ta ? Ta mutu bamu gana na nemi yafiyar ta ba ? Ta mutu ban gyara kuskuren da nasa muka aikata tare ba ? Ta mutu Alhalin ban nuna mata godiya ta akan irin taimakon da ita take tunanin ta mun ba ? Meyasa ta Mutu ta bar min nawi mai girma bissa kaina ni kaɗai ?
  Tafeeda ne ya riƙo shi ganin yadda yake surutai kusan bai cikin hayyacin sa , tabbas shi da kan sa ya ji mutuwar yarinyar , kome kuma ya kunce masa , zuciyar sa kuma ta raurawa ,
Kayi hakuri yaro mutuwa na kan kowa bari na ƙira a kawo maka ɗiyar ka , ƙanwar ta ma ta zo ku gaisa ,"
 Waya yayi cikin gidan akan a zo da Falmata da baby mama ,"
Ya maida hankalin sa kan su Youssouf da tafeeda yana nazartar su , akwai tambayoyi dayawa da yake son yi musu ba wai dan bai yarda da su ba , sai dan a farkon kawo yarinyar gidan Hamza ya sanar da shi mijin yarinyar ya mutu boko haram sun kashe shi , sai kuma ga shi yanzu ya ga jami'in tsaro a matsayin mijin ta ko daman ɓata yayi ba mutuwa ba tsawon wannan lokacin ?
Shigowar Falmata riƙe da mama tare da rahima , shi yasa biyamuradi Youssouf ɗago kan sa ,"
  Idanun sa so suke su ga ɗiyar , so yake ya samu rangwame ta hanyar fahimtar bashi da alaƙa da ɗiyar da aka samar ta hanyar banza wacce zuwan ta yayi sanadin mutuwar mahaifiyar ta me tarin rashin galihu , bai so lamuran sa su sake munana ,
  Sai dai wani yanayi da ya tsinka jinin jikin sa lokacin da hasken fuskar ƴar jaririyar da ya ɓanɓare daga hannun falmata ba tare da ya jira sun ƙarasa shigowa falon ba yayi tattaki da sassarfa ya taro su ,
  Yanayin mai ƙarfi ne da bai taɓa jin kwatankwacin sa ba da ɗai duniya ,
Jin sa yayi a wani yanayi wanda ya so ya saɓawa wanda yake cikin sa kafin ɗora idon sa akan ƴar da yaji ya gaza gane wacce matsaya yayi mata a halin da yake ciki ,
  Kallon ta yake tamkar yana son ganin abun da ke lulluɓe cikin fatar jikin ta , kallon da yake mata ya sa duk wata suffa tata jeruwa cikin tunanin sa tana juyawa tare da girma mataki-mataki har zuwa lokacin da kammanin ta da mahaifiyar sa suka gama fitowa tsaf , tamkar kobo da kobo ,
   Bai san lokacin da idanun sa suka samar da ruwan hawaye ba sai kawai ganin ɗigar su yayi akan fuskar ta , wanda ya nutsar da idanun sa kai babu shakka yana iya kallon ƙofofin gashin jikin ta ,
  Sauƙar ruwa a fuskar ta ya sanya ta buɗe idanun ta a hankali ta wara su akan sa , fes ! da shi ma ya sake ware nasa idanun tare da ɗage duk girar sa biyu abun da ya kan yi idan yana cikin yanayi na shauƙi ,