← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 269

Sashe 61

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko mintoci biyu basu ƙarasa ba suka ji muryar madam saly tana ɗuro musu ashar ,"
    Ni za'a kawo wa iskanci da tsaurin ido , dan uban ku ni da gidana ina cewa ku fita kuna yin biris da ni , sai kace da uwar ku muka haɗa kuɗin sayan gidan ?? To billahi minti goma yayi kaɗan zan sa a fitar min da ku bayan an chasa min ku ," yau naji jaraba da maSifa ,"

  Tana gama hanya ta fito ta durƙusa a gaban madam saly gami da fashewa da kuka ,"
    Madam dan Allah wanne laifi na miki zaki kore mu ? Ke kaɗai ce gatan mu dan Allah ki yafe min laifin da nayi miki , idan mun bar nan bamu da wurin zuwa ,"!

Ji min mayyar yarinya ? Ta ina na zama gatan ku ? Babu dangin iya babu na baba ? Na gaya miki yaks ni bana jurar asara , asara ce babba na ci da ke na ci da ɗan cikin ki ? Yo wanne aiki kike min da har ya kai na dunga ci da rai uku a biyan aikin ? Ga ki ga ƙanwar ki kuma ga ƙarin wani yanzu kin maƙalo a cikin ki ,' idan har kina son zaman gidan nan sai dai ki samo uban cikin jikin ki nayi masa lissafi kuɗin abincin ɗan sa ya lale ƙuɗi na ya biya ni sannan ,! Tab ina zan iya asara ?

ÆŠa a cikin ta ? Wacce magana ce wannan madam saly take faÉ—i ? Ko dai kunnuwan ta sun daina ji daidai?

   Madam wane ɗa ? Ina ɗan yake ?

Yana ƙundun uwas ki yaks nace yana ƙundun uwas ki , ni zaki yiwa bariki ? Ah lalle fa gwada min firirita irin ta sabuwar karuwa ,"

Sunkui da kai yakaka tayi kan ta yana sake ƙullewa ,"

Wai zaki ki kira ɗan iskan da ya ɗirka miki cikin  ya zo ne ko kuwa kin zaɓi barin gidan ?
    Da sauri tace !
Zan kira shi madam
  Na baki nan zuwa gobe duk inda ɗan iskan yake ki nemo shi yazo ya biya kuɗin ci da ɗan tayin sa ko kuwa yasan inda zai yi da ke ,!  Madam saly ta furta hakan tana mai wucewa ta bar wurin cikin ran ta kuwa tana ayyana irin kuɗin da zata iya samu akan cikin jikin yaks domin kuwa ta san da mutum ɗaya tak yaks tayi harka , bata shakkun shi ya fara sanin yaks kuma shine uban cikin jikin ta , idan kuwa haka ne ai ita ranta ƙwal ,

tun da ta lura da samuwar cikin take farin ciki tare da ƙulla yadda zata yi wannan ciki ya buɗe mata sabuwar hanyar kama kuɗi a hannun wannan hamshaƙin attajirin da yayi mata ɓarin naira akan taraiyar sa da yaks , wanda bata tantama wani hamshaƙin attajiri ne mai muƙami , ko kuwa dai ɗan attajiran , da har yau take mamakin ina baƙauyiya kamar yaks ta samo shi ,?  shi kuma cikin jerin gogaggun matan duniya da suka dace da shi ya rasa ta zaɓa sai ya tsallako kan yaks ? Kai ita tafi danganta tarayyar sa da yaks ma da neman wani cikar burin sa na daban , wata ƙila sa'a aka bashi aka ce ya haɗa da neman kuchakar mace irin yakaka ,wata ƙila kuma wani al'amari ne mai girma ya jirkita tunanin sa da har ta kai shi ga neman yakaka , ita dai ta san ruwa bai tsami banza !

Koma meye ita gaba ta kaita !
   Harƙƴalla da irin su babbar sa'a ce .

Ko batun korar da tayi wa su yakakar , barazana ce kawai ta shirya mata domin ta zaburar ta ta nemo mutumin da ta lura a yanzu bai cikin rayuwar yakakar , da ita kuma take ganin rashin sa a matsayin wani babbar asara , dole ya dawo ya cigaba da harka da yaks ita kuma ta cigaba da samun maƙudan kuɗaɗe ta sanadin hakan ,!

Ta shafe fiye da mintoci biyar a durƙushe nan wurin tana tunani , sai dai duk yadda ta kai ga son fahimtar inda maganganun madam saly suka dosa ta gaza ganewa ,"
    Wanne irin ciki ? Ta san ciki ake a haifi ɗan mutum , to amma ita bata da wani sani akan yadda ake a ɗau cikin ɗan mutum ! Tasan dai sai anyi aure ake haihuwar , to ai ita bata yi auren ba ! Kuma da madam saly take cewa tana da ciki , ina cikin a jikin ta ? Cewa take cikin mata huruwa yake ya zama ƙatoto sai a haihu ,? Ita kuwa nata cikin shafal yake ,"babu ko alamun tudu ,"

Wata sabuwar tambayar ce ta kutso cikin tunanin ta , toh kuma waye baban É—an cikin nata da madam.saly take cewa ta nemo ?
  "Bature kam silum" wani sashi na ran ta ya ayyano mata sunan sa a matsayin uban ɗan cikin ta da ake ikirarin tana da shi ,"

    Ɗan wani tattausan murmushi ya ratso tsakanin hawayen fuskar ta ya bayyana kan sa ,"
       Kome da ya dangance shi sanyata nishaɗi yake tare da farin ciki duk kuwa yadda ta kai ga shiga halin damuwa da tashin hankali ƙaunar sa daban ce cikin ran ta tafe take da wani irin kakkarfan shauƙi mai bata kuzari ,'
       Ina son ka dayawa !
ta furta hakan a sarari tana mai dafe marar ta da take É—an yin ciwo kaÉ—an ,"
    Karaf kalmar ta sauka a kunnuwan falmata wacce jin wucewar madam.saly da yadda ta kaya tsakanin su da yakaka , ya sanya ta fitowa duba yakakar bayan ɗan gajeran zaman jiran shigowar ta ɗakin da tayi domin akwai tarin tambayoyin da take son yi mata ,"

Rashin shigowar yakaka da wuri ya sanya ta gaza jiran ta , sashin ran ta na fatan ba ciwo ne ya sake turnuƙe yakakar ba , sai dai kalmar da taji yakakar ta ambata a kunnuwan ta ya sanya ta sa kalmar a jerin tambayoyin da take son yi mata .

Hannu ta kai ta lalubo kafadun yakaka ta É—ora hannuwan ta duk biyu kan kafadun tana fuskantar ta ta buÉ—e idanun ta sosai tamkar dai tana Ganin ta ,
    Yakaka dagaske ne kina da cikin shege ? Zaki haifi yaro ba tare da kin yi aure ba irin na falta?

    A hankali ta sauke hannun falmata daga kafaɗun ta , ta rike hannayen cikin hannun ta ," tare da yin ƙasa ƙasa da muryar ta ,"
   Bani da cikin shege falmata ƙarya madam take min so kawai take ta kore mu ,!
    Ɗan jim falmata tayi cikin rashin gamsuwa ,! Kafin ta sake jefawa yakaka wata tambayar
    To waye ne naji kin ce kina son shi dayawa ? Waye shi ?
    Kallon fuskar falmatan tayi a ɗan hargitse tana jin wani yanayi cikin ran ta ,"
       Bature kam silum ! ,"yakaka ta furta hakan a ƙasan maƙoshi.
   Ɗan zaro idanu falmata tayi tamkar tana ganin ta ,"

Nduwodo bature kam silum ? Ndan shaa noum3 ? ( wanene bature kam silum aina kika san shi )
   Kaam shaa banaangndi3 .' ( mutumin da na taimakawa )

Chaaman shaa ra'amaa ? ( daman son shi kike ? )

Shii shaawa shaa rumiind3 tayd3zin zayyrod3 , ( yana da kyau baki gan shi ba É—an gayu da shi )

ÆŠan murmushi ne ya subucewa falmata wanda ya zarce zuwa dariya , cikin muryar dariyar ta ce
    Har naji ya burge ni NIMA INA SON SHI!
     Da wani irin yanayi mai daɗi yakaka ta jaa falmata cikin jikin ta tana jin yadda ƙaunar falmatan yake zagaya duk hanyoyin jinin ta , tun da daɗewa ta sani falmata mai taya ta son abun da take so ne kome lalacewar wannan abun shi yasa ƙaunar falmata ta fifita akan duk wata ƙauna da take zagaye jinin jikin ta !
      Cikin satin ta ɗan samu sauƙin walakanci tare da bautawar da madam saly take yi mata saboda kullum cikin gilla mata ƙarya take akan uban cikin jikin ta yana nan tafe , wanda har yanzu ba wai ta yadda da cewa tana da cikin bane , neman hanyar da zata sa madam saly ta haƙura ta ƙƴale ta ta cigaba da zama gidan ta take ,  duk da cewa a halin yanzu duk ta yadda ta ci abu mai ƙarni ko yaya ne sai tayi aman sa wanda yake wahalshe ta sosai , sai kuma a wasu lokutan yawu ya kan ɗan taru mata a baki ,  bayan hakan babu wani alamun ciki da ya bayyana a gare ta wanda ita a ƙaramin sanin ta zai sa ta yadda tana da cikin ,"
      Amma ba'a je ko ina ba madam saly ta farga da cewa ƙarya ce yakaka take gilla mata sumfiri-sumfiri wanda hakan ya fusata ta , ta shiga saukewa yakaka kwandunan bala'i da masifa gami da sanya ta aiki babu dare ba rana tana kuma sake tisa mata a kullum cewa gaf take da ta kore su ,

Daga yakaka har falmata hankulan su a tashe yake akan tsangwamar da madam saly take yi musu , ita yakaka bata san wata hanya da zata bi ta nemo youssouf ba baya ga lambar wayar sa wacce ita kuma tun kwanaki biyar da suka wuce da madam saly ta turke ta ta sa ta kira lambar sa ƙwaya ɗaya jal da yake kiran ta da ita a lokacin da suke tare , sai dai kiran farko da tayi da ya shiga , har ta gama ƙara ba'a ɗauka ba , to tun daga sannan ko ta kira lambar bata tafiya , daga tayi alamun ta shiga sai ta katse , ga alama an datse hanyar shigar kiran daga computer.
Chapter 61 · 0% Book details