Sashe 165
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka yi sallama , ajiyar zuciya ya sauƙe yana nazarin Kalmomin Maimartaba kamar akwai dalilin yin su ,musamman ma tambayar da yayi masa a farko.
Nisawa yayi kana ya dubi fuskar wayar sa ya ga agogo ƙarfe uku na yamma ta kusa , can gida Niger yanzu tara na dare ne kenan Maimartaba yana sashin sa suka yi waya ? Bai tare da hajiya Umma domin da zai haɗa su su gaisa .
Kawar da tunanin yayi ta hanyar lalubo layin wayar maimounatu bata jima tana ƙara ba ta ɗaga cike da salonta na ƙwarƙwasa wanda yake da tasiri sosai agare shi ,
Yana nan a tsaye a wajen ya kwashi fiye da rabin awa yana hirar da ita ke tsawaita masu ita ta hanyar amfani da daÉ—aÉ—an kalmomin ta ,
Da suke É—umama masa zuciya da jiki daga barin jin matsanancin sanyin da ke farfajiyar wajen .
Da kyar suka rabu kafin ya ƙira Siyama sama-sama suka yi hirar da yafi karkatata ga tambayar lamuran da suka shafi 'yar sa ita kuma siyama tafi damuwa da lafiyar sa tare da lamuran sa na yau da kullum .
Bayan sun gama wayar ya maida ta aljihu ya ɗaga kai yana kallon yadda garin yake lulluɓe da tsananin sanyi .
juyawa yayi ya koma ciki nan ya tarar da irin ɓarnar da Mama take yi ta gan-gama wuta sosai a ɗan wajen hura wuta har wutar ta fito waje tana gaf da kama 'yan ƙananun kayan wasan ta da ta riga ta jefa wasu cikin wutar da hakan ya sa wutar ƙara ruruwa sosai .
" Mama me kike haka ?
Yace da maɗaukakin sauti da ya sa daga Mama har ita kan ta Falmata suka firgita , da sauri Falmata ta yunƙura tana laluben Mama cikin tambayar me take yi ?
Biyamuradi da takaicin yadda Falmata take yin jugum kamar mutum-mutumi ya fara isar sa ya dube ta a fusace ,
"Tayaya zaki iya sanin me take yi bayan baki da wani aiki sai tunanin wofi tamkar kin fi kowa damuwa a duniya ,
Saitin da yake Falmata ta maida ganin ta da kalamansa suka tunzuro ta ƙari da takaicin hirar da yake da matan banza a zaton ta ,
Muryar ta babu ƙarfi sosai tace ,
" ai ni miskiniya ce marar ido da bata wuce mabaraciya ba , da zai fi dacewa a cikin matan da kake taɗi da su kullum ka auri ɗaya da zata dunga kula da gida sosai ,
Chak ya tsaya daga tattara kayan wasan Mama , ya maida ganin sa kanta , yanzu ya samu ƙarin haske akan yadda ta sauya yake ganinta koyaushe cikin fushi da ɓacin rai ashe kishi ne ke cin ran ta ,
Murmushi yayi ya bar abunda yake tare da dawowa gefen ta ya zauna ya riƙo hannun ta , tausasa muryar sa yayi yana me tsare ta da ido yace ,
" Fatima ki saurareni , ki ji abunda zan faÉ—a miki a yanzou domin shi zai amfanar mouna ni da ke , matan da kike ji ina waya da su su biyu ba matan banza bane Matana ne su ma kamar yadda kike Matata .
Kamar ya caka mata wuƙa sai ta zame hannun ta daga cikin nasa , bakin na motsi a hankali ,
Bai kula da yanayin ta ba saboda ya shirya faɗa mata gaskiya a yanzu , ya sake riƙo hannun ta tare da cigaba da magana ,
" Fatima kiyi haƙuri amma yau zani faɗi miki doukkanin haƙiƙanin gaskiya bisa kaina .
Bai jira amsar ta ba ya shiga bata labarin ko shi wanene tiryan-tiryan , tundaga sunan sa na gaskiya, kasancewar sa ɗan sarki , aikin sa zuwan sa Nigeria auren sa da matan sa , abu guda ya ɓoye mata haƙiƙanin dangantakar sa da Yakaka .
Tamkar a mafarki haka Falmata ta tsincin wasu kalmomin nasa , cikin wani irin yanayi da ta gaza tantance wanne iri ne , muryar ta can ƙasan maƙoshi , tace da shi
" Duk cikin labarin da ka bani baka faÉ—a min lokacin da kuka yi aure da 'yar uwata ba ?
Mukut ! Youssouf ya haɗiye busasshen yawu tambayar ta zo masa a bazata ta yi masa dirar mikiya bai kuma shirya amsar bata ba a yanzu ,
" Fatima zan faÉ—i miki wannan labarin a gaba cikin lokaci na mussaman ba yanzu ba ,
Cikin rashin yarda da ya mamaye tunanin ta ta fara girgiza kai ,
" a ah yanzu nake so ka faÉ—a min muddin kana so na yarda da duk labarin da ka bani yanzu ,
zaro ido yayi yana duban fuskar ta da ƙwayar idanun ta da suke cike taf da rikici da tashin hankali ,
Ya É—an É—aga sauti yana murza yatsun ta dake cikin hannun sa ,
" Fatima ki nutsu nace zan faÉ—a miki watarana a gaba ,
Warce hannunta tayi da ƙarfi daga cikin nasa ta matsa daga kusa da shi cikin ɗaga sauti ita ma ta ce masa
" Ba gaskiya bane muddin baka faɗa min yadda kuka yi aure da Yakaka ba kai ba kaine Baban Mama ba ƙarya kake min ,
 Tsawar da ya daka mata tare da buga teburin gaban su shi yasa Mama fashewa da kuka da gudu tayi jikin Falmata ,
  wannan karon ya kaurara murya da wani irin amo da bata taɓa jin sa da irin ta ba cikin sigar gargaɗi yace mata ,
 " Fatima ki min shiru , ki min shiru nace kar ki sake cewa ƙala ,
Fuskar sa tayi jazir , jijiyoyin kansa sun fito ruɗu-rudu , baki ɗayan jikin sa yana rawa , ɓacin rai sosai ya sauƙo masa , zafin zuciyar sa irin ta soji ta hayyaƙo ,
A zabari ya miƙe ya shiga ɗaki , yayi tsaye hannun sa a dunƙule , ya rasa me yake yi masa daɗi wani irin ɓacin rai me tafe da tsoro-tsoro da a lokacin ya rasa tsoron meye ? Shine yake cin sa ,
Jibgegiyar rigar sanyin sa iya guiwa dake ajiye a gefen gado ya É—auka ya rufa akan kayan sanyin da daman suke jikin sa ya fito daga É—akin ,
Satar kallon inda suke yayi ya ga Falmatan tayi baya da kanta ta kwantar akan kujerar Mama kuma tana maƙale a jikinta tana kallon sa da raunanan idanun ta ,
Tausayin 'yar sa ya kawo masa , da hannu ya yafice ta , da sauri ta sauƙa tayi wajen sa ,
Ɗaukar ta yayi ya koma cikin ɗakin ita ma ya ƙara mata rigar sanyi tare da sauya mata hular da tafi ta kan ta nawi ya sungume ta suka fito falon ba tare da ya dubi sashin da Falmata take ba ya nufi ƙofar fita ,
Mama da idanun ta ke kan Mamar ta cikin siririyar Muryar ta tace
"Papa ma....
'shit
Yace mata yana ɗora yatsan sa manuni akan bakin ta , shiru tayi tana kallon sa suka ƙarasa ficewa daga gidan ya ja ƙofar
Ƙarar rufuwar ƙofar ya zo tare da zubowar kauraran hawayen ta , da duk motsin su daman yana kunnen ta ,
Kuka ta fashe da shi mai sauti tare da jin wani sabon tashin hankali har ta rasa takamaimai da wanne zata ji ?
Shin laifi ne dan ta tambaye shi game da yayar ta ? A sautin sa ta tsinkayo tashin hankalin da yake tafe da rashin gaskiya shin meye yake boye mata bayan wanda a yau ya bayyana mata da ta haƙiƙance ta kuma yarda ɗari cikin ɗari gaskiyar sa ya feɗe mata da ita kuma ganin wannan damar ne ya sa tayi amfani da ita wajen shigo masa da tambayar da ta kwashi shekaru tana cinta a rai ,
" Yaushe suka yi aure shi da Yakaka alhalin ita bata san lokacin ba ??
Tana share hawaye wasu na zubowa ,
"Wai ashe daman har yana da mata biyu ita bata sani ba ?ashe mijin su ne su uku ? Tausayin kanta ta ji ya kawo mata , tabbas ita ba kome bace a wajen sa face wacce ya taimaka ya aure ta sanadin 'yar yayar ta , ba kuma zata taɓa zama kome a wajen sa ba ,
'idan kuwa haka ne dole tayi haƙuri ta haɗiye kome ta kuma bar kome domin ta cigaba da zama a ƙarƙashin sa tare da Mama , a zahiri yake ai shi yafi ƙarfin auren ta , wacece ita ? Miskiniyar ɗiyar talakawa 'yar gudun hijira ? Babu shakka bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane ,
Ya zama dole ta bashi haƙuri idan ya dawo ta kuma alƙawarta cikin ran ta baza ta sake yi masa batun Yakaka ba .
Ta É—au lokaci a haka cikin kukan zuci da damuwa , kafin ta kintata tayi sallar la'asar da take da tabbacin lokacin ta ya shigo ,
A ƙasa inda tayi sallar ta cigaba da zama tunaninnika sun mata yawa , ta ƙagauta ƙwarai ta ji motsin shigowar sa ta bashi haƙuri ,
Daƙiƙoki suka dunga hanzarin wucewa suna zama mintoci har suka ɗebi awannin da Falmata ta ji su tamkar sati guda tayi tayi a zaune ,
Ta tashi ta tsaya yafi a ƙirga ta matsa jikin ƙofa ta laluba , ta kasa kunne ko zata ji motsin su , har dai ta tabbatar sun yi nisa da ita sosai ,
Wani irin mummunan tashin hankali ne ya dirar mata sakamakon tunanin da ya gitta ƙwaƙwalwar ta kan cewa ya ɗauke ɗiyar sa sun tafi sun bar mata gidan , ya sauya muhalli sun yi nesa da ita har abada , ya tafi ya bar ta a uwa duniya ƙasar da bata san kowa ba ko yaren su bata ji ,
Wannan karon kukan da ta fashe da shi tafe yake da amon matsanancin tsoro da ruÉ—ewa ,
Da gudu ta taka tayi nufin fita sai dai karon da ta ci da kujera yasa tayi baya cikin sa'a ta zauna daɓas akan kujerar kusa da ita ,