Sashe 149
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Hajja ina Fatima tare da mama sun ka tafi tun shigowata ban ji motsin su ba ,
Nan suka shiga gidan su Zainaba ta je ayi mata kitso da kunshin tafiya . Ai tana gaf da shigowa ma .
Ƙunshi kuma hajja ?
  Tafiyar mu ai ta neman lafiya ce hajja ba'a buƙatar duk irin wannan shirye-shiryen ,
Ta gefen ido hajja ta dube shi , Babban soja ai shi ƙunshi ado ne ga ɗiya mace ...
Sallamar Falmata ita ta hana ta ƙarasa zancen ,
Da gudu mama ta saki hannun Falmata da take yiwa jagora ta nufi Baban ta
 Papa bienvenue , ta ƙarasa shigewa jikin sa da ya buɗe mata hannunwan sa , ta kwantar da kan ta a ƙirjin sa , ya shafi kan ta yana sauƙe idanun sa akan Falmata da take ƙarasowa wajen jikin ta sanye da dogon hijabin ta har ƙwauri ta zauna daga ƙasa a gefe ,
Sashin da take hasashen yana wajen ta fuskan ta cikin nutsuwa ta gaishe shi fuskar ta kadaran-kadahan .
Ya amsa yana bin fuskar ta da kallo da kitson da aka mata ya sake fiddo ƙyallin fatar ta tare da bayyana hasken goshin ta ,
Hajja wacce bata zama a tsakanin su ta yunƙura ta miƙe riƙe da jakankunan a hannu ta nufi ɗaki , tana ƙiran mama wacce tayi biris da ita taƙi amsawa sai ma sake lafewa da tayi a jikin baban ta .
Fatima ya shiri ? Kin kammala kou ?
Eh mun kammala tace
To madallah gobe insha Allah zamou tafi ku zama cikin shiri kin ji kou ?
Toh ta amsa tana gyaÉ—a kai !
Shiru ne ya É—an gitta tsakani , kafin mama ta É—ago kan ta daga jikin Baban ta ,
Papa , an mana kitso ni da Mamaa na ka gani yayi chau ?
Ta janye hular kan ta , manyan kitson chuku da aka mata suka bayyana , duk da kitson manya-manya ne amma sun yi kyaun zane kasantuwar ta me yalwar gashi sai ya ƙarawa kyaun kitson armashi .
Shafa kan nata yayi yana murmushi yace ,
wow c'est très beau ,
  Da dariya ta bar jikin sa ta nufi Falmata tana zuwa ta fara kici-kicin buɗe mata kai ,
Mamaa ke ma ki nunawa papa kitson ki , yafi nawa ma chau ko papa ?
A hankali ya gyaÉ—a mata kai yana jingina bayan sa da jikin kujerar ba tare da ya janye ganin sa daga kan su ba ,
 Ture hannun ta Falmata tayi ta ɗan ɗaga sauti ,
  Ki bari mama ba na hana ki buɗe min kai ba ?
  Ba tare da ta sauke hannuwan ta daga kan falmata ba tace
 Ai papa ne zai gani .
Tsawa tayi mata lokacin da take son ta sauƙe mata hijabin a tilas ,
Firgita tayi ta ja baya ta rakuɓe tana ƙwalan-ƙwalan da ido tare da raba kallon ta tsakanin mamar ta da baban ta ,
  A hankali wasu siraran ƙwalla suka silalo daga gurbin idanun ta ganin an mata abunda ba'a saba yi mata ba ba kuma tare da an rarrashe ta ba ,
Cikin ran ta taji shirun da tayi tare da sanin manufar sa , dagulewar zuciyar ta ya zo dai-dai da zubar hawayen Mama ,
Hannu ta ɗaga ta fara lalubar inda take jin tashin shisshiƙar kukan ta , ta jawo ta jikin ta tare da ɗaura ta akan cinyoyin ta ,
 Kwantar da kan ta tayi da ƙarfi a jikin mamar ta gami da fashewa da kukan da tayi tanadin sa ,
Kamar ruwan maÉ—aci haka take jin É—acin sautin kukan ta daga cikin zuciyar ta, dan haka ta fara aikin lallashin ta ,
Hannu ta kai ta zame hajibin nata , ƙananan kitson da aka mata yir-yir suka bayyana
 Ta karya murya cikin kuikoyon muryar mama tace :
Papa ka ga kitso na yayi chau ??
A hankali ta ɗago kan ta daga jikin ta idanun ta jage-jage da hawayen rikici , ta washe ƴan haƙoran ta lokacin da take kama dogon jelar kitson shade ,'( me hawa biyu ) da aka tufke shi ya sauƙa kan dokin wuyan ta , ta waiga tana duban Baban ta wanda duk abunda suke yana bin su da ido ,
ransa cike taf da ƙauna tare da shauƙin soyayyar dake tsakanin uwa da ɗiyar ta .
Muryar ta kamar ba ita ke kuka yanzu ba tace ,
Papa ka ga kitson mamaa na yayi chau ko ?
Yunƙurawa yayi ya matso sosai gaban kujerar da yake kai ,
Yana Æ´ar dariyar yadda fuskar falmata take a É—aure tana wani takurewa yace ,
Ai tayi nissa daga can bani ganin kitson nata , ta matso nan kussa na gani kou ? Ya ƙarasa zancen yana karya wuya .
Eh Mamaa ki zo ya gani ,
Ta jawo hannun Falmata , gudun rikici ya sa Falmata ta biye mata ta taso ta biyo ta , gaf da ƙafafun sa Mama ta zaunar da ita ,
  Idanun sa ya sauƙe akan kitson da suke yir-yir kamar inji ne ya jera , ƙwarai kyaun kitson ya birge shi .
Basu yi aune ba ta jaa hannun Baban ta ta É—ora akan Falmata ,
Papa ka ga ni ?
Ta ce tana washe masa haƙoranta .
Kasa janye hannun nasa yayi daga kan ta , saboda wani irin yanayi da yake ji yana zagaya illahirin jikin sa ,
Tundaga kan yatsar kafar ta taji tashin tsikar jikin ta , da wani yanayi da ya tsinka gudun jinin jikin ta , irin yadda bata taɓa ji ba a rayuwar ta , bakiɗayan jikin ta babu kuzari ,
Ganin shirun su ya tsawaita ya sa Mama ta raba ganin ta a tsakanin su , kafin ta É—an turo baki ,
Papaa , baka ce kitson mama yayi kyau ba ??
Cikin dai-daita nutsuwar sa ya janye hannun sa daga kan ta ya janyo Mama Zuwa jikin sa ,
Kitson Maman Mama yayi kyau sossai
très belle .
Batare da ta ƙara daƙiƙa guda ba ta miƙe , tana nufar hanyar ɗakin hajja , zuciyar ta na cigaba da tsananta bugu , cikin kowanne takun ƙafafunta take jin idanun sa na yi mata rakiya .
9:30pm
Falmata ta sake muskuɗawa tana rufe bakin ta daga gajerar hamma da take yi akai-akai saboda bacci da ya fara cin ƙarfin ta ,
Ita bata kaiwa dare sosai take yin bacci a yawancin lokuta ƙarfe takwas da rabi na dare sun yi bacci ita da Mama , shiyasa yau da hajja ta buƙaci son suyi magana ta zo kuma ta tadda ta tana shafa'i da wutiri , bayan ta idar kuma ta ɗora da addu'o'i , duk sai zaman jiran ya gundure ta bacci yake kawo mata samame ,
Falmata , Falmata . Ko kin yi baccin ne ?
Na'am hajja idona biyu .
To taso ki zo nan kusa da ni magana nake so muyi ,
a hankali ta taso ta taho inda take jin tashin muryar hajja ta zauna daga gefen ta bisa dardumar sallah .
Fatima ki nutsu da kyau ki saurareni , da kunnen basira , kin ga wannan tafiyar da za kuyi ke da Mijinki tamkar wata babbar dama ce Allah ya baki da za kiyi ƙoƙari ki dai-daita zaman ku ke da shi , ki ƙarbo martabar ki ta ɗiya mace , cikakkiyar matar aure , ke yanzu ba yarinya ƙanƙanuwa bace ba , da za'a zauna ana yi miki bayani dalla-dallah baƙi da fari akan aure , shekaru biyar ana cikin na shida da yin auren ku , lokaci yayi da yakamata ku kawo ƙarshen wannan zaman kai da ƙafar da kuke yi a tsakanin ku , ku haɗa kai ku rungumi junan ku cikin inuwa da alfarma irin ta aure ,
Ke kece mace bance ba ki bada kan ki ba , amma ki yunƙura kiyi hoɓɓasa cikin dabarun ki na ɗiya mace da Allah yayi miki baiwa da su , ki karkato da hankalin mijinki kan ki , tunda jajayen sawun ki , da sauran damar ki , kina kuma tare da makaman yaƙin da zasu taya ki karɓo kambun ki tun kafin damar ki ta kufce miki , futsanci , jin kai , halin ko inkula da miji ba naki bane , yanzu anwuce wannan zamanin , zamani ne muke ciki na tarairayar miji a gatata shi ta yadda za'a masa riƙon tsauri da kufcewa zata masa wahala , kin dai ji na faɗa miki .
turai zaku je , kiyi ƙoƙari ki sau jiki , ki shige masa , ƴan kananun kayan nan da yace ana saka su a can ki sa ya kawo miki su dayawa kullum ki dunga yi masa ado da su , daman ga ki da kyakkyawan jiki.....
Ƙananun kaya fa kika ce hajja ?
Falmata ta katse ta tana yamutsa fuska .
Eh su nace to meye ba mijinki bane ? Wani ma yayi rawa bare É—an makaÉ—i ? Cewa nake kowa a garin su yake sawa ? To ke meye laifin ki idan kin yiwa mijinki ado da su ? Ji min rashin wayo .
Ta mula kafin ta cigaba da cewa :
Ƴar rangwaɗa da kisisina irin ta mata dunga yi masa , ki raba kan ki da ƙwalafacin Mama ki fara tunanin hanyoyin da za ki bi ki faranta ran mijinki saboda kin ga dai dai-dai gawargado shi yana nuna miki kulawa ke kece kike ƙin bada haɗin kai , to ki sake zane tun dundumin ki da danshi , shi mijin mace huɗu ne .
Ga ƴan magunguna nan na karɓo miki su musamman a wajen uwar zainaba , ta tabbatar min da ingancin su su ma zasu taimaka miki ƙwarai da aniya .
Anya hajja idanun nawa kuwa magungunan nan zasu min aiki ? Amma dai ba na sawa a ido bane kin san fa a asibiti sun hana ni zuba magani a ido ,