Sashe 39
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun kafin su ƙaraso ainahin cikin gidan suka soma tsinkayo muryar madam saly wacce take ta bala'i da dure-duren ashariya akan satar da ta wayi gari an ɗunguma mata har ta naira duba ishirin ,"
Ƙarasowar su ta zo dai-dai da cewar madam saly
," kuma na rantse daga yau duk wasu ƴan zaman fara ƴan zaman alfarma su nemi inda dare yayi musu tun da abun ma ya zama haka , kayi wa mutum rana yayi maka sulusin dare , ji min ganin arhar gabas ? daga yau babu shegiyar ƙaramar karuwa da zata sake kwanan min cikin gida kun dai ji na rantse ai daman kome aka yi da sabara sai ta yi kere,"
ta karasa tana sake shigar da mici-micin idanun ta da suka yi jaa domin bala'i !
Duk da yakaka ba duk kalaman madam saly ta kai ga fahimta ba , amma ganin ta cikin maɗaukakin bacin rai ya haka , yayi matuƙar tsorata ta tare da dukushe mata ƴar ƙwarin guiwar tunkarar ta da batun dawowar su zama a wurin ta ,"
A fusace ta juya ga su yakaka lokacin da taji yakakan tana gaida ta bayan ta ɗurkusa guiwar ta biyu a ƙasa ,"
    Ba tare da ta amsa mata ba ta maida ganin ta kan falmata wacce take tsaye kiƙam tana jujjuya idanun ta kan nan sai sheƙi yake tare da ɗaukar idanu.,'
Wannan ɗan ƙolon fa ? Shi kuma daga ina ??
Cikin sanyin murya da inda-inda yakaka tace" ƙani na ne " tana mai sanya hannu ta jawo hannu falmata ta ɗurkusar da ita ,"
   Ina kwa.....
Ko kafin falmata ta ƙarasa kalmar gaisuwar da ta ɗauko nufin yiwa madam saly , tsawar ta ta katse mata hanzari ,"
  Miƙe miƙe maza-maza ka kama gaban ka , ka tafi barar ka ni nan bani da buƙatar irin ku , ke yaks ɗan uwar ki wane ɗan iskan ne yace ki kawo min ƙanin ki nan ? Ko nace miki ina bukatar almajiri ne ? Oya kama hanyar ka kayi tafiyar ka kwa haɗu a mahaɗar ku kar na sake ganin ka a gidan nan ,"
Gaba É—ayan su sun firgita da tsawar da tayi musu musamman ma falmata wacce kalma korar da aka yi mata ta sanya ta jin ruwan hawaye ya fara taruwa a gurbin idanun ta ,"
Madam kiyi hakuri , shima na kawo shi ne ko akwai aikin da zai dunga yi miki ,?
    Aikin ubanki wannan ɗan tatsitsin yaron zai min ? ,"
  Kai tashi kayi naka guri nace ," ta furta hakan tana zazzarowa falmata ido ,wacce dirin muryar madam saly cikin faɗa duk ya bi ya diririta ta tare da dasa tsoron ta cikin ran ta anan take har ma ta ji ta fara nadamar zaɓar gidan ta a matsayin wurin mafakar ta ,
Cikin muryar kukan da ya bayyana kansa yakaka tace ,"
   Makaho ne madam dan Allah ki taimaka mana ki bamu wurin da zamu dunga kwana wallahi zan dunga yi miki aiki daga safe har dare koh baki biyani ba ni dai kawai ki taimake mu ni da ƙani na ki bamu wurin kwana ,?
Kallon hadarin kaji madam saly take yi ma ta ,"
  Yau ji min gantalallun yara ke yanzu ni ce zan baku masauki ke da musaƙin ƙanin ki ?? Dan uban ki yaks kin ga gida na yayi kama da masaukin baƙin ƴan gudun hijira ?? Ciki ma har da muskinai ? Ke ma ai kin sa wanan abun bazai yi yu bane "auren mage da ɓera " an faɗa miki nan gidan sarkin unguwa ne koh kuwa gidan mai gari ?? To bari kiji ni bani da wurin ajiye ke kan ki bare miskinin ƙanin ki , toh na ci uwar me da ku ??gayyar na ayya gayyar tsiya gayyar ƙwarƙwata da tsumma, dan aikin da kike min daga na ɗaga murya nayi cigiya zan samu madadin ki , dan haka tun wuri ki maida ƙanin ki inda kika ɗauko sa ,ki zo ki kama min aiki na , kina cin lokacin aiki kin kuma san dai doka ta ban yadda da asara ba ,"
ÆŠan liti wanda tun shigowar su yake tsaye a gefe ya kafe yakaka da falmatan da idanu ,yana nazarin É—an dirarren yaron mai Æ´ar kyakkyawar zagayayyar fuska da yakaka ta kira da kanin ta ," yayi charaf ya chafe zancen jin ana shirin korar masa hanyar samun abebaÉ—an arziki !
Haba haba madam saly tayaya arziki yana bin ki kina guje masa ," kuma ai a so kare har bindin sa !
   Ya furta hakan yana farfari da ido
A harzuƙe madam saly wacce ta koma daga bakin kofar ɗakin da ƴan matan ciki ke tattataro ƴan kayayyakin su suna fitowa ta juyo
,' waɗan nan ne hanyar arzikin liti bana son ƙazamar kalma," wai me kuke jira ne ?? Ta wurga tambayar ga yakaka wacce zuwa lokacin kuka take yif-yif suna durkushe cikin rana ,"
 Ke dai mutuniyar mu sanya labule ki ji bayani , kiji nufi na kar ki yanken hukunci baki ji hujja ta ba ,!"idan ban da abun ki ai Abun da ke ga amarya shi ta kan ba ango " Ya furta hakan yana jan hannu madam saly wacce take wurga masa harara ,tamkar idanuwan ta zasu faɗo ,"
 Bayan shuɗewar mintoci sha biyar madam saly da ɗan liti suka dawo ,"
  Ke yaks na yadda ki zauna anan tare da su larki a ɗakin su , zasu ɗan matsa miki wajen kwana domin wannan babban ɗakin kulle sa zan yi , ƙanin naki kuma zai bi ɗan liti su dunga kwana tare idan ya so kullum da safe ya dunga zuwa nan yana min wanke-wanke kafin ya tafi barar sa ," daga yanzu bazan biya ki ko sisi ba domin zan dunga ciyar da ku sau uku a rana da ke da ƙanin naki ,idan kin yadda toh idan kuwa baki yadda ba sai a bi wani sarkin ,!
Ba tare da tunanin kome ba yakaka da falmata suka amince bayan sun bi É—an liti da madam saly da doguwar godiya tare da addu'o'i ,
Toh sai ƙanin naki ya biyo ni yaga ɗakin kwanan koh ? duk da dai ba gani yake yi ba amma ya ɗan tattara wajen da zai sa ƴan haƙarƙarin sa ," ni ya ma sunan sa ne ??
  sunan sa kachalla !
  Ah kachallari ne toh tashi zo mu tafi mikon hannun ka ,"
Tare da rashin sakewa falmata ta jefa hannun ta cikin na ɗan liti , wanda ɗumi tare da laushin fatar hannun falmata tuɓus-tuɓus , suka nemi ruɗar da shi a karon farko ,"
Da ido yakaka ta raka su cikin ranta tana fatan Allah ya sa madam saly ta zamto gatan su ,!
Kichibus yagana suka yi ita da su falmata wacce É—an liti ya matse mata hannu gam cikin nasa yana É—an luguiguitawa , a É—an fisge ta dube su tare da gaishe da É—an liti sai dai kuma fuskar falmata da ta gani a fisge ya sanya ta sake waiwayowa da zabari sai dai bata ci nasarar sake kallon fuskar yaron ba sai bayan sa ',
Tana shigowa ta ci karo da yakaka cikin mamakin ganin ta a wurin aikin tare da alhinin abun da ya faru da su a daren jiya wanda duk a zaton ta har yanzu su yakaka suna asibitin ne ta kamo hannun yakaka ,
  Yakaka ya jikin falmata ??tana ina ? Ta samu sauki da fatan babu abun da ya same ta ??
Sai da yakaka ta É—an hah-hanga ta ga babu kowa a cikin rumfar da suke saida burkutu wanda a halin yanzu take kan tattarawa tare da goge gujeru da teburan da masu saye ke zama ," tace
   Yagana jikin falmata da sauki , kuma a halin yanzu tana gidan nan mun taho tare , yagana dan Allah ki rufa mana asiri domin a saboda abun da ya so faruwa ga falnata jiya mun bar sansanin mu mun dawo nan gidan da zama sai dai a matsayin falmata namiji , zaki ganta cikin shigar maza da askakken kai tana amsa sunan kachalla , domin Allah kar ki faɗawa kowa ita mace ce kin ji ? Ki rufa mana asiri !
   Tare da maɗaukakin mamaki yagana take kallon ta ,
 falmata ta koma namiji kuma ??kuma kun dawo nan gidan da zama ? Anya yakaka wannan hanyar mai billewa da kyau ce ? Kin san fa gidan nan cike yake da ƴan iska da ma unguwar baki ɗaya , ke da kan ki hatsari ne kwanan ki cikin gidan nan kina dai ganin yadda da ƙyar muke kwatar kan mu a hannun ƴan iskan nan idan suka sha kunun madam saly , ni a ganina gwara mazan sansanin mu basa shan wannan ruwan da ke fitar da mutum a hankali ya sa hauka, ni dai idan har kin ɗauki shawara ta ku koma sansani duk lalacewar sa yafi nan ,
Yagana falmata tace baza ta koma ba , ta riga ta tsorata , sanin halin mazan gidan nan ya sa na É—auki matakin mayar da falmata namiji domin kare ta daga idanun su ,"
  Katse ta yagana tayi ,"
  Toh idan kin kare falmata ke kuma fa ?? Bakya tsoron su cutar da ke ??
  Ɗan murmushi yakaka tayi ,"
  Zan iya sadaukar da kome nawa domin na bada kariya ga falmata , falmata miskiniya ce bata da kowa daga Allah sai ni ," ki mana addu'a kawai yagana kuma ki rufa mana asiri ,'
   Kallon ta yagana tayi na ƴan dakikai ,