← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 269

Sashe 79

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanyi da kalolin ƙamshin da ɗakin yake suka sa falmata sakin wani gauron numfashi da tun shigowar su sashin take ta jaan iska ta hancin ta tana jin wata nutsuwa ta musamman na ratsa ta ," tsafta tayi a rayuwa ,"

Cikin shauƙin yakaka ta dunga bin falon da kallo ɗan madaidaicin falon da baya ɗauke da duk wani nau'in tarkace , kome ka gani a falon amfanin sa mai muhimmanci ne kuma yana bigiren da ya dace ,

Tun daga kan ƴan madaidaitan kujerun da suka kewaye falon tare da lallausan kafet har zuwa kan labulayen duk suna ɗauke da launi guda ne ,"ruwan madara ,"  sai gefe guda kuma girkakken gogaggen teburin katako ne shima ruwan madarar da ƴar kujerar sa wanda aka ajiye wata ƴar computer tare da tulin littatafai akan sa ," daga ɗaya sashin kuma ƙaramin firiji ne ,' daga haka babu kome a cikin falon sai sanyin AC da yake daga jikin bangon ɗakin sai kuma ƙamshin mai ɗakin da ya riga ya kama ko'ina na wajen ,"

A ƙasa suka zauna daga su har rahimar da take ta basu labarin party da suka halarta yau , " lokacin da take zazzage kayan da suke cikin leda ta ɗora da basu labarin , bikin da za'a yi na gobe har sai ya fi na yau haɗuwa da yin kyau domin a na goben har da tawagar ango da abokai/dangin sa waɗanda zasu iso a gobe da safe ,'

   Woww wayyo Allah  yakaka wanɗannan ɗanɗasa ɗanɗasan rigunan dan Allah aina big bro ya sayo muku ,? Wayyo Allah ,"
    Haƙoran ta a buɗe falmata ta fara bata labarin shagon da suka je ,' a ƙarshe ta zame ɗankwalin ta , baki siɗik ɗin gashin ta mai cika da tsawo tare da ƙauri ya bayyana ,"
    Kin ga ma har kai sai da aka wanke mana ," ta ɗora da tambayar kin ga takalman da ya saya mana koh ? Su ma masu kyau amma ni dai kamar bazan iya sawa ba dana gwada Su naji  sun min tudu ,"

   haba ! zaki iya sawa mana fatima , kuma wallahi ba ƙaramin kyau zaki yi ba ,
    Wanne ne naki yakaka , wanne ne na fatima ,?
   Ware mata su tayi
Rahimar ta cigaba da santin kyaun kayan , a ƙarshe tayi alƙawarin taya su ƙwalliya tare da shiryawa ," inda har ta zaɓar musu waɗannan dogayen rigunan a matsayin kayan da zasu sa a gobe da yamma dai-dai lokacin da za'a fara gudanar da wushe-wushe a ɗora da sanya lalle ,"

ɗaya ledar ta jawo ta cire musu shawarman da take ciki naɗi uku kowacce ta ɗau ɗaya suƙa fara ci suna ƴar hirar su , har zuwa Lokacin da bacci ya ɗauke su ,"!

********

Misalin sha ɗaya na daren Alhamis biyamuradi youssouf ya samu shigowa cikin gari ƙarƙashin umarni da ya samu daga babbar headquarter su dake chan niemey inda aka bashi awanni arba'in da takwas akan ya je yayi uzurin da ya taso masa na gaugawa kamar yadda ya shida musu  ya dawo ,"

  Shi ya tuƙo kan sa ya keto dazuzzukan da suke da matuƙar hatsari saboda ƴan tawayen boko haram da suka yi bigire a cikin sa ,"

À daren ya so yaje ya gan ta har ma su tattuna cikin awanni arba'in ɗin da yake da damar su yake sa ran zai iya fara gyara ɓarnar da ya tafka ,wanda idan ya samu haɗin kan yarinyar ya na san ran zai wanke hakkin ta da ya ɗauka  ya cigaba da istigfari ,  sai dai yadda garin ya ɗau shiru ya sanya shi barin tafiyar zuwa gobe da safe , ta yadda ko da bai same ta ba kai tsaye zai iya samun abokan hulɗar ta wanda su kuma kai tsaye zasu sada shi da ita ba tare da wata wahala ba ,

Da wannan tunanin ya samarwa da kan sa wurin kwana a hotel É—in da ya saba zama a lokacin da yake sintirin a garin ,!

*******

Tsabar jin daɗin bacci su yakaka ba su suka farka ba sai ƙarfe takwas da ƴan mintoci , hanzari yin sallah suka yi suna dariyar makarar su ,

duk yadda rahima ta so da suyi wanka a banɗakin dake cikin ɗakin nasa , ƙin shiga ɗakin suka yi , yakaka ta turje tace iyakar su falo nan inda suka kwana baza su shiga masa har uwarɗaki ba ,"cikin zuciyar ta tana gargaɗin kan ta akan su kiyaye zarmewa da yawa ,"

A gurguje rahima ta kintsa masa falon yakaka tana taya ta , suka kintsa falon tsaf tamkar yadda suka same shi ,rahima tayi musu umarnin da su bar kayayyakin nasu a É—akin tun da nan É—in yau ma zasu kwana ,!

   Tana sanya mukulli tana rufe kofar falon nasa ƙiran sa ya shigo wayar ta ,"
  Big bro ina kwana ,?

lafiya rahima ,kun tashi ne ?

Mun tashi big bro, " Gamu nan ma muna shirin fitowa ina rufe ƙofar falo ne ,"

   Ki bar ƙofar a buɗe gani nan zuwa ku jira ni ,"

Toh
tace tana sauƙe wayar daga kunnen ta ,"

A shiryen sa yake tsaf cikin ƙananun kayan da suka amshi matsakaicin jikin sa ," fuskar sa babu walwala sosai bayan ya amsa gaisuwar da suke mishi yace ,"

   Ina zaku fita ku je da wuri haka ? Ku koma ku zauna a ciki har zuwa lokacin da za'a kammala abun breakfast sai rahima ta karbo muku ,"

Ba wani wuri zamu ba yaya dakta zamu shiga ciki ne , ko da aiki mu taya su ," ...

  Ke da ba isasshiyar lafiya ce da ke ba shine zaki yi aiki ? Akwai masu aiki , ki kula da lafiyar ki ,' ku koma ciki ku zauna ban yadda ku fita daga nan ba ,' ! 

  Big bro amma ni zan iya shiga ciki ko ? Saboda ka ga....

Sarkin surutu ke zaki iya tafiyar ki , amma ki bar musu mukullin a hannun su , idan anyi girki ki kawo musu , ban yadda ki ɗebo gayyar ƙawayen ki ba , ki kiyaye  .

Toh big bro ta amsa tana jiran ta ji ya jerowa su yakaka sharuÉ—an kula masa da É—akin sa , ga mamakin ta sai gani tayi ya juya yayi tafiyar sa ,

     Da sassarfa ya isa ga motar sa ya buɗe ya shiga ya jaa yana mai barin harabar gidan ya nufi gidan da mahaifiyar sa tayi matsuguni cikin sa , zuciyar sa sam sam babu daɗi ,saboda saƙon da yake ɗauke  da shi akan harshen sa zuwa ga mahaifiyar ta sa ba mai daɗi bane

   Ya rasa mai ya sauyawa mahaifin su ra'ayi bayan wahalar da ya sha kwana da kwanaki ,wurin roƙon sa akan ya amince mahaifiyar su ta tako gidan ayi bikin zainab ɗin tare da ita , da kyar ya samu nasarar shawo kan sa ya amince da ta zo tayi kwana biyu a kammala biki ta koma , sai dai a daren jiya ya sake birkice masa akan rashin amincewar zuwan ta gidan har ma yayi ikirarin idan har ya samu labarin ta zo zai mummunan saɓa mata ,

   Fir yaƙi saurarar sa yaƙi yadda da duk wasu kalaman rarrashi da yake nufin yi masa ,'  yasan mahaifiyar su mai tarin laifuka ce , amma ƙwarai yadda mahaifin su yake nisanta su da ita yana matuƙar damun sa kome lalacewar uwa uwa ce ,"ba'a sauyawa tuwo suna ,"

Da wannan tunanin ya ƙaraso unguwar gami da karya kan motar sa ya gangara , kamar yadda yake a koyaushe unguwar cike take da yara ƙanana suna ta dawurwura a kan hanya , wasun su ko wondo babu , bare takalmi a kafafun su , batun wanka daman babu shi ," hakan ya sa yake tuƙa motar sannu a hankali yana sakin hon lokaci -lokaci saboda yaran da suke ƙaraƙaina , basa ko tsoron mota ,"
   A ƙarƙashin ran sa kuwa har yau bai daina mamaki da son sanin dalilin da ya sa mahaifiyar su zaɓar rayuwar da take yi a wannan ƙazamtatciyar unguwar marar fasali ba , iyakar tunanin sa da tambayoyin da ya sha yi musu daga ita har abban su an rasa mai bashi amsa takamaimai , "

  sai dai yasan koma menene ya faru ne bayan tafiyar sa makarantar gaba da primary ta gwamnatin tarayya ta kwana ,inda bayan dawowar sa hutun zango na farko na aji ɗaya , ya tarar da baki ɗayan rayuwar gidan nasu ta sauya , na farko dai bai tarar da auntie su RAHIMA a gidan ba sai sabuwar RAHIMA jaririyar ƙanwar sa ya tarar ,'

abubuwa dayawa marasa daɗi ya tarar suna ta faruwa daki-daki wanda a ƙarshe ya jawo rabuwar auren iyayen nasu , da kawo karshen duk wata soyaƴyar da ya buɗi ido ya tarar iyayen su nayi wa junan su , hakan ya jefo mahaifiyar su cikin wannan rayuwar da take wanda yake jawo mata zagi da zargi tare da aibatawa daga dangin mahaifin su da shi kan sa ,,"

abun da hasashen sa yake bashi a koyaushe shine , koma menene ya jawo tarwatsewar rayuwar auren iyayen su yana da nasaba da auntie RAHIMA , wacce har zuwa yau da ake É—iban shekaru wurin goma sha takwas babu wanda ya san ina take , a wane hali take cikin duniya ???

Wani ƙaƙƙarfan hon da wata mota dake biye da shi ta sakar masa shi yasa ba shiri ya kauce ya bashi hanya da mugun gudu motar ta wuce ,"hilux", ce baƙa mai ɗauke da baƙaƙen gilasan da ya sa ba'a iya hangen na cikin motar,"

ÆŠan siririn tsaki hamza ya jaa yana aiyanawa a cikin ran sa wasu dai akwai su da wutar ciki ,
Chapter 79 · 0% Book details