Sashe 262
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar wacce aka dokawa guduma a ka haka Sofi ta ji, kunnuwan ta suka rabu da ji na ɗan wani lokaci duk kuwa da cewa a ɗazu Samira ta faɗa mata batun cikin Yakaka amma bata ji dukan zancen irin yanzu ba dan kuwa a ɗazu tana da ƙarfin jikin iya yin zabure-zabure a yanzu kuwa da zancen ya tabbata cewa dai Doctor Hamzan tane ya yiwa Yakaka ciki ji tayi duk wata jijiyar jikin ta tayi tsayuwa daga barin yin aiki na wucin gadi .
A yau taurin zuciyar ta gaza yin tasiri yayi domin kuwa ruwan hawaye ne ya ɓalle mata kamar an buɗa famfo .
Sai shiƙar kukan ta Doctor Hamza ya ji wanda ya mayar da kan sa ga aikin sa .
Tsam yayi yana jin ɗan guntun tausayin ta na kawo masa , daga can ƙasan ran sa sai ya ji kamar fa bai kyauta ba yadda ya sanar mata da batun cikin Yakaka dole za ta iya jin babu daɗi tunda ita Allah bai bata ba musamman da yakasance Sofi tana da bala'in kishi.
A hankali ya ɗago kan sa yana kallon ta sai dai kafin yayi wani yunƙuri ta miƙe kamar ana tunkuɗa ta ta bar wajen .
Girgiza kai yayi yana mai mayar da kan sa ga aikin sa da yake so ya kammala kafin gobe saboda a gobe da yamma yake so ya bar garin zuwa Kano .
Washegari
D
octor Hamza da kansa ya shiga kitchen domin samarwa Yakaka da abunda za ta ci saboda kusan kwana tayi da zazzaɓi asubar farko kuma ta fara Amai .
Dan haka ya kama ta zuwa falo ya kunna mata tv yace tayi kallo kafin ya gama haÉ—a mata abun karyawa.
Ba dan ta so ba ta haƙura ta bar shi ya shiga kitchen sai dan ko kaɗan bata jin ƙarfin jikin ta wata irin kasala ce take bin gaɓɓan jikin ta jikin ta babu ƙarfi gefe guda kuma bata son warin Albasa da tasan muddin ta shiga kitchen to kuwa sai ta shaƙa .
Lokacin da ya gama ya kawo mata bata wani ci dankalin da ya kawo mata tare da ƙwai na kirki ba tace ta ƙoshi .
Yana tsakiya da rarrashin ta kan ta daure ta sake ci kaɗan Sofi ta sauƙo bata dubi inda suke ba ta zauna akan kujera ta ɗau remote.
Lokacin da ya dubi fuskar ta sai da zuciyar sa ta doka da karfi ganin yadda fuskar tata ta kumbura suntum idanun ta kuwa har kamar kwanciyar jini.
Da sauri ya baro Yakaka ya juyo gare ta "Subhananlah Sofi me ya same ki haka ? cikin dare ɓarayi sun shigo gidannan ne ?
Ba tare da ta dube shi ba tace "Da aljanu muka yi dambe ko ka manta?
Yadda tayi maganar a cushe ya so ba shi dariya amma sai ya gintse fahimta da yayi so take ta zo da rainin na ta da tayi alƙawarin ta daina '
"Oh i see .
Yace yana barin kusa da ita ya koma ga Yakaka wacce ita ma ta tsorata da ganin yadda Fuskar Sofi ta kumbura tayi jawur kamar wacce ta shiga filin dambe da wanda ya fi ƙarfin ta .
Bayan ya shirya ya fito gargaÉ—i ya yiwa Sofi kan kada ta yarda ta fita ko'ina ta zauna ta kula masa da Wafaa .
Kafin azahar zai dawo su yi Sallama saboda bayan Azahar zai tafi .
Bai yi zaton samun amsa mai daɗi daga gurin ta ba amma ga mamakin sa sai ya ji ta amsa har tana masa fatan alheri hakan sai ya faranta masa tare da ƙara masa kuzari ya bar gidan cike da nishaɗi farin-ciki goma da ashirin .
Sai dai yana fita Sofi ma ta fice kai tsaye inda suka yi za su haɗu sa Samy baby domin ta bata cikon kuɗin da za'a yi harkokin aiki kama daga kuɗin jirgi da Samy Baby ta bata tabbacin ta samu wanda zai mata hanya muddin ta saki kuɗi cikin kwanaki uku ma za ta ɗaga India, da yake kan Sofi ya kunce ilmin zamanin ta tare da wayewar ta sai suka gaza yi mata amfani saboda taƙi basu dama shaiɗan da muƙarraban sa kaɗai ta sau wa ragamar rayuwar ta cikin tsakanin jiya da yau ko ibada ta daina yi kwata-kwata da daman dai ba sosai take tsayar da Sallah ba amma daga jiya zuwa yau ko Sallah ɗaya bata yi ba, cikar mummunan burin ta kawai take mafarki a bacci ko a farke ita dai burin ta ta ga bayan Yakaka "kaicho Sofi .
Haka ta É—au kuÉ—i zunzurutu naira Miliyan biyar da dubu dari shida ta bawa aminiyar ta Samy Baby bayan naira Miliyan huÉ—u da rabi da su kenan kuÉ—in da ke account É—in ta da tun a jiya tayi transfer su zuwa account na Samira.
Wannan farin kudin kuwa kudin duk wasu gwala-gwalan ta ne tare da wani daya na Momy kori da ta amsa Aro bata mayar mata ba duk ta hada su ta sayar ta dankawa Samira kudin.Â
"Samira dan Allah ki tabbatar kome ya tafi yadda ya dace kin ga Doctor tafiya zai yi to so nake kafin ya Dawo kome ya kammala sai dai ya dawo ya tarar da gawa kawai .
"Kar ki damu ƙawata to meye amfanin ƙawancen mu idan ban miki ba ? Ke ce fa Sofiya ? kar ki damu jibi-jibin nan zan bar ƙasar nan ke dai ki kwantar da hankalin ki bana son yadda duk kika bi kika tada hankalin ki kin ga yadda kika koma kuwa? Kamar wata bazaurar Jaɓa .
Ɗauke kai Sofi tayi tana jin zagin walaƙancin da Sofi tayi mata a fakaice .
Cikin wayencewa Sami baby ta miƙa hannu ta ɗau wayar Sofi da take ajiye a tsakanin su ba tare da Sofin ta hana ta ba tayi wasu 'yan taɓe-taɓen ta a wayar ta ajiye mata daga nan Sallama suka yi saboda Sofi ta ce bata so Doctor Hamza ya dawo bata gida .
Haka kowaccen su ta nufi motar ta Sofi ita ce ta fara barin harabar wajen kafin Samy Baby ma ta tada tata motar ta jaa ta cike da nishaÉ—i ta kama hanya '
Kome ya tafi mata dai-dai yadda ta tsara yanzu abunda ya rage mata kawai shine ta tattara duk wasu abubuwan da ta mallaka a garin Abuja ta cika motar ta ta bar garin zuwa garin Damaturu inda ta zaɓa domin gina sabuwar rayuwar ta .
Ita da Sofi kuma daga ta ƙarasa rufta ta a rami kamar yadda ta shirya a jibi kafin ta bar jahar Abuja sun rabu kenan haihatan ah to aina Sofi ta san za ta kama ta ? Sannan ma cikin shirin ta na ƙarshe da zata yi ta san za ta ingiza Sofi ta aikata abunda zai sa ta iya ƙarasa rayuwar ta a gidan Yari da ba zata samu damar neman ta ba ma dan haka ita ta sha kenan ta kuma rufe shafin Sofiya a rayuwar ta "kayya Samira .
Lokacin da Doctor Hamza ya dawo gida ya tarar da Sofi a kitchen tana girki ba ƙaramin daɗi ya ji ba dan haka ya saki jiki da ita ya tsaya a kitchen ɗin suka yi 'yar hira yana ta jaan ta da wasa .
Ƙarfe biyu dai-dai ya musu Sallama ita da Yakaka bayan ya haɗa su ya musu 'yar nasihar kan su zauna lafiya kafin dawowar su sannan ya ɗau kuɗi masu kauri ya danƙawa Sofi ko za su buƙaci wani abu sai suyi amfani da shi duk da ya san a store da kitchen akwai kome na daga kayan abinci
Dauriya Sosai Yakaka ta nuna lokacin da suka masa rakiya bata yi kuka ba sai Sofi ce ma ke zuba masa shagwaɓa wai za tayi kewar sa shi kuma gaba ɗaya hankalin sa yana kan Yakaka
Ko kaɗan ba son ransa bane yayi nisa da ita a dai-dai wannan lokacin sai dai dan ba yadda zai yi aikin sa aikin ceton rai ne dan haka bashi da zaɓi na lokacin da zai yi tafiya a bakin aiki inda za shi ma ceton rai zai tafi dan haka tilas ne tafiyar sa.
Haka suka yi Sallama cike da alhini ya jaa motar sa da zai tafi da ita zuwa gidan Doctor Suleiman wanda shi ne zai kai shi airport ya koma da motar tasa gidan shi .
Yakaka ita ta bada hanya Sofi ta fara wucewa cikin gidan suna shiga Sofi ta rufe ƙofar ta murɗa ɗan makulli , ta ƙasan ido Yakaka ta dube ta Kallon nan da take tsoro shi ta hango a idanun Sofi idan ba gizo idanun ta ke mata ba ma ta ga kamar tana mata wani guntun murmushi.
Zuciyar ta ta doka da ƙarfi sum-sum ta wuce ɗakin ta ta bar Sofi a wajen .
Kitchen ta shiga a gur-guje tayi girki ta zuba a kula ta bar sauran a tukunya sannan ta jidi ruwan gora da juice É—in da take É—an sha ta kai fridge na É—akin ta ta sa ta dawo ta É—au abincin tazo fitowa daga kitchen É—in ta ga Sofi ta tare hanya har yanzu dai wannan kallon ne a idanun ta sannan bata janye murmushin mugunta da take mata ba .
Muƙut Yakaka ta haɗiye yawun tsoro .
"Mai ciki girki aka yi ne ?
Sofi ta tambaye ta fuskar ta a yanayin da bai yi dai-dai da kalmomin da ta furta ba.
"Eh nayi girki ne Anty Sofi , naki ma yana tukunya daman yanzu zan zuba miki '
"Bari na kai nawa É—aki .
Sai da Sofi ta mula sannan ta É—an matsa da kyar Yakaka ta wuce tana shiga É—aki ta murza É—an makulli tana jin nutsuwa na safko mata daga nan bata sake fita daga É—akin ba har dare komen ta a ciki take yi tsakanin banÉ—aki da tsakar É—akin
Sai wayar ta take yi da Falmata da kuma Lubna da su duka biyun suke cikin watan haihuwar su .