Sashe 159
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yakaka ta furta hakan tana shiƙar kuka lokacin da take jawo jakankunan kayan ta ,
Kukan ta daga ƙasan ran ta yake , kukan tausayin rayuwar ta tare da nadama ,  ina zata je ? Tun zamantowar su 'yan gudun hijira nan gidan ne kaɗai mafakar da suka tsaya cikin ta ba tare da ƙalubale ya cisgesu ba har sai da ita da ta sanya kafafun ta da kan ta ta bar mafakarta ,
Tayi zaton kome zai zo mata da sauƙi zaton ta zai yi saurin yafe mata , tayi tunanin zai tare ta da yawan ƙaunar nan tare da tausayin da ta san yana gwada mata can baya , har ma tana sanya ran cigaba da samun kulawar sa kamar farkon fari ,
Ashe dama ta riga ta kufce mata , ta riga ta É—ibga kashi a inuwar da ta huta ,
ashe ita ɗin yanzu wulaƙantattace a wajen sa ? Ashe yanzu ita abun kƴamata ce da bata wuce a kore ta ba ? Babu shakka ba'a ɓari a kwashe du , hangen hadarin nesa kuma ya sanya ta damal-malewa cikin kashi .
Ɗauki take nema , so take ta samu wanda zai dube ta ya fahimce ta ba tare da ya aibata ta da laifin da ta riga ta aikata ba , ba tare da wani hukunci yayi tsalle kan ta ba sakamakon abunda ta aikata da bai wuce Kaddarar da zata iya hawa kan kowanne ɗan Adam ba .
Malama Maryam ita ce É—aya jal wacce ta sani da tashin farko bayan sanin laifin da ta aikata ta tausasa mata , a yanzu kuma bata nan , tayi komawar ta garin su tun kwanaki biyu da suka wuce .
Shin Mutane ba za su mata uzuri ba ? Ashe haka halli 'yan adam yake ?? Da wanne zata ji ? Ita kenan haka guguwar Rayuwa zata cigaba da walagigi da ita ? Yanzu ina zata ?
"Kar ki tafi Yakaka tsaya ina zuwa .
Rahima ta katse ta bata tsaya jiran amsar ta ba ta fita da É—an gudun ta ,
bata tsaya ba , ta cigaba da jan baccon ta da yafi ƙarfin kinkimar ta , tana yi tana rera kuka da murya mai ban tausayi .
" Yakaka , Yakaka ki tsaya , kar ki tafi nace ki zo Baba yana ƙiran ki .'
Kanta a ƙasa tana sharar ƙwalla ta shiga falon Prof , da ta tadda shi kamar koyaushe a zaune , muddin zai miƙe tsaye sai da sanda mai ƙarƙo .
Muryar ta tana rawa ta gaida shi , ya amsa yana nazarin ta ,
," Me ya faru zaki bar gida 'yata ,? meye dalili ?
Muryar ta na rawa tace
"Yaya dakta ne yace na tafi .
Ya gane wanda take nufi dan haka ya ɗan yi jim cikin ransa yana sake ganin dai-dai kan ƙudirin sa .
"Ki koma ciki , nan gidana ne ba na wasu ba , dan haka babu wanda yake da damar korar ki , kin ji ko ?
',To Baba , nagode ,"
", Madallah ku koma ciki ,'
Bayan tafiyar su ya ɗau wayar sa tare da ƙiran Doctor Hamza wanda tunda ya shiga sashin nasa ya gaza aikata kome illa kai-kawo da yake yi , zuciyar sa na cigaba da tafasa ,
Bayan ajiye wayar sa , sashin Prof ya tasamma , inda ya tarar da shi yana tsimayen sa , bai saurari gaisuwar da yake yi masa ba , ya fara da tambayar sa fuskar sa na nuna ɓacin rai
"Me yarinyar nan tayi maka zaka kore ta ?
Da sauri ya É—ago kan sa yana duban Baba , a zaton sa yau ta zo , sannan Baba bai ma san da zuwan ta ba , ashe ba haka bane .
Shin ƙarar sa ta kawo ? Babu shakka babu kome a bariki sai darussan da ke koyar da tsaurin ido tare da rashin kunya ,
Shiru yayi , ganin yayi shiru ya sa Prof sake jefa masa wata tambayar
"Ko kuwa ta aikata wani abu da ba dai-dai bane ? Ko tana kan aikatawa da ta cancanci kora ?
Shiru Doctor Hamza ya sake yi , kai tsaye ba zai ce ga abunda ya hana shi ya ce kome ba , Bazai ce ga dalilin da yasa ya gaza bayyana laifin ta da yake sirri ne a gurin sa wanda yake tunanin a iya tsakanin su biyu yake, da kuma can inda tayi rayuwar bariki ,
sai dai hankalin sa yafi tafiya akan ya rufawa ƙaryar sa da yayi a baya asiri ne, sanin da yayi Ƙarya wata mummunar ɗabi'a ce da iyayen su suka wanzu suna hanin su da aikatawa ,
"Idan baka da wani dalili ,kar ka sake korar ta , ita ɗiya mace rauni ne da ita a koyaushe , a kuma ko'ina tana buƙatar matallafi ne cikin rayuwar ta , '
" Wanda daga zarar ta rasa mai tallafar ta zata iya faɗawa kowacce irin mummunar rayuwa , yan gudun hijira su ma mutane ne kamar kowa walaƙanta su abune marar kyau , ka kiyaye .
"Zan kiyaye Baba ,
***
Yakaka tana komawa cikin gida bayan Rahima ta kama mata kayanta sun mayar su ɗakin da cikin sa suka zauna ita da Falmata tun farkon zuwan su gidan , muryar ta a ɗan dishe ta ce
 " Rahima yaya Dakta fa yunwa yake ji , da farko da ya shigo yace ki masa girki ,
 Zama Rahima tayi a bakin gado tana ɗan riƙe kanta ,
 "Yakaka wallahi kaina ciwo yake ba kaɗan ba , yau nasha yawo a School ( makaranta ) taimaka ki ɗan dafa masa ko ƴar indomie ce .
Bata ƙarasa zancen ba yakaka ta nufi ƙofa , tana amsawa da "To yanzu zan yi ,"
Bayanta Rahima ta bi da kallo cikin ranta tausayi ne me tarin yawa , Yakaka mai kirki ce kaddarar Rayuwa ce ta faÉ—a mata ta dalilin raunin Ilmi da wayewar ta .
Ita da aka ce ta dafa indomie sai ga ta ta zage damtse wajen girka lafiyayyar jalloup ɗin Spaghetti da ta sha niƙaƙƙen nama da kayan ɗanɗano , cikin sauri da azama take aikin dan haka bata ɗau ɗogon lokaci ba ta kammala , ta tafasa shayi ( tea ) da ya buƙata ta adana su a mazubi me kyau ta ɗora bisa ɗan faranti ,
Zuwa tayi ta samu Rahima tana bacci , bata son tashin ta domin kar ta ƙara mata ciwon kai .
Dan haka ta fita daga É—akin ta koma kitchen tayi tsumu a tsaye hankalin ta ya rabu kashi biyu , tunanin Dakta da yace yana jin yunwa da kuma tsoro da take ji na kai masa abincin ,
Tayi tsayuwar kusan mintuna uku ta gaza ɗaukar abincin kafin daga baya ta gyara zaman hijabin ta ta ɗau tiren tare da nufar sashin nasa da ba baƙo bane a wajen ta ,
Cikin sanɗa take tafiya lokacin da ta shiga sashin nasa a yunƙurin ta na son ta shigar masa da abincin ta fita ba tare da ya san ita ta kawo masa ba ,
Ta zo dai-dai ƙofar tayi tiris ganin ƙofar shiga falon nasa a rufe , ajiye tiren tayi , tana tunanin yadda zata yi ?
Wata dabara ce ta faɗo mata , dan haka ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya kafin ta kai hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar da ɗan ƙarfi , tayi wuf ta juya da saurin ta ,
garam !
ta ji tayi karo da mutum .
Da sauri ta ɗago kanta ganin fuskar sa a murtuƙe yana jifanta da mummunan kallo ya sa ta haɗiyar yawun tsoro ,
", Un- um daman Yaya Dakta abincin ne , Un Rahim..
,"Wuce ki bar nan bana so na sake ganin fuskar ki .
Yace da maÉ—aukakin sauti ,
Sum-sum ta ratsa ta gefen sa da yayi banga-banga yaƙi matsawa tamkar mai shirin jibgar ta ta bar wajen har tana haɗawa da ɗan gudun ta bayan matsanancin bugu da zuciyar ta ke yi .
Sanin darajar abinci ya sa shi É—aukar abincin da ta kawo masa ya shigar da shi falon nasa ya zauna tare da ajiye ledar da ya sayo abinda zai É—an ci ,
Dafadukar shinkafa ce irin wacce aka cika mata ƙaƙale da launi ruwan ɗorawa shar , da ya taka takanas zuwa shahararren gurin sayar da abinci da ake ji da shi a garin ya sayo .
Loma ɗaya-biyu yayi yaji abincin bai masa yadda yake so ba , sam shinkafar ma bata dahu sosai ba a bakin sa , shi yafi son yaji abinci ya dahu sosai ko shinkafar ce yaji ta suɓut-suɓut tuɓus-ɓus daɗin tauna , ba irin wannan dahuwar ƴan gayun ba, da yake hasashen rabin shinkafar sai dai ta ƙarasa dahuwa a cikin sa .
Rufe abincin yayi ya ɗan ture gefe , yayi jugum a zaune , yana tunanin matan zamanin gaba kamar nan da shekara hamsin anya za'a iya cin girkin su ? Ko Amne da take ba tsohuwa tukuf ba salon girkinta ya banbanta dana yaran mata irin su Hafsa, zainab ,Rahima a bar batun Safiyya wannan ba abunda tafi ƙwarewa akai irin Kwaɗon ganyen salad da take cin sa kamar me .
Ɗan satar kallon girkin da Yakaka ta kawo yayi ta wutsiyar idon sa , tsaki yayi tunowa da yayi duk kanwar dai ja ce da girkin su Rahima da na wannan da ya raina dahuwar tasa .
kasa jure yunwar da take sasuƙar sa yayi dan haka cikin yanayin, ya na iya ? Ya ɗauko tiren abincin zuwa kan teburin gaban shi ,
Sai dai Yana É—ora ido akan abincin ya haÉ—iye yawu , da sauri ya É—au chokali yayi bismillah ,gami da kai lomar farko bakin sa ,
Bai saurara ba cikin nutsuwa ya dinga aikawa hanjinsa haƙƙin sa har sai da yaji cikin sa ya samu dai-dai da buƙatar sa sannan ya sarara , a fili yace
", Alhamdulillah wannan ko wacce irin pasta ce haka Rahima ta dafa ? Wataƙila ta zallar Alkama ce ba surki .