Sashe 50
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dan haka a yanzu ma sai ta sake tunasasshe sa game da girman addu'a inda shi kuma ya tabbatar mata da yana yi ,'
Sallama yake shirin yi mata , sai kalaman ta suka katse shi ,"Tu es notre lumière, notre joie, et pour toi nous donnerons le meilleur. En te souhaitant une vie abondante et en bonne santé.Joyeux anniversaire mon fils!,' Allah shi yi maka Albarka shi kare ka du inda kake yaro na ,
Murmushi ne ya suɓce masa halin da ya wayi gari cikin sa ya sa ya ma mance da yau take ranar zagayowar haihuwar sa kalaman ta na yanxu suka suka tunassashe sa,'amsa ya maida mata cikin tsantsar ƙaunar ta da yake ji cikin ran sa ," merci mama je t'aime,"
Daga bangaren ta ajiyar zuciya ta sauke bayan kammala wayar su , babu laifi ta ɗan samu nutsuwar zuciya , sai dai ta kuɗurce a ran ta zata ƙara ƙaimi wurin neman kariyar ubangiji akan ta da ƴaƴan ta , daga makiyan su da ta san suna kewaye da su ,
Juyowar da zata yi domin nufin ta shiga É—aki ta fara sallar walha , idanun ta suka sauka akan hajiya uwa wacce take yi mata wani irin hargitsattsen murmushin da baza ta iya hasashen nufin sa ba , bata san lokacin da ta wanzu a wurin ba domin baya ta bawa kofar shigowa falon nata na ciki ,
Tsawon zaman su baza ta iya tuna rana ta karshe da hajiya saratu ta tako kafafun ta sashin ta ba , basa shiga sassan juna iyakacin su , su haÉ—u a bangaren mai martaba idan haÉ—uwar ta kama dole , ko kuwa wurin gaishe da hajiya uwa ,'
Sannan tayi mamakin ganin ta ita ɗaya kai tsaye har cikin bigiren ta da sai an nemi iznin ta kafin a shigo ,' a sanin ta tare da tawagar ta hajiya saratun zata iso kuma karƙashin jagorancin shugabar bayi ta bangaren ta ,'
Da kallo ta bita lokacin da take yi wa kan ta mazauni akan shimfiÉ—ar alfarma da ta tashi daga kan ta yanzu ,'
Hala uwargidan mai martaba sarauniya tayi mamakin wanzuwa ta gaba gare ta a yau ,? Shi yassa aka gaza wurin taryaa ta kamar yadda ya kamaace ni ,
Fuskar ta babu walwala ta ce ,"
Ban yi mamakin zouwar ki nan ba saratu , shin ƙaƙa za'ai mamakin wanzuwar macce a kowanne bangare cikin gidan amren ta ? Sannun ki da isowa ina miki lale marhaban ,' zama tayi daga ɗaya bangaren shimfiɗar ,'
Suka yi kallon kallo na tsakiyar ido , kafin saratu ta ce ,'
Yau yariman maraÉ—i ke cikkace shekarun sa talatin cikkin duniya , kou ba hakka ba ?
Kallon mamaki hajiya safiyya ta bi ta da shi tana jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa a hankali mafarkin ta na jiya ke dawo mata da fuskar saratu da ta gani cikin mafarkin ," janye idanun ta tayi daga kan ta ,"
Ƙaƙa kin ka sani ? Kafin ta rufe baki saratu ta amsa mata cikin wani yanayi mai tattare da ma'anoni ,ƙaƙa uwa zata kasa sanin ranar haihuwan ɗiyan ta ,? ???
Guntun murmushin fatar bakin ta safiyya tayi ,'haka ne kin yi gaskiya ,!
Kiraye ma ni shi na taya shi murna shine abu da ya kawo ni gaba gare ki ,"
Tsam hajiya safiyya tayi tun haihuwar youssouf yau shekaru talatin saratu bata taɓa taya shi murnar zagowar ranar haihuwar sa ba sai yau ,? Sama ta ka zata ce zata taya shi murna ? Wallah banza bata kai zomo kasuwa ,!
Ta bangaren biyamuradi youssouf kuwa tun yana cikin yin waya da umma yake jin kira yana shigowa wayar ,
Yana gama magana da umma ya bi bayan kiran da ya gani daga wata bakuwar lamba daga ƙasar su , sai dai har kiran ya tsinke ba'a ɗaga ba , yana shirin ajiye wayar ɗan guntun sako daga lambar ya shigo wayar sa ,"
Mon frère, je t'aime tellement. Que toutes les meilleures bénédictions te parviennent aujourd'hui et pour toujours. !Bon anniversaire.!
Sakon taya murnar zagayowar haihuwa ne ,duba lambar ya sake yi yaga bai san ta ba dan haka kawai sai ya share , ya fara koƙarin kiran layin maimouna kamar yadda suka saba kullum safe
Neman iznin shigowa aka yi ya bada izni aka shigo , abincin karyawar sa ne , aka shigo masa da shi,
Da hannu yayi nuni da a ajiye masa abincin ,
Allo ma jolie fille
Allô joyeux anniversaire mon amour ,
ÆŠan jim yayi yana tunanin ta yaya maimouna ta san yau ranar zagayowar haihuwar sa ,? Shi dai ba shi ya sanar da ita ba , '
Princesse wa ya fadi miki wagga batou ?
Cikin dariya ta bashi amsa a iska ta ji , murmushi yayi tare da share batun , suka cigaba da hirar su cikin nutsuwa tare da ƙaunar junan su ,
Wayar su ba mai yankewa da wuri ba ce ,musamman yau da daɗin soyayar ya juyo , dan haka riƙe da wayar ya fita ya wanko bakin sa ya dawo ya zauna cin abincin sa ,
Tashin farko ya kai abincin bakin sa ba tare da bismillah ba , saboda hirar maimouna ta É—auke hankalin sa , haka har ya cinye abincin tas tana zuba masa zantukan soyayya , sai dai me ? yana gama ci ya ji marar sa ta murÉ—a , ba shiri suka yi sallama ,' ga mamakin sa sai kuma ya nemi ciwon ya rasa ,
Dan haka ya tashi yayi shirin sa tsaf cikin kayan sa na soji , ya fito
Ya tarar da duk sauran da ke ƙarƙashin sa ma sun shirya domin a yau zasu ɗan yawata ne cikin daji ta sama ta hanyar jirgi mai saukar ungulu,'helicopter"domin su ga wuraren da ƴan tawayen boko haram suke da mafaka su tabbatar basu tsallaka iyaka sun shiga yankin ƙasar su ba ,'
Suka hau jirgi ya ɗaga da su , sun ga wuraren da boko haram suka yi bigire na dindin-din cikin dazuzzuka tare da matan su da ƴaƴa suna rayuwar su cikin walwala tare da jin daɗi fiye ma da al'ummar cikin gari , abun da ya ɗaure kan youssouf kenan , ƙaƙa ƴan ta'adda irin wannan suka samu bigire cikin ƙasa kamar nigeria ? Shin wake ciyar da su ? Wake kai musu makamai ? Waye ke da alhakin basu magunguna zuwa kaƴan bukatun yau da kullum ?? Tabbas akwai lauje cikin naɗi ,'
Sun samu kimanin awa guda a sama suna shawagi kafin suka sauko , kai tsaye ya wuce cikin tantin sa ya kwanta , gaba É—aya yau ya gaza gane kan sa wani iri yake jin sa tamkar akwai wanda ke sarrafa shi a gefe , yana ji kamar su biyu suke gudanar da kome , amma kuma shi baya ganin kowa ,"
Haka ya yini babu walwala , sun yi waya sau biyu da umma wacce take sake jaddada masa ya riƙe addu"a tare da yawaita karatun kur'ani sai dai kuma abun da bata sani ba shine yau sam-sam ya gaza yin addu'a a yanzu haka da yake kwance ya gagara tashi yayi sallar azahar alhalin kuma la'asar har ta gota , karfe huɗu ma ta wuce , sannu sannu ya fara jin wannan yanayin da yake ji na safe yana sake tado masa , " wata irin mahaukaciyar sha'awa yake ji kamar zai fidda wani sashi na jikin sa ya ajiye koh ya huta ," shi kuwa yau wacce irin masifa ce ta same shi ? Ita ce tambayar da yake yiwa kan sa ,"
Sau biyu sojojin da ke da alhakin kula da lafiyar sa suna leƙowa su duba shi domin sun ji shirun yayi yawa , koh ɗan masallacin da suka tayar suke jam'i cikin sa bai zo yayi sallah tare da su ba a yau baki ɗaya ,
Ga mamakin su duk shigar su a zaune suke tadda shi , sannan kuma yana tabbatar musu da lafiyar sa lau babu abun da ke damun sa , dan haka sai suka kÆ´ale shi ,
Zuwa magariba youssouf ya fara gagara iya riƙe kan sa domin tashin hankalin da yake jin kan sa a ciki ya wuce tunanin sa ya wuce yadda yake ji idan bai sha burkutu ba , wannan karon ji yake yana gab da mutuwa idan bai samu biyan bukatar sa ba ,
Ina zai samu mace a yanzu alhalin yana cikin jeji ? Yaya zai yi ? Dama a cikin gari yake sai ya fita ko'ina ne ya samo wacce zata taya shi ya kauda bala'in da yake ji ,'
miƙewa yayi a dudduƙe ya ɗauki walet ɗin sa tare da ID card ɗin sa , har yayi nufin fita sai kuma ya fasa lokacin da ya kalli jikin sa ya ga yadda ya ke , wani kunya da takaici suka dirar masa , lokaci guda wani duhu ya mamaye masa kwakwalwa da ya sa nan take ya mance da wani batun kunya illah umarni da yaji ana bashi akan ya tafi ,
Yana daga cikin É—akin ya danna kiran masu kula da shi ta wayar hannun sa , ba tare da jinkiri ba suka zo , yace su kawo masa mukullin mota zak É—an fita , " jim suka yi ,toh sai dai basu da ikon musa umarnin sa dan haka suka kawo masa mukullin motar suna jiran su ji yayi musu umarnin su mishi rakiya wani wurin , sai suka ji ya sallame su , ficewa suka yi suka bar shi ," suka nufi bakin masallaci domin yin shirin sallar isha'i
Suna tafiya shima ya fito ya buÉ—e motar ya faÉ—a ,' ya jaa ta da mugun gudu , ya hau titi tare da nufar cikin garin maiduguri a wannan daren ,'