Sashe 29
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun É—an yi tafiya mai nisa kafin su jiyo KiÉ—an da suke ji sama-sama yana sake cika kunnuwan su a yayin da suke dosar wani wajen matattara jama'ah shi yasa suka maida hankulan su suna bin mutanen da suka fara cin karo da su a farfajiyar wajen da kallo ,"
Da farko rumfunan sayar da abinci ne birjik a wurin wanda aka kafa manya-manyan murhu aka ɗora manyan tukwane lamba talatin-arba'in an babbaka wuta a ƙarƙashin su da basa raba ɗaya biyu girki ake ,"
Daga gefe cikin wasu rumfunan kuma shimfiÉ—un tabarmai ne da suke cike da mutane a chakuÉ—e maza da mata , ba'a jin kome sai tashin muryoyin su da dararrakin su ,"
Daga gaban su nan ne wata babbar kofa take wanda kuma daga cikin sa wannan kiÉ—an kalangun ke tasowa ,"
ÆŠaya daga cikin rumfunan sayar da abincin nan suka ga kolo ta nufa inda su ma basu yi wata-wata ba suka bi bayan ta zungui-zungui , daga bakin rumfar ta dakatar da su yayin da ita kuma ta shiga ciki inda suke jiyo tashin muryoyin wasu mata ,"
Kichibus kolo tayi da uwarɗakin ta ,wacce kallo guda za'a mata a ajiyeta a mizanin tatattun karuwan mcmc, duba da yanayin shigar ta na wata matsatsiyar doguwar rigar wani yadi da ya cire kowanne bangare na jikin ta kashi-kashi a sarari ,"uwa uba koɗaɗɗiyar fatar jikin ta da duk man sauya kalar fata ya maida ta dabbare-dabbare , sannan zaƙo-zaƙon faratan hannun ta da suka sha fenti ruwan ɗorawa zuwa gashin ɗokin da ta yaɓa a kan ta launin shanshanbale ,wanda bata samu koh da zarafin ɗaura masa ɗankwali ba ,"
Wata harara ta watsawa kolo da mitsi-mitsin idanun ta da suka sha koren fenti daga sama ," ta tauna cingam ya bada ƙarar bas-bas-tas ,"
Dan ubanki kolo yau sai yanzu kika ga damar zuwa ? Duba agogo karfe nawa yanzu ? Karfe sha biyu saura , toh bari kiji wallahi a kuÉ—in ki zan cire dan ni ba'a min iskancin banza idan kin gaji da aikin ne sai ki faÉ—a na maye gurbin ki da mai so ,"
Kiyi hakuri madam wallahi na tsaya taya ƴan uwa na neman wurin aiki ne kin gan su chan ma tare muka zo domin basu samu gurin yin aikin ba ma ," ta ƙarashe zancen tana mai nuno su yagana waɗanda duk abun da yake faruwa tsakanin kolo da uwarɗakin ta suna ji sarai daga inda suke .
Ɗan leƙawa madam ɗin tayi tayi wa su yakaka wani kallon sama zuwa ƙasa ,"
Ni dai na gaya miki zan cire kuÉ—in awa biyun da kika yi lattin su domin ni bana asara , " ki wuce ki kama aikin ki ," ku kuma "ta sake É—aga murya yadda su yakaka zasu iya jiyo ta
Sai ku shiga daga ciki domin kun yi sa'a jiya-jiya sally fara ,ta bada cigiyar a ƙaro mata ƴan aiki biyu a madafar ta domin cikin tsoffin da da suke mata aikin ɗaya shekaranjiya ta mutu,"
Turus yagana da yakaka suka yi duk da cewa sun fahimci abun da ta sanar da su toh amma inane cikin ? Kuma wacece" sally fara " ?
Ganin yadda suka yi wiƙi-wiƙi suna kallon ta ya sa ta fahimci basu gane nufin ta ba ," ƙas-ƙas ta sake yi da cingam sannan tayi wani turanci ",
Idiyot buladiful marafoka waɗannan ajawos ɗin koh fahimtata ma basa yi ," ke kolo koh kuma ma ke zauna kiyi aikin ki ɗanliti zo tafi da waɗannan garorin ciki wajen sally fara kace ga ƴan aikin cikin madafa an samu ," kai ku bishi dallah kun tsaya sai wani kif-kifta idanu kuke yi kamar an shaƙe akuya a mayanka idiyot buladiful
Sum-sum su yagana suka bi bayan mutumin da aka ƙira da ɗanliti wanda tashin farko idan an hango shi yana tafe za'a zaci wata zarkaɗeɗiyar budurwa ce sakamakon shigar mata da yayi da yadda yake karairaya da lanƙwasa kamar tarwaɗa a cikin ruwa ,"uwa uba kwalliyar da ya rangaɗawa fuskar sa har da yari da ɗan kunne ,"
Suna shiga cikin babban harabar dodon kunnuwan su ya fara tsalle a sakamakon kiɗan gurmi da kalangu da suke tashi ," a babbar harabar da tafi kama da wata ƙaramar makaranta ," mata ne da maza waɗanda kallo ɗaya za'a musu asan mutanen banza ne suke ta kai kawo ,"
Wata ƴar hanya ɗanliti ya bulla da su sai ga su sun bullo a gaban wani waje mai kama da shagon cin abinci ga irin fararen kujeru da teburan su nan birjik a wajen ta tsakanin kujerun da duk babu kowa akai suka wuce suka fito wani babban fili wanda suka taras da wasu manyan murhu da Manyan yankakkun durum bisan su wasu mata na koƙarin haɗa wuta ,"
Wani wari da tsami kamar na ruɓaɓɓen abinci shi ya fara dukan hancin su kafin idanun su yayi tozali da wasu yamusassun mata ƙomaɗaɗɗu suna ta faman wanke jiƙaƙiyar ruɓaɓɓiyar dawa suna subda ruwan yana kwarara zuwa wata katuwar magudanar ruwa ,"
Larki , hema ,duduwa ina madam sally take ? Inji danliti ,"
Koh kafin su amsa masa sai ga wata koɗaɗɗiyar mace da take tsakanin shekaru arba'in da biyar zuwa hamsin ta fito daga wani lungu hannun ta riƙe da wani ƙaton luɗayin kunu da ya kai girman a haɗa kawunan yakaka da yagana ,"
Kai liti yaya anka yi ne eh ? Waɗanan ƙuya-ƙuyan kuma daga ina ?
Daman madam jumai ce tace a kawo miki ƴan aikin ga su nan su biyu an samu ," ya ƙarashe zancen sa yana farfari da ido tare da yarfe hannu ,"
Ta ƙundumo wata ashariya ta makawa madam jumai ," kafin ta ce
Waɗannan ƴan shilan ne zasu min aikin ciki ? Waɗannan ne zasu tuƙa min DURUM ƊIN BURKUTU ? Tirƙashi waɗannan ai basu wuce suna bayan uwar su tana tatsa musu nono suna sha ba ?
Wata dariya da É—aya daga cikin matan da suke aikin wankin dawar nan tayi shi ya katse banbamin masifar da sally fara", take yi ,"
Kin ji madam sally da wani zance ai da rashin tayi akan bar arha da kuma rashin ƙira karen bebe ya bata , ban da abun ki ai gwada su zaki yi ki ga koh zasu iya ," bakya ganin kamar ɗaukar irin su ma yafi riba , zaki mori kuruciyar su da kyau kafin abar ta fara aikin ta , zasu daɗe suna yi miki bauta kina juya su sai yadda kika yi da su ? Ai madam kar ki bari wannan damar ta wuce ki ," ta ƙarashe zancen tana sakin wata sakaryar dariya lokaci guda kuma tana chafe amshin wakar ƙidan kalangun da yake tar-tar kamar a gaban su mai kalangun yake kaɗa gangar sa, "
Ɗan jimm madam sally tayi kafin ta ce toh bari mu gwada ɗin da gwaji jirgin sama ya tashi ," cikin kallon sheƙeƙe ta juyo ga su yagana waɗanda suka yi jugum suna sauraran maganganun matan da sun yi jikoki da su da mafi yawancin zantukan ma ba fahimta suke ba ," dan haka sam basu kai ga fahimtar ma'anar kalmar BURKUTU ba ,"
Zan É—auke ku aiki amma da sharaÉ—i idan naga baza ku iya ba zan sallame ku ,"
Cikin gurbatacciyar hausar yakaka da zuwa yanzu tafi yagana zaƙuwa da son ganin sun samu aikin yi tace
Mama zamu iya kowanne irin aiki ne ki bamu zamu yi koh yagana ? Ta maida tambaÆ´ar ta ga yagana wacce bata samu zarafin magana ba illah gÆ´aÉ—a kanta da tayi alamun sun amince ,"
Meye sunayen ku sannan kuma daga ina kuke ? Ina ne unguwannin ku ? Sannan ina da dokoki na , da farko anan zaku dunga kwana koh kuwa zaku dunga zuwa ne kuna komawa kullum ?
Mu Æ´an gudun hijira ne ,
Ni sunana yakaka ,kawata kuma yagana.
Zamu dunga zuwa ne kullum ,
Toh kullum karfe tara zata yi muku anan wurin ,sannan zaku tashi karfe biyar idan masu aikin dare sun zo ,"
Suka amsa da toh ,
Sannan kuma tashi biya kuke so koh biyan karshen wata ?
Suka haÉ—a baki wurin cewa tashi biya ,"
Zan baku abincin rana kaÉ—ai zan kuma baku naira É—ari uku-uku kullum bayan kun gama min aiki ,"
Cikin tsananin murna da jin daÉ—i yakaka suke yi mata godiya kamar zasu kwanta mata ," su ai sun gama samun rufin asiri naira É—ari uku-uku a kullum me suka manta ?
Cikin murmushin ƙeta take kallon su kafin ta ce su zauna a gefe za'a zo a fara gwada musu aiyukan su ,
A gaban idon su matan nan suka haɗa wutar nan suka juye rubabbar dawar nan cikin manyan yankakkun durum ɗin suna yi suna juya ƙwanƙwaso tare da bin kiɗan kalangun nan suna rere waka, tamkar dai ƴan matasan ƴan mata ba tsoffin matan da suka doshi shekaru sittin ba ,
____
Bayan fiye da awanni uku da su yakaka suka É—auka a wurin aikin su , zuwa lokacin dattijan matan nan larki da hema sun gama gwada musu duk aiyukan da zasu dunga yi kama tun daga kan shara da goge-gogen cikin shagon da ake sayar da tsattsamar giyar burkutun ,
da har kawo yanzu da ake aunawa su yakaka burkutun da zafin ta a cikin dogayen kofunan silver suna miƙawa ga mutanen da suke ta shiga da fita cikin maye da tamɓele , mata da maza , suna kuma karbar kuɗaɗen suna kaiwa duduwa wacce take matsayin mai tara kuɗin cinikin ,
su yakaka basu kai ga fahimtar burkutu giya bace domin basu san ta ba koh sunan ta ma basu taɓa ji ba, abun da suka fahimta kawai shine wannan abun da mutanen suke zuwa saya suke sha ,yana burkita mutanen tare da sanya su shiga wani mawuyacin hali na birkicewar tunani ," ta yadda zasu ga mutum.tsaf ya shigo wurin cikin nutsuwar sa amma daga zarar ya kurɓe wannan ruwan zazzafar burkutun kafin ya bar wurin zasu ga mutum ya fara surutai da layi wasu ma har da amai da faɗuwa,"