Sashe 64
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna nan zaune gari ya waye tangarai mutane suka fara kai kawo masu sana'ar safe suka fara hada-hada gasu nan iri-iri, nan yakaka ta hango wata mai sayar da ƙosai da fanke wanda ƙamshin suyar ta ya bugi hancin yakakar , nan take ranta ya biya ,"
falmata ga masu abin karyawa sun fara mai zan karɓo mana ?
ki sayo mana duk abun da ran ki yake so yakaka !
to ki kula mana da jakar kayan mu sosai .
 Â
Toh
Ƙosai ta saya tare da fanke , ta ƙarasa wurin wata mai sayar sa koko ta sayo masu , har zata wuce ta ga mai masa nan ma ta tsaya ta saya ," tace a zuba mata yajin ƙuli ya ji sosai ," nan aka baɗe mata kan masar da yajin ƙuli,"
Nan suka zauna suka ci suka gyatse , falmata ta sha ruwa daga randar da take daura da rumfar da suke, yakaka tace ita baza ta sha ruwa yanzu ba domin tana sha amai zata yi ,
anan suka cigaba da zama suna Æ´ar hirar su jifa-jifa har zuwa tara na safe lokacin da Æ´an kasuwa suka fara fitowa ,"
mutumin da yake mamallakin shagon da suka yada zango bakin sa , shi ma ya fito ,
da kallo ya fara bin su da shi cikin shakku da rashin yadda musamman da ya ƙƴalla ido ya ga baccon kayan su ai sai ya jaa baya ,
lura da shi yakaka ta yi dan haka ta fara gaishe shi nan falmata ma ta fahimci akwai mutum a wurin ita ma ta fara miÆ™o tata gaisuwar  amma maimakon ya amsa sai ta ga ya juya ya nufi wata Æ´ar hanyar da ta ratso tsakanin shaguna ya tafi ya bar su Â
Nan yakaka ta shaa jinin jikin ta ,"
Falmata kin ga wannan mutumin ƙila nan da muke zaune shagon sa ne , kuma muna gaishe shi naga ya tafi ya bar mu " ko dai bai yadda da mu bane ? Tashi mu tafi kar ya ƙira mana hukuma a kama mu ., yakaka ta ƙarasa zancen tana miƙewa ,"
nan ita ma falmata ta miƙe ,
mu yi sauri mu tafi yakaka kar a kama mu !
Har sun fara tafiya suka ji an dakatar da su , ta hanyar daka musu tsawa tare da basu umarnin tsayawa ,"
Chak ! Suka tsaya zuciyoyim su na bugun lugude ,!
[6/24, 10:59 AM] +234 701 013 7848: Mafari .......
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
21
A tsorace suka juyo , yakaka tayi arba da wani mutum jikin sa sanye da shuɗin kaya hannun sa ɗaya rike da wata ƙatuwar kulki , gefen sa kuwa wannan mutumin da take zaton sun yi masauƙi a bakin shagon sa ne
Nan take ran ta ya aina mata , ", ya ƙira musu jami'in tsaro ne ," dan haka ta matso falmata gami da sake riƙe hannun ta ƙam-ƙam ,
Daga chan inda yake tsaye yace !
Su waye ku ?
Kuma daga ina kuke ?
Meye kuma kuke tafe da shi a baccon hannu ku ?kuyi gaggawar sanar da mu kafin naje na kira sojoji .
Mukut ! Yakaka ta haÉ—iye yawun tsoro .
Mu mune su falmata kuma mu ƴan gudun hijira ne daga ƙauyen mairambiri , kayan mu ne a cikin bacco .
  Falmata ta amsa musu cikin dakiya .
Wanne irin kayan ?
Kayan sawar mu .
  Suka haɗa baki wurin amsa masa !
Ku buÉ—e mu gani ?
filla-filla suka yi da suturun nasu , ba tare da gardama ba .
Meyasa kuke yawo da kaya ? Ina ne sansanin ku ? Bai kamata kuna yawo da jakar bacco ba saboda kun san halin da gari yake ciki ba'a yadda da duk wani mutum da aka gan shi da kaya niƙi-niƙi kuma yana nuƙu-nuƙu a cikin taron jama'a bare ma ku yara mata ga kuma irin yanayin ku , kowa ya gan ku dole zai zarge ku har ma ya tsora ta , saboda yadda mafi yawancin lokaci ake amfani da ku ta hanyar rataya muku nakiyar bam ku shiga taro ku tayar ,
Ku godewa Allah ma lokacin da na gan ku a bakin shago na ba jami'an soja ko na É—an sanda na kira ba mai gadin kasuwa ne , da ace É—aya daga cikin jimi'an tsaro ne da sai sun hukunta ku dan haka nake baku shawara da ku koma sansanin ku , ku ajiye wannan jakar kayan naku sannan idan ma zaku shigo gari harkokin ku sai ku shigo , yawon ku a haka hatsari ne ga rayuwar ku ,!
Duk wannan dogon bayanin da mutumin nan yake musu yakaka ta zurfafa cikin tunani , jin ya ambaci komawar su sansanin Æ´an gudun hijira ,"
   Cikin ran ta ta ƙudurce baza su koma sansanin su ba , saboda tun bata tare da ciki ma ƙuƙaƙƙiyar wahala ce zaman sansani ƴan gudun hijira , sanan ga tozarci uwa uba fyaɗe da ake yi wa mata , to bare fa yanzu da take ɗauke da cikin da bashi da uba , ta koma sansanin su a gan ta da ciki ,? Tace aina ta samo shi ? Alhalin duk wanda ya san ta ya san ta ne a matsayin budurwa wacce bata taɓa aure ba ,
ai ta tabbatar fanne baza ta bar ta ta kurɓi ruwa ba zagi da aibatawar da zasu dunga mata sai ya samar mata da cuta , dan haka gara sun hakura da zaman sansanin sun nemi wani wurin fakewar ,"
Da wannan tunanin ta É—ago kan ta ta dubi mutumin , da taji falmata na bashi amsa da cewa
  Sun ɓata ne sun kuma manta sunan sansanin su .
Malam dan girman Allah ka taimaka mana ka samar mana da wurin da zamu dunga kwana , " bamu da kowa a garin nan mamar mu da ƙannen mu sun ɓata tun a ƙyauyen mu baban mu ya mutu , mijina ma ba'a san inda yake ba ,"
  Ta ƙarasa zancen tana mai sunkui da kai domin gujewa kallon rashin yadda da wannan mutumin yake jifan ta da shi ," cikin ranta kuwa kunyar sabuwar ƙaryar da ta gilla take yi ,
  Saitin inda take jin tashin sautin muryar yakaka , falmata ta maida fuskar ta , cikin ran ta tana mamakin yaushe su duka suka koyi ƙarya ? ?
Shiru yayi yana nazari , kwarai zai so ya taimakawa yaran ko dan kasancewar su mata , duk da cewa cikin ran sa ba wai ya gama aminta da zantukan su bane gaba É—aya ,
toh amma shi ya san ba ƙaramar fitina zai tadawa kan sa ba muddin ya ɗauki yaran nan ya kai su gidan sa ya jefa su tsakanin matan sa uku ," yana da tabbacin sai an dafa su da ran su , shi kan sa ruwan gidan sai ya gagare shi shaa da kwanciyar hankali , dan haka da muguwar rawa gamma ƙin tashi .
Yarinya ni bani da wajen da zan kai ku , ku samu wurin kwana saboda yanzu duniya ta lalace ba'a saurin yadda da mutum . Alfarma É—aya zan muku shine na yadda duk lokacin da dare yayi muku kuna tsakanin nan bakin kasuwa ku gangaro cikin rumfa ta ku kwana bazan hana ku ba ,' har ma tabarma zan ajiye muku , bayan na sanar da masu gadin kasuwa wanzuwar ku awurin kun ji ko ?
Ya furta hakan yana danne yanayin da yake ji na rashin kyautawa yana taso masa , ya san ba haka ya kamata yayi musu ba yasan taimakon da suke nema ya wuce wannan yasan bai ji tausayin su bai kuma basu kariya ba , toh sai dai yana jin iyakacin taimakon da zai iya basu kenan ,
Ga mamakin sa godiya suka dunga sauke masa kwando-kwando tamkar wanda ya basu wurin kwana a ƙuryar gidan sa , hakan ya sa tausayin su ya sake baibaye shi ,"
  Ku dawo da jakar kayan ku ajiye cikin shago na ," kuma ku tabbatar kafin cikar karfe huɗu da rabi kun bar duk inda kuke kun dawo kun amshi kayan ku domin ni karfe huɗu da rabi nake rufe shago ,"
Cikin daÉ—in rai yakaka ta kawo falmata dai-dai wurin da take zaman barar ta ,'Â ta ajiye ta bayan sun gaisa haba-haba da É—an dattijon da yake sayar da kayan miya a gefen wajen wanda suka tarar da shi yana fidda kayan lambu É—angin su yakuwa , alehu , zogale , rama da sauran kayan lambu yana shirya su akan É—an teburin sa ga alama bai jima da isowa ba , har yake jajen kwanaki da dama baya ganin falmata ,"
  Nan suka ce hana su fitowa aka yi daga sansanin su ,"
 Â
  Falmata ga naira ɗari ki sayi wake da shinkafa da salat ki ci anjima da rana , kar ki ce zaki zauna da yunwa kin san bana so ," kuma kar ki tafi ko'ina , nima ba nisa zan yi ba zagayen kasuwar zan kewaya ko Allah zai sa na samu ko dako ne nayi na ɗan samo mana ƴan kuɗi kin ga ƙarshen kuɗin hannu na ne ɗarin da na baki , bayan ita bamu da ko sisi ki kula da kan ki sosai kin ji kou ?
Naji yakaka
ta furta hakan tana mai miƙewa tsaye daga kan ɗan dutsen da yakakar ta ajiye ta , gaban ɗan teburin mai kayan miyan ta ƙarasa
  Baba ɗan Allah ko zamu samu chanji ? Tana mai miƙa masa gudan ɗarin ,
  Ƙarɓa yayi , ya bata hansin biyu ,ta ƙarba tare da lalubar hannun yakaka ta danƙa mata gudar hansin ɗaya ,
Idan kin bani duk kuɗin ke kuma da me zaki ci abincin anjima ? Kin fini buƙatar abinci yakaka , ke da baki da lafiya ,kar kiyi aikin wahala da yawa wanda zai sa ki samu matsala , idan kin shiga matsala ni kuma yaya zan yi yakaka ? Dan Allah ki lallaɓa kan ki , kuma ki dawo da wuri ,"