Sashe 106
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A wani yammaci lubna da yakakar suna zaune kan Æ´ar darduma a tsakar gida bayan lubna ta gama koya mata karatu , suna Æ´ar hirar su kafin malama maryam ta gama Æ´an aikace-aikacen da take yi a É—akin baban su ,
  Lubna ta dubi yakaka wacce ta duƙufa tana kwafar rubutu daga jikin textbook ɗin ta ,
   Yakaka ku ƴan wanne gari ne ? Naga zane a fuskar ki , kuma hausar ki ma wata iri ?
  Ba tare da ta ɗago ba tace
 Ni ƴar maiduguri ce !
  Su maman ku da ƴan uwan ku duk suna maiduguri ne , ? Kin ce nan da antyn ki kike zaune ,
  Tsam yakaka tayi ta bar rubutun da take ,"
  Ganin shirun ta ya ɗauki lokaci ya sa malama maryam fitowa daga ɗaki da duk hirarrakin nasu daman a kunnen ta yake ,
  Lubna tashi maza ki ɗora girki , yakaka kawo textbooks ɗin ki mu fara karatu ,
  Babu kuzari tare da walwala a gare ta suka yi karatun suka gama da bata wani fahimta ba ko kusa , da malama maryam ta lura da kyau ma sai ta ga taruwar hawaye a gurbin idon yakakar lokacin da suke yin sallama zata tafi gida , bata ko jira rakiyar lubna da take raka ta kofar gida ba , tayi tafiyar ta ,
Tana fita malama maryam ta ƙira lubna ta zaunar da ita tayi mata faɗa sosai akan bincikar mutum game da abunda ya shafi rayuwar sa kai tsaye ba tare da shi wannan mutumin shi yayi ra'ayin kan sa , ya bata labari ba,
  Nan tayi ta ba wa mamar ta hakuri tace baza ta sake ba, malama maryam tace ita ba ita zata bawa hakuri ba , yakaka zata ba wa ,"
 nan tayi alƙawarin gobe idan yakaka ta zo zata bata haƙuri ,
  Tun a hanya yakaka take kuka shaɓe shaɓe da hawaye har ta ƙarasa gida , tana shiga kai tsaye ta wuce samy baby tare da ƙawayen ta da suke baje a falo suna hirar su , kowacce ta bararraje kai ba ɗankwali sai tilin izgar roba da aka yi musu kitso da shi a ka ,
 Chan lungun gado ta samu ta Zauna gami da haɗa kan ta da jikin gadon ta fashe da kuka me fidda sauti , kukan tausayin rayuwar da ta bari a baya , kukan ƙewa da famuwar ciwon da ke binne a ƙasan ran ta , kukan tunowa da iyayen ta , ƴan uwan ta ,garin ta , asalin ta , kukan rashin kowa na ta da tayi ,
   Yaks kukan me kike haka ? Cewa nake yanzu lokacin kuka ya wuce a wajen ki ? Ashe har yanzu baki san cewa kuka baya maganin kome ba ? Baya sawa bare ya hana ?
  Ko kuwa wani abun malamar ta ki tayi miki yanzu na je na ci mata mutunci ? Ki min magana mana ?
  Idanun ta jazur ta ɗago kai , anty samy na tuno da su mama , baba , falmata da baby mama , bani da kowa anty samy , ni bani da kowa !
  Da wata irin murya mai ɗauke da tausayi , samy baby tace ,
  Kina da ni yaks , ni zan cike miki gurbin su , har zuwa lokacin da zaki koma musu ,
  Wasu sabbin hawaye ne suka zubowa yakaka ,
  Falmata fa ? Waye zai zama madadi na a wajen ta ? Falmata bata da kowa ita ma idan gidan su rahima suka gaji suka kore ta ina zata je ita da baby mama ? Anty samy ina son komawa na zo da su ,!
 Â
  Babu wanda zai kore su a gidan su doctor , doctor da baban sa mutanen kirki ne , ki kwantar da hankalin ki , ba yanzu bane lokacin da ya kamata ki ɗauki nawin su lokacin na nan zuwa kin ji ko ?
  Naji anty samy ,
Yauwa ko ke fa ? Yakaka matar Yarima ta furta hakan tana juyawa ga barin É—akin ,
 Da wani irin kallo yakaka ta bita ,
  Yarima
 Ta maimaita !
****
Kwanakin kammaluwar aikin Biyamuradi Youssouf Tare da komawa ƙasar sa suna sake kusantowa , aiki yana sake zafafa a gare su , inda cikin ƙasa da wata ɗaya aka samu asarar fiye da sojoji hamsin cikin rundunar sa , wanda hakan ko kusa ba abu ne mai dadi ba wajen su da ma gwamnatin ƙasar su baki ɗaya , duk kuwa da cewa aikin soja daman ya gaji haka , sadauƙarwa ne a bakin rayukan su ,
Dan haka duk yadda ya so ya samu damar zuwa sake ganin ɗiyar sa abu ya gagara dole ya haƙure har zuwa nan da kwanaki goma da wa'adin su yake ƙarewa ,
Baby mama sai girma take tana daɗa wayo , har ta wuce kwanaki arba'in tana neman cika watanni biyu , kome ƙin ka da jariri idan ka ga baby mama sai ta burge ka , ka ji kana son ɗaukar ta , idan kuwa ka ɗauke ta ji zaka yi ina ma a baka ita , ina ma ƴar ka ce ? Yarinya ce mai tsananin ruwan kyau bayan kyaun kan sa da take da shi , ƴar bul-bul da ita fara tas gwanin sha'awa madarar jariran da ake bata ta karbe ta ba'a ce jaririyar da ta barranta da shan nonon uwa bace ba ,
Bugu da ƙari kulawa da lelen da Falmata take yi mata domin duk da kasancewar falmata makauniya , tsafta yana daga halittar ta ce , dan haka ko yaya ta ji wani yanayi da bai gamsar da ita ba a tare da baby mama , take zata tuɓe ta ta goge mata jiki da wiper , ko ruwan ɗumi da tawul ta sauya mata diaper da kaya , bayan wanka sau biyu da hajja mai wurya take mata safe da yamma ," dan haka koyaushe baby mama cikin ƙamshi take da wankakkun kaya tsaf-tsaf ,
So da ƙaunar baby mama a bayan kowacce daƙiƙa sake ninkuwa yake cikin ran falmata , ta ɗauki duk wani so ƙauna da tausayi na duk wasu mutanen da ta taɓa so a rayuwar ta rashin su ya sa ta juye su akan ƴar jaririyar , tamkar ran ta aka taɓa haka take ji idan tace 'uhun' da sautin kuka ,
bata taɓa gajiyawa da hidimar baby mama , ta kan manta da yunwar cikin ta ko ƙishirwa idan ta shagaltu cikin tarairayar ta , son baby mama haɗe yake da bugun zuciyar falmata !
Waƙoƙi iri iri take rera mata da ƴar daddaɗar muryar ta cikin yaren su , sai kuwa ƴar jaririyar tayi luf , ƙulus a kwance tana kallon fuskar falmata da tunda ta fara kallon abubuwa ta himmantu gurin tsare fuskar falmatan da idanun ta a duk lokacin da take farke , ga alama bada jimawa ba zata haddace kamannin ta tare da ɗaukar yanayin ɗumin jikin ta , ta kuma gane warin jikin uwar goyon ta da ta buɗi ido tun ranar farko ta gan ta a matsayin UWA a gare ta ,"
******
Duk abunda aka sanyawa lokaci aka zana iyakar sa to fa babu shakka zai zo ya wuce tamkar da ɗai ba'a taɓa fara farkon sa ba ,
Yau shabiyu ga watan goma sha biyu ita tazo dai-dai da ranar kammaluwar aikin tawagar rundunar sojojin niger da suka kawo tallafi wurin yakar Æ´an tawayen Boko Haram zuwa cikin yankin nigeria ta kan boda inda yankunan biyu suka haÉ—u na niger da nigeria ,
ƙarƙashin jagorancin Colonel Youssouf Abdul-Azizou Baskore , a kuma yau gwamnatin ƙasar su ta bada umarnin su fara janyewa daga filin daga inda waɗanda aka turo su maye gurbin su zasu samu isowa bakin dagar a yau , ' dan haka baki ɗayan sojojin gurin idan ka dubi fuskokin su a yalwace suke da fara'a , inda dayawa daga cikin su suke ta ihu da wasanni a tsakiyar dajin domin bayyana murnar su a fili kan komawar da zasu yi ƙasar su cikin dangi da iyalan su , bayan kwashe fiye da tsawan watanni goma sha biyu da suka yi cikin daji ,
Colonel Youssouf ya bi jerin ƴan uwan sa soji wajen bayyana farin cikin sa bisa ga wannan nasarar da suka samu na tsallake hare-haren ƴan tawayen boko haram ɗin da suka sha far musu , da kuma nasarorin da suka samu wajen fatattakar ƴan tawayen boko haram ɗin ta hanyar kashe wasu tare da kama wasu da dama , hakan a gare su babban nasara ne da dukkanin su suke sanya samun ƙarin girman matsayi daga gwamnatin ƙasar su ,
Gefe guda kuma zuciyar sa cike taf da murnar sake ganin É—iyar sa da zai yi a yau , sosai ya zaÆ™u yake kuma É—ora idanun sa akan fuskar ta , dan haka duk wani abunda yake cikin Æ™uzari da karsashi yake yin sa ,Â
Sha biyun rana tawagar sojin da zasu karbi aiki suka iso ba tare da É—aukar dogon lokaci ba bayan musayar gaisuwa da wasu bayanai na sirri irin na tsaro da ya shiga tsakanin manyan sojojin gurin da zasu tafi da sabbin da zasu maye gurbin su ,
Motocin da suka kawo sabbin sojin suka fara juyawa da tawagar masu komawa inda zasu ajiye su a babban barikin garin maiduguri zuwa gobe da zasu wuce ƙasar su ta jirgi da zai tashi ta abuja !
Biyamuradi Youssouf bai jira rana tayi sanyi ba , da isar su barikin maiduguri , wanka kawai yayi ya sauya kayan sa daga uniform É—in soji ,
ÆŠaya daga cikin direbobin su ya ja sa zuwa unguwar da Æ´ar sa take ,
Ƙarfe ɗaya na rana ta gota suka isa gidan nan ya tadda prof tare da wasu baƙin sa ,dan haka ya jira su har suka gama ganawa sannan ya shiga falon ,