Sashe 75
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannan a daren na yau yana so ƙwarai ya je yaga mahaifitar sa a unguwar da tayi bigire,'
Duk yadda za'a yi dai goben zai samu ya saya musu kayan fitar bikin ko da ready made ne saboda lokacin yin ɗinki ya ƙure ," da wannan tunanin ya ƙarasa shigewa sashin sa ,'
Su yakaka a cike suka tarad da falon duk kuwa da girman sa ,"yaran mata ne masu aure da marasa aure birjik a falon su da Æ´aÆ´an su ,kowacce tana wace wance ," kaf É—in su dangin juna ne , saboda ta bangaren mahaifin su manyan gida ne kuma shahararrun masu kuÉ—i kaf garin ansa kakan su wanda ya haifi baban su ,'
Kamar jiran shigowar su hafsa take wacce take tsaye suna magana da wata ƙawar su ," tace
  Yauwa yakaka dan Allah ɗauki Mopper nan ki goge duk illahirin cikin falon nan saboda akwai ruwa-ruwa kar a tattaka a faɗi ,"
 Cikin juriya yakaka ta amsa
  toh anti hafsa ,
Tas ta goge faffaÉ—an tiles É—in ta É—auraye mopper ta ajiye , ta dawo inda ta bar falmata a tsaye ,daga bakin kofa ,
 Falmata zo muje ki gani na gano mana wurin kwana ,"
Wata Æ´ar siririyar hanya ta kai su da take bangaren hagu na falon da wata Æ´ar kofa É—aya jal ta karfe , ta tsakanin karafunan kofar yakaka ta hango step É—in bene , da yayi sama wanda a duk zaman ta a gidan kusan watanni biyu bata san cewa akwai bene ba ta cikin falon ,"
Kinga sai muyi kwanciyar mu anan tunda babu kowa , koh ?
********
Daidai da rana guda bai taɓa mantawa da ƙanƙanuwar yarinyar da ya lalatawa rayuwa ba , kullum sake ganin laifin kan sa yake a duk lokacin da yayi hasashen irin halin da ya bar ta da wanda a yanzu zata iya kasancewa a ciki ya kan shiga zullumin da yake kai ga hana shi walwala ,,
Yayi nadama marar iyaka da ta sa har yau yana laluben neman sanin haƙiƙanin abunda ya same shi a wancen lokacin da har ya aikata abunda ko a mafarkin sa bai taɓa nuna masa shi youssouf zai aikata ba ,' idan akwai abunda yake bashi mamaki da sanya shi hamdala bai wuce wucewar wannan lamarin ko kuwa yace warkewar ciwon da ya kai shi ga aikata mummunan aikin ba , tun daga ranar da ya bar ta bai sake jin son kasancewa da wata mace a irin wannan yanayin ba , ya koma youssouf ɗin sa da ya san kan sa ,"
Ko ruwan burkutu yanzu ba sosai ya cika neman ta ba , sai jifa jifa jarabar sa da burkutun ya ragu da kusan kaso shidda cikin goma , kuma a lokuta da dama ko giyar company ma ya samu ya ɗan kurɓa yana jin kwaɗayin sa da barasar ya kau ,
Bulayin neman abunda zai sa shi ya goge laifin sa ko kuwa ya gyara barnan da yayi a wurin yarinyar , ya sanya shi É—aukar tsawon lokaci bai sake waiwayar ta ba duk da cewa sau da dama a farkon rabuwar su ya sha ganin kiran ta ta layin da ya saya mata , kafin daga baya ya daina ganin kiran ,
 Ya shiga damuwa da har ya sashi fara neman layin nata sai dai amsa guda yake samu kullum daga computer shine wayar tata a kashe take ," meya same ta ? Wane hali take ciki ? Wacce irin rayuwa take yi ?? Bai sani ba !
Zuwa lokacin da ya samar da abun da yake ganin zai taimaka mishi gurin gyaro ɓarnar da yayi , kuma sai yanayin aiki ya tsaida shi ,tare da sake yin nisa da inda take , amma ya ƙudurce ba zai bar kasar ba har sai ya gyaro barnar da yayi ta hanyar da shi yake ganin ya dace ,"
Dan haka da yanzu ya samu damar da zai iya fita daga wajen aikin ya taka zuwa cikin garin da take , domin a jiya da suka yi waya da tafeeda ya sanar da shi cewa ya shigo ƙasar nigeria a halin yanzu yana abuja , '
biyamuradin ya tabbatar masa da cewa zai halarci wurin É—aurin auren , aina za'a yi bikin É—aurin auren ? Amsar da ya bashi faÉ—uwa ce ta zo dai-dai da zama domin ya tabbatar masa da auran a jahar borno za'a É—aura shi cikin birnin na maiduguri ,"
shikenan ma ba sai na zo har abuja ba , zan tsumaye ku cikin birnin maiduguri domun ai cikin garin nai bigire ," amsar da youssouf ya bawa tafeeda kenan !
Washegari , tun sassafe aka kaɗa kan su yakaka zuwa wurin aiki , ba'a ko bar su sun karya ba , sune shara wanke-wanke goge-goge basu nan basu chan , sai misalin sha ɗayan rana aikin ya dan tsahirta musu , suka shigo gidan suna rarrakaɓewa saboda kallon hadarin kaji da ake bin su da shi ,
Wanka suke so suyi su sauya kaya domin rabon su da wanka tun shekaran jiya , amma ko da suka shiga ɗakin da yake a zaman nasu , kawayen zainab da suke ta faman harƙƴallar su a ɗakin wasu na wanka wasu na karin kumallo koro su suka yi basu ko saurari zantukan da suke da nufin faɗi ba ,
haka suka fito jiki a sanyaye suka dawo bakin kofa suka rakaɓe ,"
Suna nan tsaye ya danno kan sa cikin sashin , yayi wankan sa fes cikin wani brown ɗin yadi mai shara-shara , sosai kayan suka ƙarbi kalar fatar jikin sa mai ɗan haske kaɗan ,
Akan su ya fara É—ora ido ,"
Me kuke anan fatima ?
Ya na gan ku haka wani iri ?
Anyi muku wani abu ne ?
Kun kuwa ci abinci ?
Ƙwallar da tuntuni take taruwa a idanun falmata suka tsiyayo ," lokacin da take saita idanun ta a sashin da ta ji tashin muryar sa
Mun ci abinci yaya dakta , kuma ba'a mana kome ba , cikin ne babu wurin zama sosai shiyasa muke tsaye anan 'yakaka ta amsa masa ,
Wanne irin babu wurin zama ?ba ga ɗakin ku ba ku shiga ciki kuyi zaman ku mana ko kun fi son zaman parlour ne??
Wannan Karon falmata ce tayi karaf ta amsa
  Ai ƙawayen auntie zainab sun cika ɗakin , korar mu ma suka yi da muka shiga muna son muyi wanka mu chanja kayan mu ," ta furta hakan tana turo ɗan ƙaramin bakin ta bayan ta kumbura kumatu ,"irin su da ɗakin su ɗin nan," ( su falmata samun sarari tusar asuba )
 Da kallon nazari yake bin su , yana ƙoƙarin boye ɓacin ran sa a gaban su kan abunda aka musu ,
To wai ya na gan ku kun yi datti haka ,? Ba dai aiki kika je kina ta faman yi ba a wannan yanayin da kike ciki ?
  Tun jiya muke aiki yaya dakta yanzu ma muka gama na safe , cewar falmata , irin su a dole ga garkuwar su ,( ja'ira falmata an samu wuri )
GabaÉ—aya bacin ran da yake ji ya bayyana saman fuskar sa , wanne irin aiki zasu sa Æ´ar mutane da ciki ?
Har ya taka da nufin shiga gidan sai kuma ya jaa ya tsaya ,
  Ina rahima ?
Ya tambaye su ,"
Cikin rashin jin daÉ—in yadda falmata ta bayyana masa laifin Æ´an uwan sa , yakaka ta amsa a sanyaye
Tun jiya ban gan ta ba yaya !
Baice kome ba ya zaro wayar sa daga aljihu ya shiga neman layin rahima ,"
Bugu É—aya ta É—auka
Hello big bro ina kwana ?
Rahima kina ina kizo yanzu ina kofar sashin ku ,"
  Toh ," ta amsa
Ba'a cika mintuna huÉ—u ba sai ga ta ta fito daga cikin gidan ,"
  Gani big bro ," ta furta hakan tana mai washewa yakaka haƙora gami da kashe ido ɗaya irin na shakiyanci ,"
  Ki je da su ɗakin su suyi wanka su shirya ku zo tare ke da su ," ya bata umarni fuskar sa babu alamun wasa ,"
  Toh ta amsa tana mamakin ɗakin nasu kuma zata raka su ? Kai big bro yana ji da baƙin nan nasa anya anya anya kuwa ," tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yace ,"
  Kice ga duk wanda ya nemi hana su yin abun da nace , umarnina ne a bar su suyi wanka su shirya ," nan ta fahimci akwai abunda ya faru ƙila hana su wanka aka yi , to wa ya hana su ?
  Tana shiga ɗakin ta samu amsar tambayar ta domin suna sanyo kafa cikin ɗakin sofi wacce take rangaɗa kwalliya tace ,"
   Kai kai ku koma , wai meye kuke mana sintiri kalen ku baɗa mana ƙwarƙwata ?? Daga kun zo wuri sai kun sauya kalan ƙanshin sa ,"cikin ran ta tana ji haka kawai ta tsani yaran ," ( karfin hali )
Da hannu biyu rahima ta dafe bakin ta kafin ta ce
    lalala anty sofi baƙin big bro ne fa kuma ma daƙin su ne ," yanzu ma shi yace na rako su suyi wanka su chanja kayan su ,"
    Baƙin ƴan gudun hijira ko dai bakin doctor ?
  Wallahi baƙin sa ne shi ya kawo su ,"
Yakaka ku shiga kuyi wanka , ba kowa a bathroom É—in ko ? Ta furta hakan tare da É—an kwankwasa kofar banÉ—akin ,"
Â
Falmata shiga ki fara yi ta furta hakan tana mai kaucewa mugun kallon da sofi take watsa musu ,"
  Wata purple and black ɗin atamfa yakaka ta cirowa falmata daga cikin kayan su , sabuwa ce dal falmatan bata ko taɓa sawa ba , ta miƙa mata banɗakin lokacin da tace ta gama wanka , ita kuma ta fiddo wani pink colour ɗin yadi ɗinkin doguwar riga ta riƙe a hannun ta ,