← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 222 OF 269

Sashe 222

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Soyayyar da ta tarar waɗannan ma'auratan na yi ya taɓa ranta , kewar sa da take ta dannewa kuma ta bijiro mata , baki ɗaya a lokacin , "Falmata meyasa kike kuka ? Kin san fa damuwa zata iya sa ki samu ciwo a halin da kike ciki .

Shiru tayi bata amsa ba , kamar yadda hawayen ta ya ƙi tsayawa , a dai-dai lokacin zuciyar ta tayi rauni wajen riƙe ciwon da yake damunta a rai ta hana shi bayyanuwa.

" Kiyi haƙuri zai zo ku tafi ,yana son ki dayawa Falmata inshaAllah a gidan ki za ki haihu .

" bai taɓa ƙiran mu ba tunda muka zo fa Yakaka , watakila ma ya sake ni bansani ba ni tausayin abunda yake ciki na nake yi ban..

" Youssouf ba zai taɓa sakin auren ki ba ya furta hakan da bakin sa kuma a aikace ma ya nuna ki kwantar da hankalin ki kiyi ta addu'a kin ji ko ?

GyaÉ—a kai tayi tana share hawayen ta dai-dai da dawowar Amne da ta shiga cikin asibitin yin dubiya , damuwar da take damunta ta É—an ragu .

Da layi yazo kan ta ita kaÉ—a ta shiga , su ka gaisa da likitar mace ce , ta yi mata duk wasu tambayoyin da aune-aunen da suka dace , bata da matsalar kome dan haka magungunan da yakamata masu ciki su dunga sha kawai ta rubuta mata .

Rashin ji daga Youssouf ba Falmata kaɗai yake damu ba , har Khaalty Rahima , Amnee da Prof da kan shi , rashin jin wani bayani ko da na ƙiran waya ne daga Youssoufa ya sa su a tunanin makomar auren sa da Falmata ?

Sau biyu Prof da Amnee suna tattaunawa a tattaunawar su ta ƙarshe prof ya yanke shawarar kan cewa idan har Falmata ta cika watanni biyu a gida , zai tashi ɗan aike zuwa masarautar Maradi dan sanin halin da Youssouf yake ciki da kuma makomar auren 'yar su , saboda rana ɗaiɗaiku ne bai ƙiran layin wayar Youssouf ɗin amma bai tafiya , ya zama dole yayi wani abu akai a matsayin sa na waliyyin auren kuma a yanzu shi matsayin Uba yake a wajen ta .

Falmata taso a bar ta ta dunga bin Yakaka Islamiyar da ko bayan auren ta da Doctor Hamza bata daina zuwa ba .

Da farko Prof ya ƙi yarda domin yace babu iznin Mijinta , tayi zamanta kawai a gida sai dai yadda a kwana biyun take yawan zaman shiru damuwar ta kamar ƙaruwa tayi tun bayan zuwanta awu , har 'yar rama tayi gaba ɗaya bata walwala .

daga Yakaka ta tafi islamiyyar da take kusan yini a can dan ƙarfe tara na safe take tafiya sai huɗu da rabi na yamma suke tashi kafin ta iso gida biyar saura .

Shikenan Falmata sai ta zama shiru a ɗaki ita ɗaya ƙwal, tun Khaalty Rahima na nunawa Amnee kar ta damu kan ta indai Falmata ce daman tun asali ita ba mai yawan son shiga jama'a bace kamar Baban ta take marar son hayaniya

Har ita da kan ta Khaalty Rahima ta fara damuwar saboda sai ta yini a É—aki abinci ma da kyar take fitowa ta ci , Hajja ce daman mai shiga É—akin ta dame ta har sai ta fito da ita , ita kuma wannan satin duk tana wajen danginta ana biki bata zauna ba .

Dan haka sai Amnee ta sake yiwa Prof maganar shiga islamiyyar Falmata ta sake masa ƙorafin zaman kaɗaicin da Falmatan take yawan yi kar ya sa mata ciwo .
Prof yace " zai duba lamarin .

Ranar asabat da safe kafin lokacin tafiyar Yakaka makaranta , Amnee ta shiga ɗakin su Yakaka hannun ta riƙe da baƙar leda da kaya a ciki ,

" Yakaka har kin fara shiri ne ?
Amnee ta tambaya tana ɗora ganin ta kan Yakaka wacce take sanya safa a ƙafar ta , da sauri ta ɗago fuskar ta da murmushi tace " Eh Amnee sannu da shigowa ,
" Yauwa sannu takwara ta furta hakan tana sauƙe ganin ta akan Falmata da take kwance akan gado ta basu baya ,

Ledar hannun ta ta ajiye a bakin gadon , kafin tace " Fatima tashi ki shirya yau dai ke ma za ki fara zuwa islamiyyar , tun kwanaki biyu na sake yiwa Baa Alaji zancen kin ga ashe an miki register ga Uniform É—in ki ma da litattafan ki duk kin samu sai tafiya makaranta kawai ..

Falmata wacce tunda Amnee ta fara bayani ta tashi zaune tana murmushin da ta zarce da dariya jin ƙarshen bayanin Amnee da sauri ta sauƙa daga gadon tana cewa ," Amnee nagode , nagode Allah ya saka da Alheri ki yiwa Baa godiya , inason islmiyya sosai wallahi .

Ta ƙarasa zancen da nufar banɗaki domin watsa ruwa , Yakaka da Amnee suka bi bayanta da kallo fuskokin su ɗauke da murmushi .

Sosai fara zuwa makarantar ta ya rage mata damuwa domin kuwa yini suke karatu bata samun damar zurfafa tunani ,

Yau da ƙafa ma suka taho daga makarantar da yake tazarar tsakani ba mai yawa sosai bace Falmata tace, "Yakaka nafi jin daɗin makarantar nan fiye da Ecole ɗin mu ta Niamey wallahi ,

"Meyasa ko kin fi gane karatun nan ?

" A ah saboda a can ko na tafi ecole tunanin Mama baya bari na gane karatun sosai , Allah sarki Mama ta kusa watanni biyu da rasuwa amma koyaushe ji nake kamar É—azu ta bar ni .

Murmushi Yakaka tayi , "ke da Mama ƙauna ku mai girma ce ai, nima naso Allah ya bani damar yin rayuwa tare da ita ko da ba mai yawa bane da nima na samu ladar jinyar ta da sanadin haka Allah zai bani lada mai yawa .

" da kuma za ki so ta dayawa fiye da son da kike mata domin Mama 'yar baiwa ce a cikin yara sa'o'in ta wayon ta daban ne kaifin hankalin ta yafi na shekarun ta .

Murmushin Yakaka tayi tana jin kewar 'yar ta na zagaya jinin ta , kewa kuwa mai tarin yawa ,

Ajiyar zuciya Falmata tayi daga nan ta shiga ba wa Yakaka labarin wayo da iyayin Mama wanda daman kusan rana É—aiÉ—aiku ne da ba ta bata wasu labarai da suka shafi Mama .

Tun a harabar gidan suka fahimci akwai baƙi a gidan saboda baƙin motoci da suka gani har uku ,
"yau baƙi ne a gidan ko su waye ?
Yakaka ta furta hakan tana bin motocin wajen da kallo , can daga ƙasan ran ta tana fatan Doctor hamza baya cikin su .

" To Allah yasa baƙin alkhairi ne ,
Falmata ta furta hakan lokacin da suke nufar ciki

Tun kafin su shiga falon ƙamshin da ya karaɗe illahirin harabar wajen yake basu tabbacin baƙin na girma ne .

Da Sallama suka shiga falon , idanun su akan hamshaƙan mata huɗu da suke kan kujerun falon sai kuma Amnee da take a tsakanin su fuskar ta fal fara'a .

Ɗan taƙaitattcen kallo Falmata ta yi musu da taimakon gilashin idanun ta ta shaida fuskar Ammi , yayar Biyamuraɗi Youssouf , fuskar ta na nan zane a zuciyar ta kamar yadda munanan kalmomin da suka jefa musu yake rubuce tsaf a cikin kwakwalwar ta ,

Dan haka sai taƙi tsayawa kamar yadda Yakaka ta tsugunna gaishe su ,duk kuwa da cewa ita ma ta gane Ammi ,

sai ita ta ratsa ta bayan kujerun falon tayi hanyar É—akin su .

Yadda tayi sam bai yiwa Amnee daÉ—i ba , dan haka ta É—an É—aga sauti tace " Fatima zo nan , zo ku gaisa da surukan ki mana ko baki gane su bane ? Yanzu suka iso .

Jaa tayi ta tsaya kafin ta waigo cikin rashin kuzari ta dawo baya kaɗan ta yi durƙuso daga nesa tace " Ina wunin ku ?
" Kadaran-kadahan Ammi ta amsa ,"da lafiya lau , tana janye ganin ta daga kan ta

Asma'u wacce tun shigowar su take faran-faran cike da kissa tace " tashi tashi ƙamna ta durƙuso ba naki ne ba , ɗaga yayar ki daga durƙusso Mairama .

Da sauri Aisha Mairama ta miƙe fuskar ta ɗauke da faffaɗan murmushin ganin Falmata , kafin ta ƙaraso Falmata ta miƙe akan ƙafafun ta guntun murmushi ta yiwa Aisha bata tsaya ba tayi juyawar ta ba tare da ta yadda ta sake duban kowa ba ta nufi ɗaki .

" Mama kar ki tafi ki barni ki jirayeni Mama , nan ina ne muka zo Mama ?

Chak ta tsaya a bakin ƙofar ɗakin zuciyar ta na sauya bugu wannan muryar ta Mama ce , Mama ce take ƙiran ta , da kitsima hakan cikin ranta ta juyo da sauri laɓɓan bakin ta na ƙiran Mama .

Idanun ta suka sauƙa kan 'yar yarinyar da bata kai Mama a girma da wayo ba sai tsantsar kamanni da take yi da Mama , tana kokawar riƙe hannun Mamar ta da suke sauƙowa tare daga ƙafar benen a tare Khaalty Rahima na bin su a baya ,

"Yumna
Ta ƙira sunan ta da ƙaramin sautin da bai hana Yumna ta jiyo ta ba , a hankali ta ɗora ganin ta kan ta tana wara manyan idanun ta masu cike da wayo , sai ta sake matsawa jikin mamar ta tana riƙe hannun ta da kyau lokaci guda ta haɗa da maƙale kafaɗa .

" Yumna ki je wajen Mamar ki tana ƙiran ki , Siyama ta furta hakan tana ƙoƙarin zare hannun ta daga cikin na Yumma ,
Chapter 222 · 0% Book details