← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 269

Sashe 119

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Soja garin nan na ku kuwa ya karɓe ka , ka ga yadda kayi fes da kai kana ƙyallin fuska sai ka ce sabon ango ? Ah lalle miyar umma da zaƙi ta sa kayi shar da kai duk wannan hautsinewar sojin sun kau , ke Fatima kin kuwa gaishe da maigidan naki ??

Na gaishe shi hajja ,

To ban ga kin kawo masa ruwa ba , ?

Zata miƙe ya dakatar da ita ƙyale ta hajja ita da take da larura baza ta iya aike ba !

Ƴar dariya hajja tayi

Zata iya Babban soja ai matar ta ka ba dama akwai lura da kaifin ƙwaƙwalwa saurin gane waje ne da ita , ka ga dai ba mu rufa wata guda ba a gidan nan amma ta haddace kusan muhallin kome da kome da yake cikin gidan nan ,

ita da kan ta take zuwa ta É—au ruwa a firiza ko ta je kitchen ta haÉ—a madarar mama , kullum addu'a nake mata Allah shi kawo mata waraka .

ÆŠan murmushi yayi yana duban falmata wacce ta koma ta zauna ta juyar da kan ta gefe ,

Kalaman hajja sun tuno masa da abunda ya so mantawa , watau kai falmata asibiti tare da samar mata gurbin karatu ,

Ya zama dole yayi duk wani abunda zai iya yi gurin kyautata rayuwar falmata ko domin ya samu girman laifin sa ya ragu a wajen Allah .

Hajja ku shirya zamou tafi babban hospitalisé a duba lafiyar idanun fatima yanzu. !

   To to yanzu kuwa , falmata tashi ki shirya bari nima na ɗan kintsa , !

Niamey national hospitalisé nan suka je , inda basu wani ɗau dogon lokaci ba suka ga ƙwararren  ophthalmologist , bayan haske-hasken da tarin tambayoyin da yayi mata akan idanun nata , a ɗakin gwaje-gwaje .

Suka dawo ofishin sa inda youssouf ke jiran su , bayani ya soma yi masa daki-daki

A sakamakon binciken da nayi a zahiri ban hango wata cuta ba a idanun nata sai dai raunin ƙwayar idanun nata watau ainahin jijiyoyin idanun suna da rauni , a tambayoyin da nayi mata nayi ƙoƙarin sanin tayaya ta fara samun rashin gani ko da shi aka haife ta ?  amma sai ta shaida min bata da masaniya akan mafarin samuwar rashin gsnin ta ,

A takaice cikin binciken da muka gudanar da kuma sakamakon amsoshin da ta bayar yayin yi mata gwaji da akwai yiyuwar dawowar wani kaso daga cikin ganin ta idan har za'a samu ƙwararrun kayayyakin aikin da zasu taimaka wajen dawo da ganin nata ,

Sai dai a halin yanzu bamu da waɗannan kayayyakin a nan gida niger da sauran ƙasashe masu tasowa , sai a manyan ƙasashen duniya da suka yi fice wajen samun ingantattun asibitoci masu isasssun kayayyakin aiki tare da ƙwararrun likitoci ,

Dan haka a yanzu abunda zamu iya yi mata kaɗai shine zamu bata magungunan da zasu iya taimakawa wajen bada kariya ga idanun nata daga kamuwa da wasu cututtukan da zasu iya kassara sauran ƙarfin jijiyar idanun da kuma hana idanun yin ciwo ƙaiƙayi da zubar ruwa ,
   Da fatan kun fahimce ni ?

Mun fahimta Doctor mun goude zamu dawou gare ka idan buƙatar neman taimakou game da asibitin da ya kamata a kai ta a wata ƙasar ya tasou mun goude ƙwarai Madallah .

Washegarin ranar Biyamuradi bai zauna ba , ya shiga binciken makarantar makafi me kyau da yake son ya kai falmata ta fara karatu kafin lokacin da zai sake yunƙuri me ƙarfi akan lafiyar idanun nata a karo na biyu .

Association Nationale Pour la promotion des aveuglés , nan ne inda ya ji gamsuwar sa akan ya kai falmata nan ta fara ɗaukar darasi , wacce jibiya ce ta koyar da makafi tare da basu tallafi me tushe daga ƙasar amurka , da ta tanadi ƙwararrun malaman makafi ,

Cikin sati guda yayi mata rajista da duk wasu abubuwan da ya kamata , ya samar mata da direba bayan ya sa an kawo masa ɗaya daga cikin motocin sa da suke maradi ya danƙa makullin ga hajja wacce take cike da farin cikin wannan cigaba da falmata zata samu a rayuwa .

Ranar da zai bar garin zuwa bakin aikin sa jahar dosso , ya yi musu sayayyar kayan abinci da abubuwan da zasu iya buƙata tare da ƴar ƙaramar waya me sauƙin amfani ya ba wa hajja bayan ya zuba mata lambobin sa a wayar ya adana ta su a ta shi wayar ,

Suna zaune a falo yana musu sallama akan yau zai koma bakin aikin sa , sai kuma zuwan ƙarshen wani watan zai komo

Godiya me tarin yawa hajja ta yi masa ,
    Ya amsa tare da waiwayawa sashin falmata da take ta faman lila mama akan ɗan lilon ta wanda baban ta ya sayo mata su tarkacen kayan wasan yara iri-iri har da wanda ya fi ƙarfin shekarun ta , tun daga kan lilon yara , kekunan koyon zama har zuwa ƴar mota ta yara da ƙananun kayan wasanni irin na ƴaƴan gata na sosai  , bayan suturun da ya daɗa jibgo mata.

   Fatima baki da wata matsala kou ?

Shiru tayi tana É—an lila mama a hankali ,

  Falmata hala kin samu kurunta ? Kina jin Babban soja na magana kin yi shiru ? Uhum yau ni naga abunda ya shallake tunani na ,

     Babu kome kawai ina son unmh

    Uhum ina jin ki me kike so ??

A kaini makaranta

  Ai na sanya ki makaranta fatima sati me kamawa zaki fara zouwa ,!

Na islamiya ? Ina so a cigaba da koya min karatun addini ma ,!

Toh babu damouwa idan Allah ya yarda zan bincika a samu me koyar da ke na Islama ma ,

Akwai wata damouwa bayan wannan ?

Daman ka gaya musu zan dunga zuwa da mama makarantar ko ?

Babu inda zaki dunga goyon ta kina tafiya da ita anan waje na zaki dunga barin ta idan ya so kafin ki dawo na sauya ta , ko kuwa na gudu da ita,  kina nufin baza ki maida hankali kan karatun naki bane ? Zaki dunga ɗaukar ta kina zuwa da ita makaranta ki ɓige da raino memakon karatu ni ke meyasa ana nuna miki hanya kina daɗa bauɗewa ne ??

Ɓata rai tayi ta ɗauke kai

Murmushi youssouf yayi , shi dai rigimar hajja da falmata na ba shi dariya 

Duba fatima ki bar mama a wajen hajja har ki tai école ki dawo Kin ji kou ?  Ba'a tafiya da yara école.

Shiru tayi idanun ta na kawo ƙwalla ita dai bata ƙaunar abunda zai raba ta da mama ko na ƴan mintoci ne bare fa makaranta da awanni zata yi a can , kai anya zata iya , ?

To hajja mu dunga zuwa tare da ke mana makarantar ? Sai ki dunga riƙe min mama nayi karatun na fito ?

Ke raba ni da wannan gudun birin , gotai gotai da ni zani makarantar ? Yaushe rabon duniya da ayyaraye ?  Babu inda za ni ke kaɗai zaki tafi makarantar ki ki dawo ki same ni ina nan , ilmin ai shine Babban gatan ki falmata kin ji ko ?

Naji hajja

Yauwa mutuniyar ai shiyasa nake son ki akwai ki da saurin fahimta ,

Sallama suka yi da youssouf yana sake yiwa hajja godiya me tarin yawa tare da ɗanka mata ƴan kuɗaɗe wanda da kyar hajjan ta yadda ta karɓa sai da yayi ta roƙon ta da Allah  .

Daga nan Dosso yayiwa tsinke bai jin marmarin zuwa maraɗi duk da cewa fiye da kaso talatin na ɓacin ran sa game da sha'anin sa da gimbiya maimouna ya kau , domin har sun yi waya ma cikin kwanaki biyun .

  

Assalamu Alaikum kowa da kowa !

Da fatan kuna lafiya ?

Ina neman afuwar ku bisa jinkirin zuwan wannan shafin , hakan ya faru ne sakamakon tafiya da ni zuwa gida , ban samu zama ba ziyarar dangi da sauran Al'amuran yau da kullum .

Da fatan zaku cigaba da haƙuri da tsaikon da ake samu cikin ajizanci irin na ɗan Adam ?

Nagode

   
[9/3, 10:14 PM] +234 806 122 1116: Fikrah writers association

MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

32

Bayan Shekaru Biyar

Lokaci baya jira sai dai a jira shi , ba'a masa shamaƙi a yayin wucewar sa , Lokaci gudu ne da shi fiye da saurin  bugun zuciyar ɗan adam ,

Lokaci yayi juyi ya juya ya zo da sauyi ta mabanbantan fuskoki a rayuwar mutane a cikin tsawon shakaru biyar .

Yakaka tana ɗaya daga cikin mutanen da suka samu sauyi ta fuska me kyau tare da tarin nasarori daki-daki cikin rayuwar ta , wanda a yau ta kawo matakin kammala makarantar ta secondry wacce ta rayu tsawon shekaru biyar tana faɗi tashin neman ilmi a cikin ta , da jajircewar ta tare da nuna ƙwazo ya sa aka ɗaga ta aka mata tsallaken aji na shekara guda daga jss3 zuwa ss2.

Da hakan ya kawo kammaluwar karatun nata cikin shekaru biyar kachal .

Ta fito da sakamako mafi kyau da ya sanyata farin ciki ita da duk wasu makusantan ta musamma malama maryam da lubna waÉ—anda da jajircewar su cikin taimakon yakaka a harkar ilmin ta har ta kawo wannan matsayin .

Samy baby ma wacce ta tashi daga matsayin samy baby ta koma ,Hajiya samira ,"  ita ma ta taya yakaka farin cikin kammala karatun ta wanda duk wasu kuɗaɗen hidindimun karatun daga farkon sa har ƙarshen sa ya fito ne daga aljihun Alhaji Gali da har kawo yau suke liƙe a naniƙe da juna , bata da wata maraba da matar sa , kai har ma ta zarta matar sa ta aure iko da shi tare da samun kuɗaɗen hannun sa , Alhalin kuwa har yau da suke samun wajen shekaru takwas tare sun gaza yin aure ."illar bariki kenan ,!
Chapter 119 · 0% Book details