← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 269

Sashe 160

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Yakaka ta idar da sallah tayi addu'o'in da ta saba yi duk bayan sallar ta ,

Ta waiga ga Rahima wacce ta farka daga bacci

"Rahima yaya ciwon kan naki ? Kin ji sauƙi ko ?

" Ya É—an sake ni Yakaka thanks ,

"Yakaka yawan ibadar ki na burgeni ga yawan addu'o'i da kike yi kin fa kusa mintoci ishirin kina addu'a , Yakaka me kike roƙa haka mai yawa ? Ko dai har da shi ake yiwa addu'ar ,

Ta ƙarasa zancen tana ƴar dariya tare da kashe idonta ɗaya na ɗabi'a .

ÆŠan zaro ido Yakaka tayi sai kuma tayi murmushi ,

"Rahima , Bawa baza'a tambaye shi me yake nema a wajen Ubangijin sa ba , Duk abunda nake roƙa bai wuce neman gafara da samun Rahamar Ubangiji ba gare ni da iyayena da 'yan uwa na ,

  Jim tayi kafin ta cigaba da cewa ,

,"Ummin mu , Rashin sanin a wanne hali mamana take tsakanin Rayuwa da mutuwa yana matuƙar tayar min da hankali Rahima , kullum roƙon Allah nake ya ƙaddara haɗuwar fuskokin mu , idan kuma ita ma ta rasu kamar Baban mu , ina tsawaita musu addu'ar samun gafara a wajen Allah .

Hawayen da ya tsatsafo a idonta ta goge cikin ranta ciwo take ji na rashin iyayen ta .

Cikin tausayawa Rahima tace ,

"kiyi Haƙuri Yakaka , babu shakka abune mai ciwo naka ya ɓata har gara ma ace mutuwa yayi kaga gawar sa aka yi jana'iza aka binne , kowa ma jiran mutuwa yake ,

" Muma akwai Auntie na takwarata ce sunanta aka sa min , ita ma ɓata tayi tun ma kafin a haife ni ,

"Amne tana bani labari lokacin tana da ciki na ,  Khaalty Rahima ta bar gida tana yarinyar ta yadda Amne ke bani labari bata ma kai mu shekaru a yanzu ba  ,

" tundaga lokacin Rayuwar gidan mu bata sake zama dai-dai ba , duk da bansan Ƙhaalty Rahima ba amma labarin kirkin ta da yadda Amne ke ƙaunar ta yasa nima ina sonta sosai , ina kuma so ta dawo wataƙila rayuwar gidanmu ma ta dawo mai daɗi , "

Cike da jimami da tausayi Yakaka tace ,

   " Allah sarki Khaalty Rahima Allah ya bayyana ki daga yau zan dunga saka ta cikin addu'o'i na .

  " Nagode Yakaka , duk ranar da muka je gidan Amne tare zan sa ta nuna miki hoton Khaalty Rahima .

Cikin zumuÉ—i Yakaka tace
"  yaushe zamu je Rahima ? Ina so naje na gaishe da Amne .

"Weekend ( ƙarshen sati ) insha Allah .

" Allah ya kaimu ,

Rochester New York City

Tafe Biyamuradi Youssouf yake akan titin 3rd Ave, jikin sa sanye da kayan sanyi daga ƙafa zuwa kansa da ya ɗora hular da take da laɓɓa biyu da suka rufe masa kunnuwa elmer fudd da aka fi ƙiranta da Trapper hat   .

Hannun sa ɗaya riƙe da 'yar jakar takarda da ya sayo ( Hot chocolate ) mai dauke da tambari tare da sunan kamfanin chocolate and Vines a jiki , domin su ɗumama cikin su ɗumin hot chocolate ya ratsa musu gaɓɓai kafin su fita zuwa cikin asibiti nan da awa ɗaya mai zuwa ,

Cikin kwanaki biyar da suka biyo bayan zuwan su ƙasar Amurka zuwa ganawar su da likita da duk wasu bayanai da suka samu game da Cutar dake tare da Mama .

Daga Biyamuradi Youssouf har Falmata sun rasa karsashi da nishaɗin su , musamman Falmata wacce tundaga wannan ranar take cikin damuwa da tunanin hanyar da zata iya bi domin ganin ta samar da abunda zai zama sanadi na samun warakar cutar Mama da sanyin ƙasar tare da sauyin ruwa suka haɗu suka sa ta ɗan fara kukan ciwo ,

Sai dai kasancewar nan Amurka ba kamar ƙasashen Africa da basu cigaba bane ta fuskar kula da lafiyar ɗan Adam .

Cikin ƙanƙanin lokaci a rana ɗaya aka bata magunguna tare da duk wani taimakon da ya dace a ƙarshe likitan ya gargaɗe su akan kiyayeta daga wannan sanyin mai tsanani , dan haka ciwon bai tsananta ba ya lafa  .

Kwanaki biyu Biyamuradi yayi yana tsara abunda ya dace na daga sabon kuÉ—irin sa , da tunda ya samu gamsassun bayanai daga bakin likitan Mama ,

Ya dangana da nema mata lafiya a yanzu domin babu damar yi mata dashen ɓargo ko juyen jini da zai iya bata waraka , dole zasu cigaba da haƙuri tare da kula da ita , tana shan magungunan ta har zuwa wasu shekaru nan gaba da za'a samu wani cikin 'yan'uwan ta da zai isa sadauƙar mata da ɓargon sa .

  Tun a washegarin ranar ya koma asibiti ɗauke da sabon ƙudirin sa bayan dogon nazari tare da kai komo a ƙarshe zuciyar sa ta amince ya haƙiƙance cewa zai kai Falmata ga Manyan likitocin ido dake Mayo clinic su duba ta , idan tana da rabon gani shi zai yi iyakar ƙoƙarin sa wajen biyan kuɗaɗen da za'a buƙata domin yi mata aiki zuwa kan magunguna domin  samun warakar ta .

Babu shakka Falmata ta cancanci duk wata kulawar sa duba da yadda take nuna ƙauna ta haƙiƙa ga gudan jinin sa da yake da tabbacin ko mahaifiyar Mama baza ta so ta sama da son da Falmata take yi mata ba ,

Sannan akwai wani abu da shi yake ji game da Fatima da ya kasa fasaltawa a zuciyar sa sai dai yana yawan sakawa a ransa cewa saboda irin kulawar da take yiwa 'yarsa ne.

Bayan haka Halin mutum yana zama tsani wajen samarwa da mutum Alkairi ko akasin sa ,

halayen Fatima mafi yawansu masu kyau ne , ƙwari yake yabawa da Yakanah tare da Nagartar dake gare ta .

   ****

Yau ne Alƙawarin sa da Sabon likitan da zai Fara duba Falmata wacce bata kai ga sanin ƙudirin sa ba , domin bai kai ga sanar da ita ba .

Kasancewar ƙarfe uku na yamma shine lokacin da zasu ga likitan hakan ya sa shi fita sayo musu hot chocolate Su sha kafin fitar su domin zai taimaka wajen rage musu jin matsanancin sanyi .

Da Sallama ya tura 'yar ƙofar ya shiga inda ya tarar da su a zaune yadda ya fita ya bar su , da ɗan gudu Mama ta taho gurin sa

",Bienvenue Papa, que m'as-tu apporté?  (sannu da zouwa Papa me ka kawo min ?)

Rungumar ta yayi suka ƙarasa kan doguwar kujerar da Falmata ke zaune fuskar ta ɗauke da siririn murmushi ,

", Sannu da dawowa Baban Mama ,
  "Sannu da hutawa Maman Mama , yace da sigar zolaya yana kallon fuskar ta
  
  Hot Chocolate ɗin ya ciro musu gami da sanya 'yan chokula ya sakawa  Falmata nata a hannu,

Ya ɗauki Mama ya ɗora a cinyar sa ya shiga bata a baki tana kurɓa a hankali

Shiru ne ya biyo baya ,

ɗumin shayin da aka yi shi da garin koko ( cocoa ) da damammiyar  Madara mai zafi yana ratsa sassan jikin su daɗin sa kuma yana basu nishaɗi , da yasa Falmata bata farga da tayi shan haɗama ba sai da ta ji 'yar robar hannun ta sakayau , ta kai chokalin baki , taji bata ɗebo kome ba .

Biyamuradi Youssouf wanda duk idanun sa ke kan ta ya ga irin shan da tayiwa chakulan É—in, ya kai hannu a hankali ya zare robar daga hannun ta tare da musanya mata da nashi wanda bai kai ga fara sha ba ,

", Fatima bois ça aussi ( ki sha wannan ma )

  " Baban Mama na ƙoshi fa , nagode .

   Ta furta hakan tana jin kunya na taso mata ,

Murmushi mai sauti yayi , ganin yadda gefen bakin ta ya ɓaci ,

ya kai hannun sa kusa da fuskar ta , hannun sa na sauƙa a jikinta ta jaa baya da sauri tare da ajiye robar hannun ta ,

   "Dakata Fatima , repérer zan ɗagga miki daga fuskar ki ,

    Babban ɗan yatsan sa ya kai gami da goge mata gefen bakinta inda hot chocolate ɗin ya sauƙa bata sani ba .

Kanta a ƙasa tace
  "Nagode .

bai amsa ba illa É—ibar chakulan É—in da yayi ya kai bakin ta ,

  " amshi lait au chocolat chaud ,

buɗe bakin ta tayi cike da kunya ta karɓa ,

"zan iya sha da kaina .

tace masa muryarta can ƙasa ,

yayi kamar bai ji ta ba ,  tare da cigaba da bata a lokaci guda shima yana sha , bata sha dayawa ba tace da shi ta ƙoshi ,

cikin nishaɗi ya shanye sauran , yana ƙurewa fuskar ta kallo da take sumul babu ɗigon ƙwalliya ,

Bayan sun gama , yace mata

  "Fatima zamou fita zouwa hospitalisé ku shirya yanzou ,

  " Baban Mama zamu sake ganin wani likita daban ko ? Wannan bai ƙware ba sosai ya zai ce cutar Mama bata warkewa bace ? akwai ciwon da bashi da magani ne ?

  da wani irin yanayi yake dubanta yadda take maganar cike da son samun warakar Mama ya taɓa ransa , ita bata da wani sauran buri ne a rayuwa da ya wuce lafiya tare da walwalar Mama ? Bata yiwa kanta wani shiri ko tanadi ? Bata da wani buri ne na gina tata rayuwar ?

" Doctorat gasskiya ya faɗi Fatima , cutar Mama batta maganin waraka a yanzou sai fa kou ɗaya bissa hanyoyin da ya faɗi da kouma babu dama a yanzou , ba bissa lafiyar Mama zamou tafi hospitalisé ba ,

Shiru tayi ranta babu daɗi , yaya zai ce babu hanyar samun warakar Mama , shi baya irin tunanin da ita take yi ne  ? Meyasa bazai yi wani yunƙuri ba domin taimakawa gurin samar da yadda zasu yi su tsaretar da Mama daga wannan ciwon me azabtarwa , ?
Chapter 160 · 0% Book details