← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 269

Sashe 139

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motar da take tahowa daga bayan su sannu a hankali saboda ruwan sama  da ya kwanta bisa kan kwaltar , wacce ta fito daga layin gidan su yakaka ,ita ce ta matsa musu hon ,

Su biyun suka haÉ—a ido , yakaka ta janye hannun lubna , da nufin ko Suna bisa hanya ne sun matsa daga hanyar ,

Maza biyu ne a cikin motar wanda kallo guda za'a musu a gane cewa ba ƙananun samari bane , mazaje ne waɗanda suke kan ganiyar shekarun su na 40 cif , wayewa tare da gogewar da ta bayyana kan ta a jikin su ita take nuni da tarin ilmin da yake jibge a ƙwanyar su , ɗaya yana mazaunin direba yayin da ɗayan yake daga gefen sa ,

Na gefen ya kai hannu a karo na biyu da nufin sake danna hon , na gefen nasa ya tare hannun nasa ,

  Suleiman meye hakan kake kuma ?
Yace yana kai kallon sa gare shi ,

   Dan Allah abokina yi parking ka bani mintuna biyu zan fita ,

  Bai ce masa ƙala ba saboda yanayin sa da bai tare da nishaɗi ya sa baya buƙatar doguwar magana , ya gangara daga gefe ya tsayar da motar ,

Da sauri suleiman ya fice daga motar ,

A hankali yayi musu sallama cikin nutsuwar da take halittar sa tun ƙuruciya ,

Tana jin muryar sa ta gane shi , shine dai maƙalemata manne matan da ya liƙe mata tsawon shekaru uku yana bibiyar ta ba tare da ta taɓa saurarar sa ba ,

Matsa hannun lubna da yake cikin nata tayi , ta mata alama da kar ta kula sa , sai dai irin nutsuwa tare da kamala da ƙwarjini na musamman da lubna ta hango a gare shi ya sa ta fahimci ba irin sa ne mazan da mata ke gwatsalewa ba dan haka taƙi amfani da umarnin yakaka ta ja ta tsaya tare da amsa sallamar sa 

Baiwar Allah naji daɗi da ki ka tsaya kika amsa sallama ta domin nasan da ta ƙawar ki ce baza ku tsaya ba , dan kuwa tsawon shekaru kusan uku kenan ina bibiyar ta amma bata taɓa tsayawa ta saurare ni ba,

  Da sauri lubna ta kai kallon ta ga yakaka wacce ta yi gaba kaɗan ta tsaya tare da ɗauke kai daga barin kallon su .

Dan Allah kayi hakuri,

tace da shi , girman sa na sake cika mata idanu

Babu kome duba da cewa a yanzu bisa titi muke ba darajar mu bace yin magana anan dan haka ki sanar da ni adireshin da zan same ki ko kuma number ta wayar ki saboda ina son yin magana da ke game da ƙawar ki idan kin bani dama ,

Da sauri lubna ta ba shi number wayar ta , tana jin farin ciki na ratsa ta , a karon farko yau wani namiji ya nuna yana da ra'ayi akan yakaka , namijin ma gangariya irin wannan ai kuwa yau ummi na da farin labari .

Bayan ya karɓi number yayi mata sallama ya juya wajen motar su , da ƴar dariya a fuskar sa ya dubi abokin sa da hankalin sa ke gefe guda da alama yayi zurfi cikin tunani .

Abokina ka taya ni murna ga alamu na sanya ƙafa a kasancewa mijin mata biyu , ramla ta kusan samun abokiyar zama , tsawon shekara uku da nake bin yarinyar nan tana yin biris da ni , sai yau nayi sa'ar haɗuwa da ƙawar ta ga alamu ita zata min tsani na samun ta , 

na rasa me yake fusgata akan ta alhalin sau biyu kawai na taɓa ganin fuskar ta ,

Da alama akwai rabo ne a tsakanin mu me ƙarfi ,

A hankali ya tada motar ba tare da ya bada muhimmanci a zancen nasa ba ,

To ai sai ka ɗau harama , takaicin matan duniya ne bai ishe ka ba , ko kuwa ma nace har yau baka san wacece mace ba da irin tarin abubuwan ƙi da yake tare da ita da ace ka sani da baza ka yi sha'awar ajiye su har su biyu kamar kayan ado a gidan ka ba ,

Wuce su suka yi a hankali ,

Lokacin da suleiman ke bashi amsa

Hamza kenan kai dai na rasa wanne irin tabo mace tayi maka a duniya kake musu irin wannan kuɗin goro , duk kuwa da yadda safiyya take tarairayar ka tare da lelen ka kamar wani jariri sabon haihuwa , bana jin ta taɓa saɓa maka a rayuwar zaman auren ku .

Ya ƙarasa zancen tare da dariyar shaƙiyanci .

Murmushin takaici doctor hamza yayi ,

   Baza ka taɓa ganewa ba suleiman !

Ya maida ganin ga madubin  motar sa , yana hango ta ta jikin madubin ƙwarai tafiyar ta ta ɗau hankalin sa , mace ɗaya ya taɓa gani da salon takun nan , wacce bai ko son giftawar tunanin ta cikin ran sa sai fa yau da ya sake ganin wata wacce fuskar ta take a rufe  Bai kai ga ganin kamannin ta ba .

Yakaka ashe daman irin zaman da kike da ni kenan ??
  Cewar lubna idanun ta na bayyana ɓacin rai ,

A kaikaice yakaka ta dube ta , kin ga sahiba bana ciki da rigima , daga kawai mutum ...

  Hmm
  Lubna ta katse ta ,

Wallahi sahiba abu É—aya zan faÉ—a miki a matsayin ki na wacce na É—auka Æ´ar uwa ,

Kar ki yadda kiyi wasa da damar da ta zo miki , idan har wannan mutumin da gaske yake ki bashi dama ku fahimci juna , aka yi bincike bashi da wani aibu wallahi ki bada dama kuyi auren ku shekarun mu sun fara tafiya ishirin da biyu mun rufa ta da uku muke hari ,wallahi wasa ba namu bane dama kuma sau É—aya take zuwa a rayuwa ,

  Shiru yakaka tayi

Kalmar ,"Dama," na maimaituwa a cikin kan ta , ita har tana da wata dama da ta rage mata kuwa ? Ai damar guda ɗaya da take da ita ta riga ta zo ta wuce tun a shekarun baya , " damar da mahaluki ɗaya ya bata wanda ta tabbatar baza ta taɓa samun  makamancin sa ba, bata yi amfani da damar ba a maimakon haka ma sai tayi masa mummunan sakamo da har yau idan ta tuno shi kunya tare da nadama basa ƙasa a guiwa wajen danne ta ,

ina ma ina ma ina ma ?? Da ace dama zata dawo mata ? Da ace zai sake ba ta dama ko da gutsire daga irin damar da ya bata a baya ? Wataƙila da ta gyara kuskuren ta ta wata fuskar ,

, abunda ta sani shi ɗin ya riga ya mata nisa ita ta zama wata shuɗaɗɗɗan lamari da ya taɓa giftawa cikin rayuwar sa ,

Bata da wani shauƙi ko tunani mai armashi akan wani ɗa namiji har yau ta gaza sake son wani ɗa namiji , " zata iya cewa ta ƙi maza ," ƙi irin na wanda kunama ta taɓa harbin sa babu shakka idan ya ga gizo-gizo kakkaɓe shi yake , dangantakar nesa nesa ce ke tsakanin ta da maza ,

shiyasa har yau ta gaza samun saurayi ɗaya tak , ita ce bata saurarar su bata bada fuska , take boye kan ta tare da killace surar ta daidai da fuskar ta a rufe take , ta zaɓi hakan , ta kuma fi son tayi tsarayuwar ta a haka ba tare da wani ɗa namiji ya sake ratsa rayuwar ta , burin ta ɗaya ne shine tayi ilmi kuma tana godiya ga Allah tana godewa malama maryam tare da addu'ar Allah saka da alkhairi ga baki ɗayan zuri'ar ta ,

Ko da ko kusa bata sahun malumma amma kai tsaye a yau ta wuce a ƙira ta da jahila , ta nemi ilmi tana kan nema kuma zata cigaba da nema har.....

   Har suka kawo gida bata cewa lubna ƙala ba ,

   Sai da suka shigo gidan ta ruga da ɗan gudun ta ta rungume malama maryam wacce take tsaye daga ƙofar kitchen tana amsa sallamar su .

  Ni bazan yi aure ba har sai nayi ilmi na zama kamar ummi malama ta , sai ki san yadda zaki yi da mutumin da kika ba wa phone number .

Murmushi ummi tayi ,
   Anya kuwa yakaka ? Aure ai shine cikar darajar ɗiya mace

Lubna wacce take zama akan kujera ta shiga bada labari tiryan tiryan tana yi tana hararar yakaka wacce take yanka musu cabbage da zasu ci abincin rana da shi .

Sosai malama maryam ta yiwa yakaka faɗa daga ƙarshe ta ƙarƙare da yi mata nasiha tare da faɗa mata fa'idojin aure da girman matsayin sa a addini .

Jikin yakaka yayi sanyi har idanun ta na tara ƙwalla , ta gaza cin abinci na kirki .

A ƙarshe ta jaa kunnen ta akan daga yau kar ta ƙara ƙin saurarar duk wani namijin da yake da kamala da ya nuna yana son ta , ta ƙoƙarta ta saurare shi na ɗan wani lokaci ta fahimci wanene shi , daga nan idan ta yarda da halayen sa na ƙwarai ta bashi dama ita ma tayi aure , ko kusa kar ta kawo aƙidar ƙin aure kusa da ran ta saboda wani shuɗaɗɗan dalili nata , .

A ladabce ta amsa mata da zata yi yadda ta faÉ—a mata .

Bata wani jima ba saboda yadda walwalar ta tayi ƙaura ta musu sallama tana barin gidan ƙarƙashin rakiyar lubna wacce duk ta damu da rashin walwalar ƙawar ta ta , sai faman jan ta da hirar raha take ,

Har ƙofar gida ta rako ta ,

Zata tura ƙofar gidan ta shige lubna ta riƙo hannun ta , ta waiwayo tana kallon ta da sakakkiyar fuska .

Sahiba idan baƙya son sa idan ya ƙira insha Allah zan faɗa masa dan Allah ki bar damuwa .

Murmushi yakaka tayi ,
   Ni dai ban ce miki ba , kawai ....shiru tayi ,
    Baza ki gane ba sahiba .
Chapter 139 · 0% Book details