← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 219 OF 269

Sashe 219

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma ace sanadin son zuciya irin na Hajiya Mama duk ta rusa mata farin-cikin ta a lokaci guda ? Gani take kamar Hajiya Umma da sauran Æ´an uwan ta duk zasu tsane ta akan laifin Mahaifiyar ta da É—an uwanta , a tsakanin hakan take yawaita tambayar kanta anya kuwa tayi sa'ar uwa ???

An cigaba da tsare Gimbiya Maimounatou tare da Mammadou a Niamey , saboda rashin sanin halin da Youssoufa ke ciki ya hana a tura su ga kotu ,

kawo yanzu kuwa Mammadou iyakar nadama ya yita , ko abincin da ake ɗan kawo masa , baya iya ci duk ya lalace yayi duhu , bai taɓa zaton akwai wani lokaci da zai zo yayi danasanin zazzafar ƙiyayyar da yake yiwa ɗan uwan sa ba irin wannan lokacin da ya sarƙe cikin sharrin Gimbiya Maimounatou da ta tsaya kai da fata kan shi ya kawo mata gubar da ta ciyar da Youssouf da a zahiri ba gaskiya bane ba shi ya kawo mata ba ,ba shi kuma da wata masaniya akan haƙiƙanin me ya faru ga Youssouf a wannan daren , iyakar abunda ya sani shine yaje gidan Youssouf mintoci kaɗan bayan ƙiran sa da tayi saboda kusancin da yake tsakanin gidajen nasu biyu da wuri ya isa , ƙarƙashin jagorancin gnala da ta tare shi tun a babbar ƙofar gidan ya cimma har falon da Youssouf ke yashe a ƙasa cikin halin fitar hayyaci , a lokacin shi da kansa ya shiga ruɗani ganin halin da ɗan uwansa ke ciki , a ɗimauce ya shiga tambayar gimbiya Maimounatou

" Ya mutu ne ?
Da gaske Youssoufa ya cimma kushewa tai ?

Bai gama tantance da abunda ke faruwa ba lokacin da suka tsinkayo jiniyar 'yan sanda ,

Kallon-kallo aka yi tsakanin su ukun , da ruÉ—ani ya bayyana a fuskokin su sannan da wani irin sauti Gimbiya Maimounatou tace ,

" Mammadou ka shigo da ha'inci cikin lamarin mu amma kayi kuskure ka kuma yi shuka a idanun maƙwarwa , muddin kuwa baka yi wani yunƙuri ba tarkon da kayi na iy afkawa har da kai da makusantan ka ,

Cikin ruÉ—ewa yace ,

"ki bar surutan banza ki faɗi wanne tanadi kika yi kafin ki aikata wannan aikin domin nayi gaugawar shafe girman laifin ki kafin lokaci ya ƙure miki , ko kin manta Yarima ɗiyan sarki kin ka kashe ?

Kafin yin wani yunƙuri mai girma jami'an tsaron da bai kai ga tantance kakin soji ne a jikin su ko kuwa na 'yan sanda ba , suka dunga tururuwar shigowa falon kafin ya farga sun cika falon , bai shaida fuskar ko ɗayan su ba , sai fa Tafeeda da shi kuma tun shigowar sa ya rufu ga Youssoufa bakin sa ɗauke da sallalami gami da addu'o'i .

Hanjin cikin sa ya kaɗa lokacin da ya lura jami'an tsaron wajen riƙe suke da bindigogin su da suke ɗane a saitin su shi da gimbiya Maimounatou , tsoro mai girma ya ziyarce shi lokacin da ya farga da tsaka mai wuyar da yake ciki , da dukkanin alamun da suka bayyana ya taka sawun ɓarawo .

masaniyar sa ɗaya shine yasan gimbiya maimounatou tana da mummunar manufar kashe Youssouf tun shekarun baya da ta taɓa furta musu hakan shi da Hajiya Mama lokacin da suka yi wata ganawa ta sirri da su da ita wanda a lokacin suka haɗa hannu wajen ganin sun kai Youssouf ɗin ƙasa da shi da Hajiya Mama ba burin su kashe shi ba , ( kashe shi abune wanda ba sa hangowa kansu hanya mai ɓillewa ta nan ) kwaɗayin su tozarta shi suke irin tozartuwar da zata kai shi ga rasa damar sa ta hawa ƙaragar mulki burin su ya bar nahiyar su yayi nesa da sarauta , yayi rayuwa mai cike da baƙin-ciki tare da rashin nasara to ko'ina Mulkin Maradi ya zama na Mammadou .

Ga rashin sa'ar su sai ta ritsa da su munafunci shi ai daman dodo ne ubangidansa yake cinyewa , Mammadou ba shi da wata kafar kufcewa daga zargin da yake ciki , Maimonatou kaÉ—ai ita ce ke iya fidda shi ita kuwa bata shirya hakan ba ,

kafin a raba musu ɗakin da ake tsaron su cikin a cikin sa , babu irin roƙo da magiyar da bai mata ba kan ta tausaya ta faɗi gaskiya , amma tayi funfurus sai yaɓa masa baƙaƙen kalmomi masu cike da raini take yi wanda a lokacin shi basu ishe shi sauraro ba bare yayi hanƙoro akai , nadamar son zuciyar da ya aikata cikin kowanne sa'a guda na sake yi masa dabaibayi .

Gimbiya Maimounatou kuwa ? Zuwa yanzu lamura sun fara zuwa saɓanin tunanin ta , dan kuwa har kawo yau da take cika satika uku , sau ɗaya bata ji daga wani nata ba wanda kuma tana da masaniyar tuntuni labari ya je musu , to yaya haka ta kasance mata ? Tana sane ko kowa ya iya kauda idanunsa daga gareta sakamakon laifin da ta riga ta aikata , Abban ta ba zai iya ba , saboda sanin da tayi tauraruwar ta ta ɗara ta kowa haskawa a zuciyar Mahaifin su sumfurin ƙaunar ta kuma mai banbanci ce da ta sauran ƴaƴa , duk kuwa da kasancewar ta ɗiya mace ,

Tun tana sanya ran za'a buɗo kofa ace ta zo ga Maimartaba mahaifinta yazo ganinta da kansa ,tare da Mahaifiyar ta , daga nan ta san zasu nemi belin ta tana da tabbacin za'a basu idan yaso daga baya sun haɗu a kotu su da mutanen Youssoufa da take jin ba wani nisa shari'ar zata yi ba za'a kawo ƙarshen ta sanin da tayi tasu masarautar ai tafi ta su Youssoufa ƙarfi har ma da dukiya .

shiru ya tsawaita babu wani motsi daga iyayen ta .

ta sassauko burin ace ko da wani daga cikin tarun yayyunta maza da mafi yawa basu wani cika shiri da ita ba musamman waɗanda suke yan uba , amma duk da haka tana harin ko uku daga cikin ne su zo ko da kuwa ace zasu ƙare mata zagi, ita dai ta yadda su zo su ƙarbi belin ta .

Har ta kai cikin ƴan kwanakin nan ta fara burin ina ma da ace ko da wani babba daga cikin masarautar su ne ya zo ganin ta ? ko da ace bai nemi belin ta ba ya jishe ta labari na daga abunda ke faruwa ga iyayen ta da ma masarautar su baki ɗaya da yasa suka yi watsi da ita a cikin wannan maƙasƙancin wajen da yafi dacewa da wajen hora maƙasƙanta daga cikin bayun ta .

Jita-jita ya kasance gaskiya domin kuwa a daren ranar Maimartaba sarkin Maradi tare da Hajiya Umma suka dawo cikin masarauta .

Da dawowar su bai fi da awa guda ba labarin samun lafiyar Biyamuradi ya kewaye masarautar , inda ake da tabbacin farfaɗowar sa daga magagin ciwo sai dai an yi masa aikin da yasa zai ɗan sake yin wasu kwanaki a can ƙasar India kafin ya warke baki ɗaya ya dawo .

Tamkar rana haka masarautar ta ɗauki murna har da ƴan bushe-bushen algaitu na bayyana jin daɗin samuwar lafiya ga Biyamuradin Maraɗawa wanda tamkar hatsarin rasa shi da aka shiga ne ya wanke duk wasu laifukan sa na baya da ake ganin sa da shi tare da haɓɓako da ƙaunar sa a zuciyoyin Al'umma .

ruwan ƙiyayyar kuma da ganin aibun sai yayi tsallen alkafira ya wanke Hajiya Mama tare da Mammadou , ta ukun su Maimounatou babu wasu abun aibatawa da ya wuce su lungu da saƙo na birnin na maradi murnar dawowar Maimartaba ake tare da farin-cikin jin cewa Yarima yana samun sauƙi .

Siyama wacce tunda Hajiya Umma ta shigo sashin nata da daman ita ma tun bayan faruwar lamarin ta baro ɓangaren gidan su ta dawo ɗakin ta da yake sashin uwar riƙon ta ,

Ita ta bi bayan Hajiya Umma har zuwa ƙuryar ɗakin ta ta kuma shiga Hidimar abincin Hajiya Umma , tana sauraron duk wasu amsa waya da Hajiya Umma ke yi da 'ya'yan ta da sauran jama'ar ta , da duk dai batu ne kan samuwar lafiyar Youssoufa , cikin wayar ne ta ji Hajiya Umma na lissafa sunayen waɗanda zasu tafi India domin cigaba da zama da Youssoufa na ƴan wasu satika kaɗan nan gaba , ƙannen sa maza biyu kawai ta lissafa bata ji sunan ta a cikin masu tafiyar ba.

amma duk da haka zuciyar ta cike take da farin-cikin jin lafiya ta fara inganta ga Mijinta , bayan irin tashin hankali tare da fargabar rasa shi da ta shiga da har ta kai ta ga kwanciya rashin lafiyar sati guda sai da ta fara samun labarin samun sauƙi a gare shi sannan ita ma ta fara gyagijewa .

Bayan ta kammala haɗawa Hajiya Umma abincin a can ɗakin ta na ƙurya inda ba wani mai shigar sa cikin bayu sai fa su 'ya'yan ta da kuma makusanta na sosai , fitowa tayi daga ɗakin ta dawo ɗan madaidaicin falon da yake tsakanin ɗakin da sauran manyan faluka ta zauna .

Hajiya Umma bayan ta idar da sallah ta ɗan taba abincin sama-sama , sai ta ɗaga waya ta ƙira Siyama , nan take kuwa ta shigo tana rike da hannun Yumna , wacce da shigar su ɗakin ta saki hannun mahaifiyar ta tayi wajen kakar ta da gudu ta faɗa mata akan ƙafafu ,

Da ƴar dariya Hajiya umma ta ɗago ta tana cewa , " ke zainaba ki ɗagga ni kadda ki ƙarasa min ƙafafu ki sa ni ɗingishi dagga dawowa ta daman yaya lafiyar ƙafar ?
Birgima yumna ta sake yi akan ƙafar Hajiya Umma kafin cikin 'yar muryarta mai cike da wayo tace ' Umma na faɗi miki ni suna na ba Zainaba ba suna na Yumna ko Mamaa ?

Da murmushi Siyama ta ɗan yi gurfano daga gefe tana ƙoƙarin janye Yumna daga kan Hajiya Umma tace , " Yumna bakya jin magana ko idan baki ɗagga Umma ba gobe ban tahiya dake unguwa .
Chapter 219 · 0% Book details