Sashe 32
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasan kun gaji , nasan kun min uxuri ,nasan kun tsumaye ni , nasan ya kamata na baku yafi haka , toh amma yanayi ne ya zo da haka ,ina fatan zaku ƙara hakuri , kuyi fata daga yau babu sauran dogon jira , wanda nima nake fatan haka .
Inaso mu shawarta zaku dunga hakurin ganin posting sau É—aya koh biyu a sati amma da dogon jadawali mai É—auke da kimanin kalmomi dubu takwas zuwa tara / koh kuwa zaku fi son gajeran jadawali a kullum ,mai É—auke da kimanin kalmomi dubu É—aya zuwa biyu ? ???
Ina jiran ra'ayoyin ku , yadda kuke so haka za'a yi insha Allah
  Â
#son so
#fikrh
#umm'muaz
[6/24, 10:57 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association.
MAFARI .........
( Hargitsin Rayuwa. )....
umm'muaz
13
Tuki Hamza yake cikin rashin kuzari wanda ba domin kan titin shal yake babu kowa ba a sakamakon gudun da kowa yayi , da tabbas babu abunda zai hana ya samu tukuicin zagi daga wurin sauran direbobi saboda sam ya gaza yin sauri , zuciyar sa taƙi aminta da ya tafi ya bar ta cikin halin da take ciki , wani sashi na zuciyar na son sanin me ma ya kai ta wannan unguwar wacce take cike da hatsari .?
Gangarawa yayi gefen titin ya tsaya dai-dai lokacin da tunanin abun da zai iya samun ta marar kyau idan har dare yayi mata a wannan unguwar ya gitta masa , da hakan ya sa ba shiri ya karya kan motar ya juya batare da la'akarin ba akan hannun da yakamata ya juya bane .
Wannan shine karo na biyar da take safaa-da-marwaa a bakin babban titin tana mai kwalla kiran sunan falmata , wanda zuwa yanzu da ta kawo tsakiyar hanyar ta ji juya ya fara kwasar ta a sakamakon muguwar yunwa da kishirwa gami da tsantsar sanyin da yake ratsa bargo da kasusuwan ta ta jikin jiƙaƙkun kayan ta da iska ta fara busar da su ,
Ba shiri ta dira guwowin ta duk biyu a ƙasa tare da sake fashewa da wani matsanancin kukan da baya fitowa sosai a sakamakon kwalla kiran da take ya fara dusar da karfin muryar ta .
Kuka take bilhakki tana kiran sunan falmatan a hankali cikin ƙaramar murya ,"
Falmata nyi dan3? ( falmata kina ina ?)
Falmata nyi dan3? ( falmata kina ina ?)
Allahgammama falmata are3 nyi baa maa range3 kindaa dikkin3 baa ," (Dan Allah falmata ki dawo idan babu ke bazan iya rayuwa ba )
Ƙarasa bajewa tayi daɓas a cikin guntun ruwan da yake wajen idanun ta na fara ganin bibbiyu ,
Daf da ita ta bayan ta ya zo yayi birki , kallon ta yayi ya É—auke kai gami da matsa mata hon ,
Taji ƙarar motar sarai a daf da ita amma bata yi wani alamu na motsawa ba hasalima wani ɗan guntun tunani ne ya gifta mata na ina ma da motar nan zata take ta ta mutu ita ma kamar yadda mahaifin su ya mutu take kuma hasashen mahaifiyar su da sauran kannen ta ciki har da mafi soyuwa a gareta "falmata" duk sun riga sun mutu sun bar ta ," tunanin hakan da tayi ya sa ta sake muskuɗawa ta matsa kan titi sosai yadda zata bawa motar da ta taho damar bi ta kan ta ,"
Wani dogon tsaki ya saki ganin yadda ta rarrafo ta hau kan titi a maimakon ta taso ta zo su tafi kamar yadda yake nufi ,
Balle murfin motar yayi ya fito laɓɓan bakin sa suna furta kalmar "sokuwar banza ƴar kauye ",
Tsayuwa yayi a kan ta ya zuba mata ido yana nazarin ta cikin tantamar samuwar cikakken hankali a gareta , gefe guda na zuciyar sa na yaba kyaun dogayen fararen yatsun kafafu da na hannayen ta da suke zara-zara kuma fasalin yatsun hannayen nata kamar an feƙe fansiri haka suke da ɗan tsini ta saman su , gwanin ɗaukar hankali duk da ɗauɗa da maikon miya da suka bata su .
Tsayuwar sa akan ta bai sa ta É—ago kan ta da ta É—ora bisa hannayen ta dake kan guwaowin ta ba wanda hakan ya bata É—amar dunkulewa guri guda tana jiran motar tayi awon gaba da ita ,"
Ganin taƙi ɗago kan nata ya sanya ransa sake ɗugunzuma ganin sa tana neman ɓata masa lokaci alhalin shi taimakon ta kawai yake son yi wanda har zuwa yanzu ya rasa dalilin da ya sa yake son taimaka mata ,"
  Ke duba bana son wawanci ki taso na mayar da ke sansanin ku tun kafin dare yayi miki anan karnuka su yagalgala ki ,
  Hamza ke furta hakan yana yi yana yamutsa fuska tamkar an sanya shi yin maganar a dole ,"
Har illa yau dai yakaka taƙi ɗago kan ta taƙi cewa koh uffan duk da cewa ta gane shi ,a ranta kuwa ta gama yankewa kan ta shawara a dalilin zancen karnai da ta ji ya ambata wanda take taji hanyar mutuwar ta mafi sauki shine kawai ta kwana a nan wurin domin tana da tabbacin idan har tayi ido biyu da karnuka a sulusin dare babu abun da zai hana jijiyoyin da ke kai jini cikin zuciyar ta su tsinke ta mutu nan take ," tunanin hakan ya sa ta sake gyara kwanciyar kan ta ta maida fuskar ta zuwa ɗayan bangaren cikin sallamawa.
 Wanda hakan ya bawa hamza damar ganin fuskar ta da jijiyoyin kan ta daga goshin ta da na gefe-gefen idanun ta suka taso raɗa-raɗa koraye shar "kasancewar ta fara sol "
 Firgita yayi da ganin ta a haka wanda a take ya fahimci rangwamen lafiya a gare ta kasancewar sa cikakken likita kuma kwararre wanda gwamnatin jaha ta amince da shi har ya zama ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da marasa lafiyan dake sansanin ƴan gudun hijira .
Sunkuyawa yayi a gaban ta gami da kai hannu ya taɓa goshin ta ," a ɗan tsorace ta ɗago da idanun ta da suka ƙanƙance gami da sake zurmawa ciki ainahin launin su na zaiba-zaiba kamar gilashi suka bayyana tar ,"
Da sauri ya janye idanun sa daga cikin nata sakamakon ji da yayi kamar akwai wani ɗigo dake sashi cikin wani yanayi tun daga ƙasan ruhin sa a tare da idanun yarinyar .
 Ya janye hannun sa tare da miƙewa ya tsaya ,"
  Baki da lafiya , ki taso mu tafi na mayar da ke sansanin ku a duba ki a baki magani zaman ki anan hatsari ne ,"
  Kin ji koh ?
  Jin ta sake yin shiru a karo na biyu ya sa shi shafa sumar kan sa cikin gundura da halin ta ,"gefe guda na ran shi yana mamakin kan sa ta yadda ya damu har yake rarrashin ƴar gudun hijirar da bai san ma daga wanne ƙauye take ba.
  Ke idan baza ki tashi ba zan cicciɓe ki koh da bakya so na kai ki saboda hakki na ne na kula da lafiyar ku , ( haka kou ? naga alama 😂 )
 Ji da tayi yace zai ɗauke ta ya sa ta miƙewa tsaye batare da ta bari sun sake haɗa ido ba , ta nufi cigaba da tafiya ,
 Idan kika sake kika sake taku biyu da waɗannan ramammun siraran kafafun naki zan ɗaga ki sama na jefa ki cikin mota ,"idan ya so ki karye ma ke kika sani doluwa kawai , "dan ma kin samu ina sauke hakki na na taimakon ki da Allah ya ɗora min shine zaki dunga min iskanci da reni ,???
Tare da rashin jin dadi danganta ta da yayi da mai reni ta koma da baya ta tsaya a jikin motar ,' tana mai riƙe kan ta da hannu bibbiyu wanda yake masifar yi mata ciwo tamkar zai faɗo ,"
 Da sauri ya buɗe mata murfin motar
  Shiga muje ! ?
 Tafiyar kurame ita ta biyo bayan gudun da hamza yake shararawa akan titunan da babu wani wadatar motoci , cikin mintuna goma sha biyu ya karaso bakin sansanin nasu ,"
 Â
 Sauke gilashin motar yayi gami da gaisawa da sojojin da suke gadin sansanin da hakan ya sanya yakaka ɗago kan ta da tun da ta shiga cikin motar yake sunkuye ,"
Karaf ta sauke kwarar idanun ta akan ta tana tsugunne a tsakiya tana fuskantar duk wanda zai shigo sansanin ,"daga inda take tana hango yadda take rawar sanyi da jikakkun kayan jikin ta ,"
Wani irin numfashi ta sauke mai tafe da nishin jin daɗi bata yi wani jinkiri ba ta fara tura murfin kofar da kokarin ɓalla ta ta fita ,'cikin sautin da yake bayyana tsantsar murna da farin cikin ta take jera kiran sunan ƙanwar ta ta ,"
  Falmata nah !
  Falmata nah !
Mayar da duban sa yayi inda yaga idanun ta suna kallo ,' yamutsa fuska yayi tamakar ya ga kashi ,"domin haushin yakaka da yake ji kaÉ—an ne akan irin tsanar da yayi wa falmata.
Ke dallah ki nutsu kar ki ballamin murfin mota ," ke da baki da lafiya ina zaki fita da gudu ki je ??
Tun kafin ya rufe baki ta amsa masa cikin siririyar muryar ta da take gauraye da sautin farin cikin da ya gaza boyuwa har akan siririyar fuskar ta da siraran laɓɓan ta suke ɗauke da dariyar da har ya bayyana gajejjerun hakoran ta irin na ƴar uwar ta ,"
  Na warke wallahi na warke falmata na ashe ta dawo bata mutu ba ,"bata ɓata ba dan Allah ka buɗe min kofa naje wajen ta wallahi na daina jin kowwane ciwo a jikina .
Shagala yayi wurin sauraran sassanyar muryar ta da koh kaÉ—an bata tare da hayaniya uwa uba É—an bakin ta da yake bayyana baki sidik É—in dasashin ta da ya kawatu kwarai akan farar fuskar ta ,"
Jijjiga kofar tayi da ɗan karfi cikin nuna alamun ƙosawa
  Dan Allah ka buɗe min !