← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 269

Sashe 8

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara tsayuwar sa yayi bayan ya kammala sauraron bayanin bakin jakadiyar , sannan ba tare da ya nuna wata alama! Akan fuskar sa ba ya ce "madallah da ke jakadiyar sarki zan kuma yi taka tsan-tsan tare da sanya ido sosai domin gano gaskiyar wannan zancen da kika zo min da shi , "bayyanuwar wani abu wanda ya sha banban da wanda kika sanar da ni a yanzu " zai iƴa jawo hukunci me tsanani a gare ki dai-dai da yadda doka da shari'a ta tanadar ga masu yin ƙage da sharri , wanda kin riga kin san haka .

Daga haka ya juya ya fara tattaki domin nufar wurin mahaifiyar sa "cikin zuciyar sa kuwa cike taf da bakin ciki da baci rai ! Akan labarin da jakadiya ta zo masa da shi game da É—an uwan sa muhamadou .'mamman"

Muhamadou shine É—a na huÉ—u a É—akin hajiya mama "kuma shine É—an ta É—aya tal namiji .

******************

Dai-Dai ya sanya kan shi cikin ɗan madaidaicin wurin "da yafi kama da dakin hutawa " ita ma ta kawo kai kiris ya rage su ci gware cikin sauri ta ɗago kai da niyyar buɗe baki amma ganin wanda yake tsaye a gaban ta ya sanya a take ta diririce "tare da yin ƙasa da sauri ta kai gwiwowin ta ƙasa cikin ƴar siririyar murya tace "ina kwana hamma youssouf " , kallon ta yayi na daƙikan da suke gaza da biyar ya ɗauke kansa tare da sake yin kicin-kicin da fuska daga bisani ya wuce yana me amsawa ciki-ciki da lafiya lau " bayan sa ta bi da sassayan kallo daga bisani ta miƙe daga durƙusan da tayi tana me kakkabe gefe da gefen fara sol ɗin rigar da take ɗore bisa kan kayan ta , gyara zaman farin gilashin idanun ta tayi " da saboda firgitar da tayi kiris ya rage ya subuto daga kan siririn karan hancin ta ",

Cikin sassarfar yake taku fuskar sa ɗauke da yalwataccen murmushi da yake bayyana ƙatuwar wushiryar da take tsakanin fararen hakoran sa na sama" har ya ƙarasa gefen dardumar da farar dattijuwar take zaune hannun ta riƙe da wani ɗan ƙaramin littafin addini tana dubawa "zama yayi tare da miƙa hannun sa ya kamo nata hannayen da suke ciƙe da awarwarayen zinare da suke ta faman haske idanun me kallon su , ɗaga hannuwan nata yayi dai-dai fuskar sa ya sumbancin bayan hannuwan nata ɗaya-bayan-daya kafin ya sarƙafe dogayen ƴan ƴatsun sa cikin nata yatsun da suke ƙawace da adon jaan ɓakin lalle da yake ta faman sheƙi tare da tashin sassanyan kamshi "

Fuskar ta ɗauke da tattausan murmushi take bin duk wani motsin sa da ƙwarar idanun ta zuciyar ta fal! Cike da ƙaunar gudan jinin zuciyar ta
"ina kwana ummana kin tashi lafiya ? Yaya fama da jama" ? Allah ya ƙara miki nisan kwana da hakuri da mu umma " cikin murmushi take shafar baƙar kwantatciyar sumar kan sa tana me amsa addu'ar sa da Ameen kafin ta ɗora da tambayar lafiyar sa shima sannan ta ƙara da tambayar sa yayi karin kumallo ? Ƴar dariya yayi sannan "yace umma na makara sai naje officie zan sha café " tana shirin yin magana ta sake shigowa palourdes (falo ) " Bakin ta ɗauke da ƴar siririyar sallama "Budurwar da suka kusan yin karo da biyamaradi ce "

Tare da kulawa hajiya umma take kallon ta kafin ta ce yaya kuma kika dawo SIYAMA ? Ke da kike ta mitar kin yi latti , 'cikin inda-inda tare da satar kallon biyamaradi da ya ciro wayar sa yake dannawa "da alama kira yake shirin yi " tace "umm daman umma kamar nayi mantuwa ne , cikin sauri ta juya gami da nufar wata Æ´ar kofar da take tsakankanin kofofi huÉ—un da suke cikin wurin "bayan ta hajiya umma tabi da kallo cikin ran ta kuwa tausayi-kauna gami da soyayyar siyama ce taf take kai kawo"

Tana shiga ta tura kofar gami da dafe kirjin ta bayan ta jinginu da jikin ƙyauren kofar " a hankali ta juya tare da zamewa ta durƙusa gami da sanya fuskar ta a dai-dai saitin ramin ɗan mukullin kofar , nan take idon ta ya ƙƴallo mata fuskar sa yana hirar sa da mahaifiyar sa hankalin sa kwance in da yake sanar mata da zancen tafiyar sa a cikin kwanaki uku masu zuwa "idan mai martaba ya amince" ɗan jim hajiya umma tayi sannan ta ɗora da cewa wai kou yarona (bata kiran sunan sa saboda sunan surikin ta ne ) shi tahia bisa aykin ba'a iya yin sa ne tare da amre "abun nuhi bai yuwuwa mutun ya tai tare da iyalin sa " ? ...
[6/24, 9:49 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association

*MAFARI .........*
( _HARGITSIN RAYUWA_ )

*Umm'muaz*

3

Gyara zama Biyamaradi yayi kafin yace " A zahiri ummana ba wai ba'a tahia akan hidimar aiki tare da iyali bane sam-sam sai dai duba da irin wurin da zan tai ba kasa ta bace ba ,kuma zan tai ne domin kwantar da tarzoma sannan zan jagoranci mutane sama da dubu É—aya ne ,ni ne shugaba gare su ina bukatar tattara hankalina kachokam na É—ora bisa aykina tare da kula da mutanen da suke karkashi na "

Numfasawa yayi daga bisani ya ɗora da cewa kuma"ummana ki yi duba da irin ita Maimuna ɗiyan sarki ce wacce du inda zata ta zauna sai tare da bayun ta masu yi mata hidima , shin ya kamata daga amren mu na douke ta zuwa wata ƙasa a bakin ayki na wurin da babu tabbacin zata samu irin gatan da take samu a gidan su da kuma wanda zata iya samu da ace anan ta zauna da auren mu ? Ummana a duba lamarin nan da kyau ,?

Sauke numfashi "hajiya umma" tayi duk zance ɗan nata gaskiya ne aykin sa me tattare da hatsarin rasa rai ne , ayki ne na sadaukarwa ga ƙasar sa ,shi ya sanya tun farko bata so ba youssof ya zaɓi da ya zama soja , so tayi yayi ta karatu me zurfi har ya zama alkali ta yadda du ranar da ya zama shi ne bisa gadon sarauta mulki ba zai taɓa yi masa wahalar gudanarwa ba ,

Sai dai duba da yadda shi youssof ya ɗage ya tsaya kai da fata kan ra'ayin sa , ya sanya daga karshe ita da mai martaba suka tsaya masa wurin ganin cikar burin sa bayan kammala karatun jami'ar da ita ma da rarrashi da ban baki youssof yayi "domin da farko so yayi yana kammala karatun gaba da primary ya fada makarantar horar da sojoji " sai dai mai martaba yayi masa jaan ido sosai sannan ya yadda yayi karatun jami'a inda ya karanci fannin sociologue" yana fitowa kuwa ya miƙa takaddun sa ga neman shiga soja , nan take kuwa aka ɗauke sa "kasancewar sa ɗan manya"

cike da so da kaunar aikin sa gami da nuna tsantsar ƙwazo ya fara aykin wanda hakan ya jawo nan take ya fara taka matakan nasara hawa hawa , sau biyu ana sawa da shi a cikin zaɓaɓɓun sojijin da ake turawa kwantar da tarzoma a kasashen ƙetere "kasar Somalia da Libya " cikin ikon Allah kuwa duk tawagar da yake jagoranta lafiya suke dawowa cike kuma da tarin nasarori " hakan ya bashi ɗaukaka a cikin ƙanƙanin lokaci har ta kawo sa ga matsayin da yake kai a yanzu wanda a karo na uku sai ga shi an sake tura shi ƙasar Nigeria domin yaƙi da ƴan tawayen Boko haram "

Cikin yanayi marar daɗi yake kallon fuskar mahaifiyar sa wacce da alama tayi nisa cikin tunani "shi ya san daga mai martaba har umma basa son aikin sa "kuma da yana da iko tabbas da ya haƙura da aikin amma toh shi yaya zai yi ne shi ya tabbatar haka Allah ya halicci zuciyar sa da ƙaunar aikin soja "domin baya mantawa tun yana shekaru biyar yake ƙwalafaci tare da mararin ganin sa riƙe da bindiga sanye da kakin soja haka ya tashi ya tsinci kansa kullum wayewar gari da mafarkin ya zama soja "abun a jinin sa yake "

Muryar sa ce ta doki dodon kunnuwan ta tare da dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula "ummana a cigaba da yi mana addu'a kamar yadda aka saba da iznin Allah babu abun da zai faru da mu sai Alkhairi sannan shekara kamar kwana ce tamkar yau zaki ga É—an ki ya dawo , ya karashe zance yana dariyar tsokana ".

Ƴar dariya itama tayi kafin ta ce addu'a muna kan yin ta yarona kuma insha Allah zamu cigaba fatan mu Allah ya kiyaye tare da shiryar mana ku a duk inda kuke da sauran ƴaƴan musulmai baki ɗaya ,

to yaya ita É—iyar tawa da fatan ka sanar mata da batun tafiyar duk da cewa ma nasan idan har tafiyar takasance mai martaba da kansa zai tada É—an aike zuwa Birnin Agades É—in " ta É—ora da sake tambayar sa, yaya É—iyar tawa ta aminta dai kou batare da ta tayar da hankalin ta ba ?

Gimtse fuska biyamaradi youssof yayi kafin ya É—ora da mun gama magana kuma ta fahimta , cikin ransa ! Kuwa mamakin yadda wannan lamari zai tafi a haka karfi da yaji yana namiji umman sa ta dunga nunawa da lalle ne ya yi abun da maimouna take so ,

Sau tari hakan ya sha faruwa hatta akan tsarin ginin gidan sa da aka yi duniya guda daga can Babban filin da yake karshe a cikin masarautar maimouna ita ta zaɓi irin ginin da take so kuma irin sa sak aka yi , ya rasa gano dalilin haka ,

Shi shine namiji shine shugaba tayaya za'a dunga gwada masa sai abun da matar da zai aura ta zaɓa shi zai yi ?

Miƙewa yayi yana me duba agogon hannun sa cikin sauri yake yi wa umma sallama "Ummana ni zan wuce ina ga yau zan iya kaiwa cikin dare kafin dawowa ta sabadda yau zamu fara zuwa bakin bodar da ta haɗa mu da Nigeria domin duba irin tsaron da za'a fara ajiyewa ta wurin" ,
Chapter 8 · 0% Book details