Sashe 70
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
doctor hamza shi yace mata ta dunga zuwa ta na ɗan taya su hira ko da ta awa biyu ce , bayan ya nemi iznin mahaifin su , yayi masa bayanin su falmata da ƙudirin sa akan su na taimaka musu, sai dai ya boye masa cikin jikin yakaka na banza ne ,maimakon ya fadi gaskiya sai ya ce masa boko haram ne suka kashe mijin ta tun a garin su ,"
Maifinsa bai ƙi ya kawo su gidan su zauna ba , sai dai yayi masa gargaɗi mai karfi kamar yadda ya saba yi masa a kullum cewar ,"Ya tsoraci MATA tare da ƙaidin su yayi hankali da lamarin mata domin sau dayawa su ɗin ba'a gane gaskiyar su , wanda duk ya bada gaskiyar sa a gare su tabbas zasu takaita shi watarana ,"
    Kamar koyaushe ya amsa masa yana jin yadda wani ɗaci ke yawo a zuciyar sa , sam bai so ba da mahaifiyar su ta zamto silar da ya sa mahaifin su ya samu mummunan tabo akan mace da yakasance kullum kalaman sa masu tsauri ne akan MATA ,
*********
Yau yake da niyyar kai yakaka ayi mata scan tare da gwaje-gwajen da ya kamata ayi wa mata a tun farkon samuwar cikin su , duk da cewa har kawo yau bai sake tada maganar cikin ga ita yakakar ba wacce ya lura ita bata da wata damuwa da zaman cikin a jikin ta ,
abun da bai kai ma ga gama fahimta ba kamar son cikin take sosai , saɓanin sauran matan da ya sani da suke shiga damuwa tare da ƙin abun da yake cikin nasu a duk lokacin da suka samu cikin ta haramtatciyar hanya irin nata ,
sai dai ya danganta hakan da kasancewar yakaka yarinya ce kuma akwai ƙarancin wayewa da rashin ilmi a tare da ita , ko ma menene shi daman ba shi da burin raba ta da cikin jikin ta wanda ya riga ya fahimci yayi ƙwari a mahaifar ta .
Ya zaɓi ya kaita wani asibitin daban a duba ta ne a saboda ƙoƙarin sa na kare martabar ta ko da anan gaba ya aure ta , domin a halin yanzu kowa ya san ba shi da mata , to kuma duk sauran likitocin da zai iya haɗa yakaka da su , abokanen aikin sa ne da suka riga suka san juna sosai ,ya kai ta wurin su a zuwan matsayin me take a gare shi ?
Bai son a kodayaushe ya dunga yin ƙarya dan haka ya fi son ya kaucewa duk wani abun da zai sa shi yayi ƙaryar ,"
 Sai da ya bari rahima ta zo misalin karfe huɗu da rabi , ta hau sama ofishin sa tare da ajiye masa na shi abincin , nan yake sanar da ita zata Zauna tare da falmata , shi da yakaka zasu je wani waje su dawo ,"
Tare suka shiga ward É—in inda suka tarar da su suna Æ´ar hirar su , babu laifi cikin sati guda falmata ta ji sauki sosai saboda kulawar magunguna masu kyau da take samu zuwa abinci mai inganci , uwa uba kwanciyar hankalin da ta samu , yini take a kan gado iskar fanka tana kaÉ—a ta , ga ta ga yakakar ta a gefen ta , wanda hakan shi yafi kome sanya ta farin ciki ,
Â
  Cikin fara'ar da jin muryar su ya sanya ta take gaishe da doctor hamza da zuwa yanzu take matuƙar girmama shi tare da ganin ƙimar sa har ma take jin sa a matsayin wani jigo cikin rayuwar su ita da yakaka ,
Shima faram-faram ya amsa mata yana mai sake tambayar ta yanayin jikin nata , kafin ya maida duban sa ga yakaka wacce take zaune bisa kujerar gaban gadon , "suna gaisawa ita da rahima wacce suka yi sabo da juna cikin Æ´an kwanakin ,"
Duban ta ta mayar kan doctor hamza tana mai gaishe shi , cikin Æ´ar siririyar muryar ta ,
  Fuskar sa a sake ya amsa mata yana mai kallon fuskar ta da take fayau babu ko ɗigon kwalliya sai ƴan siraran shunkuran ta "zane" da suke tarwai akan farar fuskar ta ,
  Fatima zamu je na kai yayar ki wani wuri baza mu daɗe ba zamu dawo ga rahima nan zata kula da ke kafin dawowar mu kin ji koh?
  Toh yaya dakta sai kun dawo ! Yakaka sai kun dawo !
Zo mu tafi ,"
 yace da ita yana mai fara taku ,"
  Tiris ! tayi akan kujerar , ina kuma za su ? ? Ita fa sam bata son kaɗaicewa da shi , duk ya bi ya ishe ta da kallo ga warin wannan ƙaƙƙarfan turaren nasa da ba so take yi ba ,"
  Kallon fuskar rahima tayi wacce ita ma ɗin ita take kallo cikin nazari , dan haka ta miƙe a sanyaye gami da yi musu sallama bayan ta jaddadawa falmata akan yanzu zata dawo !
A motar sa suka fita a asibitin , duk da cewa har zuwa yanzu bai faÉ—a mata inda zasu ba ," sai da ya hau titi É—oÉ—ar tukun ya juyo ga kallon sa kan ta da ita kuma ta juya fuskar ta ga kallon titi ,"
  Ƴar kwantatciyar sumar da take gefen kunnuwan ta zuwa gaban goshin ta da tayi luf-luf yayi wa kallon daƙiƙai kafin ya maida kallon sa ga titin gami da yin gyaran murya ,"
   Â
 Asibiti zan kai ki a auna ki tare da duba lafiyar abun da yake cikin ki , dan haka ina son sanin sunan ki mai kyau , domin ayi amfani da shi wurin buɗe miki file ,"
   A hankali ta juyo da ganin ta kan shi ,"
   Cikin ran ta tana jin daɗin yau karo na farko bayan ita da falmata wani ɗan adam ya nuna kulawar sa akan cikin jikin ta har ma zai kai a duba lafiyar abun da yake cikin , "
  Sai dai tambayar sa ta ƙarshe ta bata mamaki daman duk zaman su bai taɓa sanin sunan ta ba ???
Babu shakka ita bata taɓa ji ya kira sunan ta ba , ko magana zai mata kawai yana jefa maganar sa ne a saitin ta kai tsaye ba tare da ya kama sunan ta ba ," amma ai yana ji koyaushe falmata tana kama sunan ta a gaban shi , sai dai idan wani walakanci ne hakan ," zai ce bai san sunan ta ba .
  Kamar ya san tunanin da take
  Ba tare da ya dube ta ba yace ,"
  Sunan ki mai kyau nace ,"wannan sunan da ake kiran ki da shi ba suna mai kyau bane dole akwai ainahin sunan ki ,
  Bani da wani suna bayan wanda ake kira na da shi ,"
  Ta bashi amsa ƙasa-ƙasa , a ran ta Kuwa tana jin haushin kalmomin sa ya za'a yi yace sunan ta bashi da kyau ??
 Ba wanda ya sake cewa ƙala har suka ƙaraso ɗan ƙawatatcen asibitin mai zaman kan sa da yake cikin unguwar G.R.A ,
Jerowa suka yi suna tafe tamkar sabbin ma'aurata , ta wutsiyar ido ya kalle ta tana sanye ne da wata atamfa ruwan ɗorawa da aka yiwa dinkin doguwar riga wacce ta buɗe daga ƙasa , ɗaya daga cikin kayan da rahima ta ba su ne ," nan ya ga yadda ɗankwalin kan ta yayi baya sosai har ya bayyana lallausar sumar da take gaban kan ta , gyalen ta da ta rufu da shi daga kafaɗar ta iskar juyin yanayi da ake na ta kaɗa shi ,"
   gani yayi ta yi masa kyau ba kaɗan ba ,"
Sam baza'a ce mace mai ciki bace , domin idan ban da cikar da ta sake yi tayi ƴar ƙiba kaɗan tare da ƙarin haske , babu wani alamun ciki , cikin bai bayyana a sarari ba ,"
  Â
   Ki gyara ɗan kwalin ki , kuma ki rufa gyalen zuwa kan ki ,"
  Ta tsinkayi muryar shi yana bata umarni ,"
ba tare da ta ce uffan ba tayi yadda yace lokacin da suke ƙarasawa cikin ainahin asibitin ,
Ba tare da É—aukar lokaci ba ya shige gaba ya kammala kome da ake yi a dokar asibitin kafin a ga likita , wanda kuÉ—aÉ—e ne tsababa saboda asibitin na manya ne ,
 Wurin bada sunan ta ne ya so shiga ruɗani kafin lokacin da zuciyar sa ta yanke masa shawarar abun da ya kamata ,"
Aka yi musu jagora zuwa wajen ainahin babban likitan mata da yakasance shine mamallakin asibitin baki É—aya ,"
 Nan ya tare su da fara'a duk da cewa ba wai ya san doctor hamza bane amma yanayin sa ya bayyana masa wayewar sa tare da ilmin da ya hango tare da shi , "
   Bayan bayanin da doctor hamza yayi masa akan a duba lafiyar uwar da abun da yake cikin ta tare da son sanin ranar da zata iya kasancewa ranar haihuwar ta ,"
  Likitan ya fara aikin sa cikin gwanancewa, nan ya fara da ɗaukar jinin ta domin yin gwaje gwaje , ya kuma bata wata ƴar roba yace ta kawo fitsarin ta tare da ƙiran ɗaya daga cikin nurses akan ta gwada mata banɗaki , bayan ta dawo yayi mata awun blood pressure, ya ga jinin ta dai-dai ne , sai yayi umarni da ta hau wani ɗan gadon duba marasa lafiya da yake gefe guda cikin ofishin domin yayi mata scanning ,"