← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 207 OF 269

Sashe 207

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har dai a kwanaki shida bayan zuwan su ta daure bayan sun gaisa da Hajja wacce take kishingiÉ—e akan Æ´ar katifar É—akin ta , ba tare da ta yadda sun haÉ—a ido da Hajja ba tace ,

" Hajja daman zuwa nayi nace miki , un'un wai inji Baa , sai kuma tayi shiru ,

Hajja wacce ta tashi zaune , tace ,

"UwarÉ—akina faÉ—i mana , me kike son faÉ—a min ?

"Daman nace Hajja idan kun yi waya da shi ki ce masa akwai saƙon da nake son faɗa mi shi inji Baa ,

Kallon tsanaki Hajja take yi mata kafin ta ce , " Shi wa fa ?

  Ɗago kanta tayi ta saci kallon Hajja , tana sake gintse fuska tace , " shi Baban Mama ko ?

Salati Hajja ta sa tana tafa hannuwa , kafin tayi ƙanƙan da ido tace ,
   " Ke Fatima ki fita idona na rufe ,nace ki fita idona ,  idan ba kin mayar da kanki wata bi ta can ba , har kya bani saƙo wajen Mijin ki ? Cewa nake ke kika fi kusanci da shi fiye da kowa a ƙasar nan ? To bari na faɗa miki daman ina cike da ke akan irin sakarcin da kika yi na gudowa daga ɗakin auren ki , akan wannan mummunar zuciyar taki mai ƙullaci da bauɗaɗɗan halin ki na miskilanci idan baki gyara kin nutsu kin san ina ke miki ciwo ba ke ce da Nadama marar amfani wataran , ni nagaji da nuna miki gabas kina daɗa bauɗewa,

Zunburo baki Falmata tayi , ƙasa-ƙasa tace " to ai ba komawa zan yi ba ,

Ashe maganarta ta shiga kunne Hajja , sai ji tayi tace ,
  " Auho aikin kawai kike domin shima kuwa wannan karon kin kai shi bango da iyashegen ki , dan tunda muka taho yau kwana shida muna yini na bakwai bai biyo sawun mu ba ko da da ƙiran waya , ni kuma na ƙira layin nasa da nake da shi bai tafiya , ai kin ga sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha , idan zaman gidan daɗi ne ki zauna ga waje kiyi ta zama har mahadi ya bayyana .

Daga haka ta jaa bakin ta ta tsuke tana kawar da kai .

Rai a ɓace Falmata ta miƙe ba ko sai anjima ta fice a ɗakin , Hajja ta bi bayan ta da kallo , cikin ran ta cike da tausayin ƙuruciyar dake ɗiban ta tana shirin sanyata yiwa kanta sakiyar da ba ruwa , ita a karan kanta ba ƙaramin damuwa tayi ba da rashin ji daga wajen Youssouf kamar yadda yace kafin rabuwar su zai ƙira domin jin labarin halin da suke ciki , rashin ƙiran nasa ya ɗaure mata kai , tsoron ta ɗaya kada ace ya sau auren Falmata , ko kaɗan bata fatan hakan , tayi ƙiran wayar sa aƙalla sau goma bayan tahowar su amma bata shiga fatan ta Allah yasa lafiya .

Haka kawai ta ji damuwa tana mamayar ta kan cewa da Hajja tayi tunda suka taho wai bai ƙira ba , ita a nata zaton su na gaisawa da Hajja ta waya , kawai bai neme ta bane sanin da yayi tana fushi sosai da shi dan haka ko an kawo mata wayar ma ba karɓa zata yi ba kamar yadda ita ma ta kuɗurce a ran ta ,

To ashe ma ita take zaton haka shi yana can ko tunawa da sha'anin da ya shafe ta baya yi , ya riga ya yada da ita da abunda ke tare da ita , duk sai jikin ta ya sake yin sanyi ƴar hirar da suke yi ma ita da Yakaka da Rahima ƙarama kafin tashin ta zuwa ɗakin Hajja,  sai ta gagara cigaba da sa baki tayi lamo a kwance tana jin yadda abunda ke cikinta yake dunƙulewa waje guda ,

Yakaka ita ta lura da shirun da tayi dan haka ta kai hannu ta jaa yatsar ƙafar falmata tare da cewa ,

  " Maman baby yaya ne ? Akwai damuwa ne ?

  Janye ƙafar ta tayi ba walwala a muryar ta tace ,
   " Maman mama kin san dai na ce ku daina ƙirana da sunan nan bana so ,

Rahima ta kwashe da dariya "  to Yakaka mu daina cewa Maman Baby , mu koma ƙiran ta da Matar soja yafi daɗi ko Hajja Falta ?

Kuka ta fashe da shi da a farko suka yi zaton na wasa ne , sai da suka ji har tana jaan hanci tukun suka tsahirta daga dariyar da suke duk kuma sai hankalin su ya tashi jikin Yakaka har rawa yake ta tallafo Falmatan zuwa jikin ta suna rige-rigen tambayar ta " me ya same ta take kuka ??

   Ba tare da ta daina kukan ba tace ," Nace muku bana so  , bana so bana so , kun ƙi dainawa .

  Da sauri Rahima tace , " Yi hakuri ba zamu sake ba dan Allah ki daina kuka daga wasa ? Haba Fatima-zahra Maman Baby ,
   Da sauri Yakaka ta ɗago tana hararar Rahima ,
   Dariyar da Rahima take bata tuƙe ba ta dafe baki tare da cewa
   " Au So nake nace Mamar Mama ta biyu , yi haƙuri ba zamu sake ba kin ji ƴar ƙanwata ?

Batare da ta amsa ba ta zame daga riƙon da Yakaka tayi mata ta koma ta kwanta a inda ta tashi , wani irin yanayi marar daɗi na sake mamayar ta baki ɗaya bata jin daɗin kome , abu kaɗan sai ya ɗaga mata hankali ya ƙara mata damuwa .

  Fuskar Yakaka cike da damuwa take kallon ta , damuwar da ta hango tare da ita ya ɓata mata walwalar da take ciki mai daɗi , cikin ran ta ta haƙiƙance akwai abunda ke damun Falmata haka kawai ba zata yi kuka ba daga ɗan wannan wasan , ji tayi ta damu da son sanin damuwar ƙanwar ta  .

Tun daga ranar sai duk walwalar ta ta ragu damuwa ta bayyana a cikin suffa da mu'amalar ta , kome take yi babu nishaɗi duk kuwa da cewar basu taɓa tsintar kan su a cikin gata da riritawa irin na wannan lokacin ba , daga kan Mamar su har zuwa Amnee da Baa , Rahima da kusan kowa na gidan nan-nan ake da su ,

Sai dai damuwar ta mai zurfi ce , kullum cikin kasa kunne take ta ji ko Hajja zata ƙira ta tace ga Youssouf ya ƙira su yi magana ko kuwa ma tace ya ƙirata ita sun gaisa amma ko alama ta yin ƙiran nasa bata ji ba , ita kuma tsoron surutun Hajja ya sa ta kasa tambayar ta .

***

Yau tana zaune a tsakanin mamar su da Amnee suna Æ´ar hira , su ukun ne kawai a wajen , Rahima da Yakaka sun tafi amso sabbin É—inkunan su da Baa ya bayar da kuÉ—i aka kawo musu atamfofi da lesika aka kai É—inki domin su yi amfani da su wajen bikin auren Rahima da yanzu bai fi kwanaki goma sha biyu ba suka rage .

Amnee ta É—an dube ta tana murmushi tace ,
   " Fatima zahra , cikin nan naki wata nawa yake ciki ne ? Anya bai kamata ki fara zuwa awo ba ?

  Da sauri ta ɗago kai ta dubi Amnee sai kuma ta sunkui da kai batare da tace kome ba ,

Khaalty Rahima ta É—an dube ta , tace Fatima ba dake ake ba ?

  A hankali tace , " Nima ban sani ba Amnee ,

Jimm Amnee tayi kafin ta ce , " to ai ya kamata ki fara zuwa awo banda ma dai shirme irin naki Fatima cikin fari da ake ɗokin sa da yi masa ƙirgen ƙwaƙwaf amma ke kyace baki san watannin sa ba ?

Hajja wacce take ƙarasowa falon daga waje inda ta gyara shanyar alkamar da ta wanke ta yin kunun Baa , sarai ta ji wasu daga kalaman Amnee , tace
   " Wallahi uwar masu gida ke ma dai kya faɗa , wannan uwarɗakin tawa da kike gani kome nata daban ne bata ajiye kome ba sai wauta , cikin nata yana gaf da cika watanni huɗu a yadda lissafi na ya nuna min , sai dai kuma kin san cikin fari ɓuya ce da shi amma lokacin da suka dawo dai daga can turai cikin bai wuce watanni biyu ba da ƴan ɗoriya , daga can ta yo cikin ,  yanzu kuma kin ga dawowar tasu kusan kwanaki talatin .

Dariya ce ta so kama Khaalty Rahima jin wannan ƙokari na Hajja na ƙididdige kwanakin cikin Falmata da ko ita kakar ɗan ko ƴar ba ta iya haka ba ,

Ran ta cike da jin daɗin tsantsar ƙaunar da ta lura Hajja na yiwa ƴa ƴan ta tace ,
  " Hajja baki da dama ke da Uwarɗakin ki ba mai shiga tsakanin ku , wannan zuwa awon ma ai ke zaki dunga raka ta  .

  Ƴar dariya Hajja tayi kafin ta harari Falmata tace ,
    "  can dai su ƙarata ita da Babba Uwar Mama ita zata raka ta bana iya miskilancin fatima ba .

Dariya Amnee tayi kafin tace,
  " zan yi maganar da Baa Alaji idan ya so sai ya nema mata iznin mijin nata , kan fara zuwa asibiti saboda kuwa zuwa awo abune mai matuƙar muhimmanci ga mata masu ciki , yadda duk muka yi sai ki shirya a fara kai ki kin ji ko ƴata ?

A hankali ta gyaÉ—a kai kurum , tausayin abunda ke cikin ta kan yadda Mahaifin sa yayi banza da su ya fara kamata .

Daga haka Amnee da Mama suka cigaba da yin hirar su , a hankali ta miƙe ta nufi ɗakin su , domin kuka da take jin yana taso mata ,

Tana shiga É—akin ta sanya tafukan ta duk biyu ta rufe fuskar ta tana fashewa da kuka marar sauti .
Chapter 207 · 0% Book details