Sashe 208
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana tsakiya da yin kukan ta tsinkayo Sallamar Doctor Hamza , shuru tayi tana saurarawa jin tashin muryar gaisawar da suke shi da iyayen su ,
Jin sun gama gaisawa sai ta miƙe tan share hawayen ta , Doctor Hamza yana sawun gaba na mutanen da ba zata manta alherun su ba a rayuwar ta ,dan haka ya zama dole duk inda ta ji shi ta je ta gaishe shi ko da kuwa babu ƴan uwantaka a tsakanin su bare yanzu da suke ƴan uwan juna makusanta ,
A hankali ta fito , ta tako zuwa tsakiyar falon ta zauna tana gaishe shi ,
Da murmushi yake amsawa yana jin daÉ—in ganin ta samu lafiya , yace
  " Fatima ƙanwata ke ce haka kika girma ? Alhamdulillah lafiya ta samu .
Ƴar dariya tayi , kafin tace " Ni ce Yaa dakta ,
 Dariya shi ma yayi yace " lalle girman 'ya mace ba wuya , Al'amarin Ubangiji kuma ya zarta yadda duk muke zato , Khaalty lokacin da na kawo yaran nan gidan nan ko kusa bani da masaniyar muna da wata alaƙa tsakanina da su , kawai nayi niyyar taimakon su ne domin Allah , ashe kin ga ma abun farin-ciki ƙannena ne su , lokacin da Amnee take sanar da ni ba ƙaramin mamaki nayi ba da farko ma ni na shiga ruɗani ne su waye Amina da Fatima ? Sai da ta min bayani sosai ,
Ya nisa kafin ya cigaba da cewa , " Khaalty nayi murna da Allah ya haÉ—a ki da Æ´aÆ´an ki , Allah ya kuma kare ku baki É—aya , ya sa bakin wahalar ku kenan .
 " Amin Amin ɗana , tace da sigar zolaya ,
 Shima dariyar yayi da sauti sanin cewa ta ƙira shi da ɗanta ne dan tasan bai son haka tun yana ƙaramin sa a cewar sa tayi ƙanƙanta ta ƙira kanta Mamar sa ina ma laifin tace ita yayar sa ce ?
 Khaalty Rahima ta cigaba da cewa , " kawai sai muka gan ka babu sanarwar zuwa ? Ko wani aikin ka zo yi ?
 Jingina kansa yayi da kafaɗun kujerar da yake kai , yace
 " Baa ne ya ƙirani tun shekaran jiya , yace lalle na zo cikin kwanaki biyun nan , to nima daman kuma ina shirin zuwa saboda shirye-shiryen bikin nan ban sani ba ko akwai abunda za'a iya buƙata mai muhimmanci ayi a gama akan lokaci tunda ga ku , kar ya zama irin na bikin su zainab kome a hagunce , aiki ne ya tsare ni ban iso da wuri ba .
 " Na fara shiga wajen Baa ɗin amma na tarar da shi da mutanen nasa kin san sai kuma ya sallame su da abunda suka saba , kai mutanen mu sai a hankali , wai kawai sai ku mayar da wani mutum ɗaya wajen zuwa ku faɗi buƙatun ku da damuwar ku kamar wani shi ɗin injin buga kuɗi gare shi ? To wai wanene bashi da buƙatu da damuwowi ?
Sallamar Rahima da ta shigo da ɗan gudun ta , ya sa shi mayar da ganin sa kan ƙofar , dai-dai da shigowar Yakaka , wacce tunda ta ji Rahima na murna tana cewa ga motar Company ya zo , ta ji jikinta yayi sanyi duk taku ɗaya na kafafun ta da jin ƙarin hauhawar bugun zuciyar ta ,
Idanun ta ta sauƙe kansa da shigowarta falon , karaf suka haɗa ido ,
Kowanne su yayi saurin janye ido Doctor Hamza ya haɗa da kawar da kai ita kuma ta sunkui da kan ta , cikin raggon taku ta ƙaraso ta bayan kujerar da Amnee take kai , tayi durƙuso da kyar ta haɗo kalmomin ,
  " Ina wuni ,
 Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da zolayar Rahima da yake cewa " ke little idan ana shirye-shiryen aure ramewa ake yi ke kuwa ga ki sai sake kumbura kike , me takwarar ki take baki haka hala ɗure take miki ??
  Dariya Khaalty Rahima da Rahima ƙarama suka sa a tare , kafin Rahima ta zagaya ta kujerar da Amnee take ta saƙalo hannuwanta a wuyan ta , tana haɗa fuskokin su tace ,
  " Khaalty kar ki faɗa masa , abun sirri ne ko ?
Â
Amnee wacce ta lura da yadda yayi watsi da Yakaka , kuma bata ji daÉ—in hakan ba sai ta ce ,
  " Takwarata tana gaishe ka fa ?
Wani wur-wur yayi da ido , sai kuma yace " Ok Lafiya , ba tare da ya dube ta ba illa haÉ—e girar sa da yayi , ya zaro wayar sa daga Aljihunsa , kaf fara'ar fuskar sa ta É—auke .
A hankali Yakaka ta miƙe tana murmushin yaƙen akan wasan da Mamar su da Rahima suke yi , sum-sum ta wuce ɗakin su .
Ƙiran wayar Amnee da aka yi yasa suka ɗan tsahirta daga hayaniya , bayan ta ɗaga wayar sai ta saurara ,
 " to Baa Alaji tace.Â
Duban Khaalty Rahima tayi , tace
 " Ukhtee , da ke da Ɗan ki ku zo muje Baa alaji yana ƙiran mu .
***
Bayan sun sake gaisawa a tsakanin su ,a ƙagauce Amnee da take zaune daga gefen sa tace
 " Baa Alaji lafiya dai ko ? Wannan Æ™iran Allah ya sa Alheri ne.Â
Prof ya dube ta da É—an murmushi , yace " inshaAllah Alheri ne Aminatu ,
ganin ya mayar kan Hamza da Khaalty Rahima da suke zaune a ƙasa kafin ya fara cewa .
" Dalilin da yasa na ƙira ku ba kome bane sai kan wata magana ko kuwa nace shawarar da na yanke tun watanni baya , amma ban sake haƙaƙewa akan abunda nake niyyar yi ba na haɗa Aure tsakanin Ƴaƴa na biyu kai Hamza da kuma ƙanwar ka Amina ba , sai da tabbatuwar yaran nan ƴan uwan ka ne ba wasu bare ba da ba'a san asalin su ba , hakan ya sa na sake ganin dacewar lamarin fiye da farko ,
" Duk da cewa batun ƙarin auren da nace kayi ba sabon abu bane a wajen ka , tun kwanaki na sanar da kai ka kuma yi na'am kawai wacce nake burin ka aura ɗin ne baka kai ga sani ba , sai a yanzu nake sanar da kai Aminatu ƴar Rahima ƙanwar Mahaifiyar ka ita ce matar da nake son ka aura a matsayin matar ka ta biyu , da fatan ba zaka yi gardama ba ??
Daga Khaalty Rahima har Doctor Hamza baki ɗaya idanu suka zuba suna kallon sa , a hargitse sosai ƙwaƙwaƙwar Doctor Hamza take , meke nan yake ji ? Yaya Baa zai masa haka ?
A hankali ya sauƙe ganin sa daga kan prof ya sunkuyar da kansa ƙasa , ta wutsiyar ido yake hango yadda Khaalty Rahima ta dawo da ganin ta kan sa , zuciyar sa na shaida masa cewa amsar sa kowa a wajen yake jira , kan ya amince ko kuwa a ah ?
abunda ya bi duk wasu gaɓɓai na jikinsa ya kassara bai wuce kaifin idanun Khaalty Rahima ba , matar da tunda ya buɗi ido ya gansu tare da Mahaifiyar sa a matsayin shaƙiƙan juna , ƙaunar ta a gare shi kuma mai tarin yawa ce , jin daɗin wasannin ƙuruciyar sa duk ya yi tare da ita , shi kuwa ta yaya zai iya cewa yaƙi ƴar da ta haifa daga cikin ta a tsatson idanun ta ? wallahi ba zai iya ba , Baa ai bai kyauta masa ba da ya titsiye shi da wannan batun a gaban idanun Khaalty Rahima ,
Satar kallon Amnee yayi yaga yadda ta nutsu fuskar ta da wani irin yanayi na nuna zaƙuwa tana kallon sa .
Yawan ƙaunar da Amnee ke yiwa Rahima ya san kuskure kaɗan idan yayi kan lamarin nan zai matuƙar sanyata a ɓacin rai , shi yaya zai yi ne ?
Muryar Khaalty Rahima da ta ratso shirun wajen ya katse masa tunani ,
 Da wani yanayi cikin muryar ta da ya sha banban da murmushin yaƙen da yake fuskar ta a lokacin tace ,
 " Yaya , mun ji daɗi mun kuma yi farin-ciki da wannan haɗin da kayi niyyar yi , Sai dai Yaya , Hamza ai tuni ya riga ya zaɓi abokiyar zaman sa har kuma tafiyar su ta fara miƙawa cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna ba tare da yana da niyyar ƙara yin wani auren ba , dan haka ni ina ganin Yaya da dai an bar yarona ya zauna da matar sa ɗaya kar a ɗaura masa nawin mata har biyu da bai shirya ba .
Prof da yake kallon duk su biyun , ya gyara zama , yana mayar da ganin sa gaba É—aya kan Khaalty Rahima .
" Rahima wannan ba hujja bace da zata hana auren Hamza da Aminatu , sai dai idan kin nuna min Aminatu ba ɗaya take da sauran 'ya'yan da na haifa da nake da ikon zaɓa musu abokan rayuwa ba, ko kuwa har yanzu baki huce daga abunda ya gabata ba shiyasa zaki gwada hakan ta hanyar hana wannan al'amarin tabbatuwa ko Rahima ?
Da taruwar hawaye a idanun ta muryar ta cike da tashin hankali , ta shiga girgiza kanta tana cewa " Haram ko kusa ba haka bane Yaya , dan Allah kar kace haka , a tun kafin bayyanata Aminatu da ƴar uwarta suna da wani majiɓanci da ya wuce ka tsawon wannan shekarun ? kayi haƙuri ba nufina ba kenan , ni shi nake...
"Â idan ba haka bane to ki barni nayi abunda nake da manufar yi inshaAllah alheri ne a garemu baki É—aya ,
Bai saurara ba ya juya ga Doctor hamza da zuwa lokacin gumi ke tsattsafo masa a goshi , da murya dake cike da gargaÉ—i Prof yace ,
  " Likita kai nake saurare kai kuma me kace ?