← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 269

Sashe 22

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ciki-ciki ya amsa mata da "lafiya" saɓanin tafeedah da suka gaisa sosai cikin sakewa har ma yake tambayar ta akan lamarin aikin ta inda ta tabbatar masa da ta ɗauki hutu na tsawon sati uku ,"

cigaba tayi da satar kallon biyamuradi da aisha wanda suke hirar su ƙasa-ƙasa cikin tsantsar shaƙuwa da kulawa da junan su da alama wata matsala ce da aishan wanda ta ƙagautu ta haɗu da yayan nata ta faɗa masa kasancewar ta rainon sa kuma abokin shawarar ta ,

cikin nazari take kallon sa bata samu ƙwanciyar hankali na sosai ba sai da ta fahimci faɗuwar sa ta jiya da dare bata haifar masa da wani rauni ba ,"ta sauke boyayyar ajiyar zuci , tana me Ƙwaɗaitawa a ranta ina ma ita ce maƙale da kafaɗun biyamuradin yana sauraren ta cike da kulawa da ƙauna kamar yadda yake yi wa ƴar ƙanwar ta sa ,"

lokaci zuwa lokaci suna sakarwa juna murmushin yaƙe ita da tafeedah da rabin hankalin sa yake kan wayar sa domin idan da sabo yaci ace ya saba da yadda yake zama saniyar ware a duk lokacin da biyamuradi da aisha merama suka haɗu .

Da yalwatacciyar fara'ar ganin ƴaƴan nata ta ƙaraso falon , cikin hanzari bayun suka yi jerin gwano suna masu isar da gaisuwar su ɗaya bayan ɗaya , kafin cikar mintuna biyu sun cika babbar dardumar da suka shimfiɗa da kawatattun kwanukan abinci na alfarma ,ficewa suka fara yi ɗaya bayan ɗaya bayan sun sake kai gaisuwa .

Da murmushi take amsa gaisuwar yaran nata tare da tambayar su yaya suke ,"

Umartar aisha tayi da ta zubawa yayun nata abinci ," ita kuma tuni siyama ta zuba mata abubuwan da take tunanin zata so ,"ta ɗebo ruwa a wani kyakkyawan mazuɓi tare da kamo hannun umma ta hau wanke mata su ," cike da so da kauna take sanya mata albarka ," tana me sunkui da kai take amsawa da ameen umman mu .

Bayan sun kammala cin abincin ne tafeedah ya miƙe bayan amsa wayar da yayi wanda saƙo ya iso gare shi ana neman sa ," ƙarasawa gaban umma yayi tare da yi mata sallama addu'a tayi masa tare da ɗaurawa da nasiha ta ƙare da gargaɗin sa akan idan har yana cikin garin maraɗi kar ya yanƙe zuwa wurin ta kullum koh da bayan tafiyar aminin sa ,

Tare da ladabi yake amsa mata da yi mata alkawarin ba zai ɗauke ƙafar sa daga sashin ta ba koh da youssof baya nan , sallama yayi mata tare da miƙewa ya fice bayan sun yi musabaha da aminin nasa .

Bin sa yake son yi domin ya shawo kan sa amma bashi da kuzari koh kuwa bai tanadi kalmomin da zai yi amfani da su wurin wanke fushin da yake hangowa a idon tafeedan ba , dan haka ya bar shi ya sarara zasu  shirya a waya , domin sanin da yayi cewa shi da aminin nasa basa iya wani dogon fushi da juna , duk saɓanin ra'ayin su bai taɓa jawo musu fushi da junan da ya wuce awanni ishirin da huɗu ba , dole daya zai nemi daya koh da ta waya ne koh ta hanyar sakon kar ta kwana su shirya ," kaunar junan su daga Allah take ,"

Cikin son fahimtar samun saɓani a tsakanin su umma take bin su da kallo har lokacin da tafeedan ya bacewa ganin ta ," tasowa biyamuradi youssouf yayi gami da dawowa daf da ita tamakar zai hau cinya ,"riko hannayen sa tayi tana me murmushi tace ,"yarona tun kafin ka tafi ka fara bani kewa ƙwarai zan yi kewar ka bani kaɗai ba har mai martaba ma jiya ya ɗauki lokaci yana mitar nisan da zaka yi mana alamu sun nuna kiris yake jira ya janye alfarmar da yayi na barin ka tafiyar nan ,"

Tare da tsananin ƙaunar iyayen nasa da yake taso masa yana kokarin dannewa yace "umma na shekara tamkar kwana ce kamar yau zaku ga Allah ya dawo muku da ni ,'kuma a jiya mai martaba ya sanar da ni cewa duk lokacin da yaga dacewa zai dunga tashin mutane daga nan musamman suna zuwa dubo masa ni ,ko da shi da kan sa bai samu damar zuwa ba ,"

umma na nima zan yi kewar ku ya karashe zancen sa yana me "É—aga tafin hannunuwan ta ya sunbata tare da sanya kumatun sa a tsakanin hannun ta ,"ya cigaba da cewa addu'ar ku ita nafi bukata domin ita zata min jagora zuwa kan dukkanin wasu matakan nasara akan tafiyar da na sa gaba ,"

Murmushi tayi tana jin yadda kowacce ɗakika ɗaya take ƙaruwa da yawan kaunar ta ga gudan jinin zuciyar ta ", baza mu gushe ba muna masu yi muku addu'a har sai lokacin da mai rabawa ta raba tsakani ," ta furta hakan tana me kokarin maida ƙwallar da take son cika mata gurbin idanu ," yi maza kayi harama yarona .

Waiwayawa tayi ta dubi sashin da siyama take zaune wacce a zahiri take shafa fuskar wayar ta da ta jiƙe sharkaf da ruwan hawayen da yake ta ɗiga a bisa fuskar wayar ,"a dalilin matsananciyar kewar biyamuradi tare da wani karfin son sa da yake hanƙoro a cikin zuciyar ta , uwa uba damuwar ta da halin da biyamuradin zai iya kasancewa a ciki bayan tafiyar sa zuwa wata ƙasar , duk da cewa ba wannan ne karon sa na farko ba ,amma ita a gareta a duk lokacin da zai yi nesa da yin tozali ga idanun ta rauni ne sabo zuciyar ta take yi .

Siyama ta kira sunan ta ,"na'am umma ,!

Yi maza ki sa a fito miki da kayan naki a kai mota ku zo ku kama hanya kar rana tayi sosai ,"

Ta juya ga biyamuradi youssof wanda bai kai ga fahimtar kalaman mahaifiyar tasa ba , tace ", koh zaka yi magana ga hadiman naka "sojojin sa" tun da su suka san shirin motocin tafiyar ta ku , zu zo su É—auki jakar siyama zata bi ka ku tafi tare zuwa niamey É—in , ku kaita har gidan "ubbo"

Cikin jirkituwar fara'ar fuskar sa yake kallon bakin mahaifiyar tasa lokacin da take rattabo masa bayanin , amma kuwa lalle yarinyar nan tayi bala'in raina sa , watau ma da shi zata haɗa hanyar ta duk tarin direbobi da motocin da suke jibge a gidan nan ta rasa waye zata nema haɗa hanya da  sai shi ? A fusace ya waiwaya bangaren da yake zaton take da niyyar gargaɗin ta da idanun sa amma wayam yaga bata nan .

Cikin kwantar da kai yace ,"amma umma ni ba kai tsaye zan tafi zuwa niamey ba zamu tsaya a wasu wuraren me zai hana direba ya kai ta ?

Cikin É—an É—aure fuska umma tace ,"ko ma ina zaka biya tun da dai niamey É—in ka nufa tare zaku tafi hankalina zai fi kwanciya sanin tana tare da kai cikin tsaro fiye da idan direban gida ne zai kai ta ," kayi musu umarni a zo a fito da kayan ta ,

Bai samu zarafin amsa mata ba ya hango fitowar siyama wacce ta sauya shigar ta daga doguwar rigar da take jikin ta a ɗazu ,zuwa wani sassalkan leshi ruwan madara wanda aka yi masa ɗinki riga buba da zane ta ɗaura ɗankwalin ta ya zauna mata ɗas akan tarin bakin gashin ta irin na fulanin usul , sosai kayan suka haska mata fatar ta me dauke da matsaicin haske ,zanen kuwa ya zauna ɗabas a cikakken kunkumin ta ,kafafun ta sanye cikin takalma marasa dunduniya bakake , hannun ta ɗaya rike da bakin mayafin ta ɗaya hannun kuma ƴar ƙaramar jaka ce da kallo daya za'a musu asan tare aka ƙera su da takalman kafafun ta ,

Cikin takun ta na rangaji wanda ya dace sosai da zubin ta na doguwar mace samɓal take takowa bayan ta bayun ta ne biyu biye da ita ɗayar rike da jakar kayan ta ɗayar kuma ta riko jakar da take ɗauke da computer ta da kuma wasu tarkacen takaddun su na likitoci ,"

Wani banzan kallo me tafe da sumfurin harara iri daban-daban da biyamuradin ya watsa mata lokacin da take ƙarasowa falon shi ya sa ta kusa faduwa ba shiri ta ɗauke idanun ta da tsautsayi yasa ta jefa su cikin nasa ta mayar da hankalin ta kan ummu wacce take ta faman sakar mata murmushi ,"umma na fito ,"

A fusace biyamuradi ya miƙe gami da yiwa umman sallama tare da tabbatar mata cewa zasu kasance akan waya a kodayaushe ," ba tare da ya sake kallon sashin da take tsaye ba ya sanya kai ya fita a karkashin rakiyar addu'o'in mahaifiyar sa .

Risnawa tayi tare da yiwa umman sallama wacce take jaddada mata da ta kula kan ta , kuma ta tabbatar bata wuce iyakacin kwanakin da ta É—iba zata yi ba a karshe ta É—ora mata da tarin addu'o'i ,"maza je ki kar su jira ki Allah ya kiyaye hanya ,"

Da gudun ta , ta karaso har tana ɗan haki jikinta rigar wankan ce sai katon tawul ɗin da ta rufu da shi ,"kar dai hamma nah ya tafi ta furta hakan tana mai taro ƙwalla cikin idanun ta ,"

Ba tare da siyaman ta amsa mata ba ta ɗaga kafafun ta tana me ƙarasa ficewa daga falon tana jin lokacin da hajiya umma ta fara rarrashin aishan wacce ta ɗauke ta tamkar ƴar cikin ta ba ƴar kishiya ba ,"

Ta É—auki tsawon mintoci biyar a tsaye gaban jerun gwanon motocin su biyar bayan da tun fitowar ta wani soja ya amshi jakankunan hannun bayun ta ya sanya su a bayan mota, bayun suka koma suka tsaya daga bayan ta sanin cewa basu da ikon tafiya su bar wajen har sai idan ita tayi musu umarni koh kuwa sun ga tafiyar ta .
Chapter 22 · 0% Book details