← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 269

Sashe 134

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manzon Allah yana cewa : duk wanda yayi tuba na gaskiya to zai kasance kamar bai taɓa aikata wannan Zunubin ba , amma wanda yake tuba alhali yana komawa ga aikata zunubin sa to tamkar yana yiwa Allah izgili ne .

kiyi Tuba na gaskiya yakaka tare da niyyar baza ki sake kusanta kan ki ga aikata ZINA ba a rayuwar ki , Allah zai yafe miki ya wanke ki a idanun Al'umma domin Laifin shi kika yiwa ,

Sannan , ki tashi ki nemi ilmi ki kuma yi aiki da shi idan dama ta samu gare ki kome ƙanƙantar sa ki koyar da ilmin da yake gare ki domin sauran Al'umma su amfana ,

shiriya ta zo miki hasken ilmi ya zo miki ki sa hannu biyu ki karɓe su ƙwarai akwai falala tare da samun dacewa a cikin su , ki manta da rayuwar baya ki himmantu wajen neman gafarar ubangiji akan saɓon da kika wanzu kina aikatawa , da fatan kin fahimce ni ??

bata amsa ba illa hannu da ta kai ta rungume malama maryam , idanun ta na zubar ƙwallar da ita kaɗai ta san dalilin sauƙar su a daidai wannan lokacin

Godiya ta dunga jerowa malama maryam har lokacin da ta sanya ƙafar ta tana barin gidan lokacin dare ya fara shiga karfe goma saura ,

kan titi babu kowa garin ya sake ɗaukar sanyi , a hankali take tafe iska yana ɗaga hijabin ta , tayi zurfi cikin tunani , daki-daki take tuno kome da ya dunga faruwa a rayuwar su ita da ƙanwar ta ,

tana so ta zargi iyayen su akan killace su a gida da suka yi suka hana su neman ilmi , sai dai so irin na tsakanin ɗa da iyayen sa ya mata dabaibaiyi yaƙi bata dama , ji take suna da wata hujjar su , babu shakka akwai dalili ,

tunanin falmata da baby mama yayi mata dirar mikiya , wata irin kunyar falmata ta ji tana nuƙurƙusar ta , yaya zata Ji ranar da duk ta san irin kuskuren da tayi har ta samar da baby mama ta gudu ta bar mata ita ? Wataƙila daga ranar zata fara tsanar ta ,

tsoro take ji tsoron girma ya zowa baby mama ta samu sani akan irin ta hanyar da aka samar da ita , ? Me zata cewa waÉ—annan bayin Allah biyu ??

Lalle wajibi ne a gare ta ta nemi ilmin addini ko domin ta samun ƙarfin guiwar da zata iya fuskantar su tare da tarin hujjoji da bayanan da addinin ya tanadar domin ta gamsar da su ta kuma wanke kan ta a idanun su su san cewa ta aikata kome ne cikin DUHUN JAHILCI ,!

Ko zasu fahimce ta ? Ko falmata zata yadda ta cigaba da riƙe ta a matsayin ƴar uwa masoyiya ? Ko baby mama zata yadda da ita a matsayin uwa ?? Yaushe wannan ranar zata zo ? Zata zo nan kurkusa , ko sai bayan shuɗewar tsawon wani lokaci ? Abun da ta riga ta sani muddin su na raye wannan ranar zata zo ,

YARIMAN MARAÆŠI ,

Zuciyar ta ta auno mata da sunan sa da kome da ya wakana cikin rayuwar ta a wannan gaɓar shine sanadi ,

bata gan shi ko kusa tare da duhun jahilci makamancin nata ba , kome da shi yayi mata yayi ne cikin ilmin sa ,da sanin sa ya aikata Zina da ita ,

zuciyar ta take ji tana wani irin buÉ—awa da sabon yanayin da yake shigar ta akan sa da sabon matsayin da ya kamata ta ajiye shi tun farko a ran ta ,

Tunowa ta fara yi filla filla da farkon haɗuwar su har zuwa ranar ƙarshe da ya kore ta daga motar sa a tsakiyar titi  tana kuka , yayi tafiyar sa ya bar ta har yau bai sake waiwaiyar ta ba ,

tabbas shi macuci ne azzalumi agare ta bai chanchanta da samun soyayyar ta ba ko kaÉ—an ,

bai taɓa son ta ba , kawai amfani yayi da jahilcin ta ya ribaci gangar jikin ta ya yasar da ita tare da cikin da yayi mata , wani irin yanayi mai ƙarfi da kaifi ta ji yana keta zuciyar ta a game da shi , hannun ta ta kai ta tattaro bakin hijabin ta ta riƙe tare da cije gefen leɓen ta na ƙasa da ya zo daidai da zubowar hawayen ta da yake nuni da mummunan ƘULLACIN da tayi masa .... !!!!!!
[9/3, 10:13 PM] +234 806 122 1116: Fikrah writers association

MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )

umm'muaz

31

Ba ƙaramin kaɗuwa Youssouf ya yi ba lokacin da Maimartaba yake shaida masa zancen auren sa da Siyama , da har an riga an miƙa dukiyar auren ta ga mahaifin ta dake niamey , za'a yi ɗaurin auren sa da ƴan matan duk biyu a rana guda kamar yadda ya buƙata ,

Ya jima a zaune gaban Maimartaba yana jin yadda zuciyar sa take cunkushewa da tarin takaici ,

Ba tun yau ba ya gama lura da take-taken yarinyar , shi yasa sam baya sakar mata fuska ashe bai sani ba har tayi girman da zata iya yin tsaurin ido irin haka a matsayin ta na mace ta doshi iyayen sa da buƙatar son a haɗa su aure ? Babu shakka zata ɗanɗani kuɗar ta a hannun sa , sai tayi danasanin wannan mummunan shisshigi da tayi ta kutso kan ta cikin rayuwar sa da take a hargitse a halin yanzu ,

Ganin shirun sa ya tsawaita ba tare da ya amsa da amincewar auren ba , ya sa me maimartaba yin gyaran murya

  Da fatan ba zaka bijirewa oumarnin mu ba ? Bisa ga wannan haɗi da munka yi na amre tsakanin ka da ƴar ouwar ka , saboda ba muyi haka ba face sai da munka hango tarin alkhaire tare da dacewa sannan munka so ƙulla igiyar amre a tsakankanin ku , wannan ɗiya ɗiyar ƴar uwa ta ce , kai ma kuma ƴar ouwa take gare ka , ina yi maka oumarni ka karɓi amren nan da hannu biyu da ikon Allah gaba kai zaka yi farin ciki .

Kalmar 'Umarni, ta daƙile dukkanin wani yunƙuri da zai iya yi , domin shi ɗin me yawan biyayya ne ga iyayen sa , haɗi da sanin da yayi a yanzu shi me tarin laifuka ne , wanda yake neman wata kafa ko yaya ne da zai iya faranta ran iyayen sa ta dalilin ta, ko domin su iya masa uzuri a duk ranar da laifukan sa suka bayyana a gare su , su duba irin faranta mu su da yayi su sassauta masa hukunci ,

Cikin harhaɗa kalmomin da suke suɓcewa daga harshen sa saboda kaifin su da yake iya ji ya furta ,

Na Amince , Allah shi ƙara girma da ɗaukaka .

Da murmushi bisa fuskar sa yace

Madallah da kai , Allah shi maka Albarka , Ya Albarkaci zuri'ar ka , Allah shi yi katanga tsakanin ka da miƙiya , kana iya tafiya ka fara shiri doumin nan da sati biyu da ranar tayi dai-dai da gomma ga watan gobe ake ɗaurin amre .

Godiya yayi ya miƙe yana barin shigifar sarki , kai tsaye gidan da zai tarar da Tafeeda ya nufa ,

Cikin sa'a ya same shi dawowar sa kenan daga aiki da sanyin la'asar ,

Babu walwala a fuskar sa ya samu wajen zama bisa kujerun shan iska ,

  Ɗan ouwa ka kuwa san me ke shirin farouwa gare ni ?

Maida ganin sa yayi kan sa , bayan ya miƙa masa sassanyan lemun da ya tsiyayo masa a kofin gilashi ,

Sanar da ni É—an ouwa

Wai amren mataye biyu a rana gouda , kuma amre tare da yarinyar nan siyama da ko ƙamnar duban ta bana yi , shin baka yi tounanin akwai wani dalili da ya sa maimartaba haɗa min amren mataye biyu a rana gouda ba ?

    Ɗan guntun murmushi tafeeda yayi

Banda abun ka Yarima shin amren mataye biyu a rana gouda ba gata bane ?
   Ita siyama ai duk inda ake neman macen amre ta zarta ,

  Maimartaba bashi da sani kan kome wataƙila hasashe ne yayi irin nasu na manya ya sanya shi yi maka gatan amra maka mataye biyu a rana gouda ,

Juyar da kan sa gefe yayi yana jin yadda ran sa ke sake ɓaci , kan batun auren , ga kuma ya lura Tafeeda ba shi da niyyar taya shi jimami , shi ina zai kai mata har uku a shekarun nan nasa ??
   
Kurɓar lemun sa tafeeda yake yi yana satar kallon youssouf da yayi tagumi hannu biyu ya nisa cikin tunani ,
   So yake ya masa tambaya game da al'amuran sa na ƙasar nigeria , ɗiyar sa da take can , ƙaƙa ya ƙarƙare da barin ta a chan ? Hannun wa ya baro ta ? Sai dai rashin son tuno masa da ita ya sanya shi haɗiye tambayoyin sa , ga zaton sa Biyamuradi yayi amfani da shawarwarin sa , ya baro duk wasu kuskuren da ya aikata a inda ya aikata su !

Farin cikin da Siyama ta tsinci kan ta cikin sa bai misaltuwa , domin duk wani da ke mu'amala ta kusa ko ta nesa da ita zai iya shaida farin cikin tare da walwalar da ke tare da ita , da ɗai bata taɓa farin ciki me yawan haka ba cikin rayuwar ta ,

   Ƙulluwar aure a tsakanin ta da Youssouf wani abu ne da tayi shekaru tana mafarkin sa a bacci ko a farke , bata taɓa zaton zata samu damar mallaƙar sa a matsayin miji a sauƙaƙe haka ba , a kuma daidai lokacin da take zaton ya sulluɓe mata zai zama malakin wata ba ita ba , duk tunanin ta na bata sai wani nisan shekaru wataƙila idan da rabo suyi aure , ga haɓakar farin cikin ta ashe tabbatuwar mafarkin ta zuwa gaske yana kurkusa , ashe tare zasu mallake shi ita da wacce take tunanin ta fita sa'a , ashe sa'ar na gare ne su biyu ,?
Chapter 134 · 0% Book details