Sashe 55
Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yakaka wacce É—oki ya sa bata ko yi sallama ba bare tayi wa falmatar magana , tace,
     Nice fa falmata nah ,"
Aiyo yakaka na , to ai baki min magana bane ! Yau har kin gama aikin ne ?
Ban gama ba falmata ,
Mutumin shekaranjiya ne ya dawo yana so mu je na sake taimaka masa ,"
Zuruf falmata ta miƙe nima zan biki yakaka ,!
Tsam yakaka tayi ta bar ƙoƙarin sanya kayan ta da take yi ,
Ta taso ta zo ta kamo hannuwan falmata ,"
  Falmata na kiyi hakuri ki zauna har naje na dawo , kin ga aikin da nake yi masa mai wahala ne baza ki iya ba , kuma yau bazan kwana ba , anjima kaɗan zan dawo kin ji ?
  Da kyar ta shawo kan ta ta yadda zata jira ta tare da alƙawarin baza ta kwana ba zata dawo , da haka ta kammala shiryawa cikin wata atamfar cote d'ivoire ruwan zuma mai cizawa da aka yiwa ɗinkin riga da siket , duk cikin ire iren kayan da samy baby tayi mata kyautar su ne da basu sha jiki sosai ba ," wani turaren da samy baby ta bata lokacin da take menses ta ce ta dunga shafawa a jikin ta ,"shi ta ɗauko ta mutsittsika ,"
  Fes tayi kyau ta ɗaura ɗankwalin ta shigen yadda ta ga samy baby na yi , bata sanya gyale ba domin bata da shi kuma ka'idar gidan madam saly ba'a yawo da mayafi .!
Wannan karon a tsaye ta tarad da shi ya saka hannun sa ɗaya cikin aljihun wandan sa , da alama tsumayen ta yake cikin ƙaguwa ,"
Babu laifi a idon sa tayi kyau , duk da cewa shi ba wannan bane ya dame sa ,
Sai dai tana matsowa kusa da shi ya ji wani ƙamshi marar daɗi a hancin sa yana tashi daga jikin ta , sam ƙamshin bai masa ba ,!
Juyawa yayi ya fara taku ba tare da yace da ita ƙala ba ,"
Zungui-zungui ta bishi a baya ,
Duk yadda yaso ya Daurewa ƙamshin turaren dake tashi a jikin ta ya kasa , sosai yake jin wani yanayi marar daɗi a cikin ƙamshin , shi mutum ne mai tsananin tsafta da ƙyanƙyami sam bai son wani abu da yake da alaƙa da ƙazanta ,"
Dan haka lokacin da suka daidaita akan titi ,ya É—an juyo da ganin sa kan ta ,"
  Ki gwouda mini hanyar les salons !
  meye kuma Les salons, ? ita hausar sa gaba ɗaya wahalar fahimta take yi ma ta ,"
   A takaice ta amsa
  ban san wajen ba !
Wani wuri ya samu a gaba kamar super market ya tsaya shaguna birjik a wurin ,
Mayuka tare da sabulai zuwa turaruruka na mata , masu kyau da tsada ya jida ,
Ya koma banagare kayan sawa ,"shi ba wani sanin size ɗin ta ya yi ba dan haka ya ɗauki dogayen riguna baƙaƙe biyu ,
A wurin biyan kuÉ—in ya tambayi Cashier wurin salons , nan ya masa kwatance na wani shahararren wurin gyaran jiki da yin kwalliya , TaTa saloons da yake kan titin danboa .
Ya ajiye kayan a kujerar baya ya zo ya tada motar ba tare da yace da ita ƙala ba , ita ma kuma tayi shiru bata magana sai satar kallon sa ,
Tata salon babban wurin gyaran gashi , ƙafa da ƙumba , yin kwalliya da gyaran jiki , zuwa sayar da turarurrukan arabs masu kyau da ƙamshin sanyaya rai ,suna da gyalalluka na yayi masu matuƙar kyau da inganci .
Hajiya ruma mamallakiyar shagon mace ce mai karamci wacce ta san harkar kasuwa dan haka take girmama abokan cinikayyar ta , ( Allah ya ƙara ɗaukaka ƴar ƙanwa ta )
Sun ci sa'ar tarar da ita da kan ta , inda tayi musu tarɓar girma tare da ruwan gora da lemun gongoni ,"
nan youssouf yace ayi wa yakaka gyaran jiki tun daga salons zuwa pédicure , kai har wanka ma ayi mata ,! . Aka sa masa kuɗi ya biya .
Nan aka shiga da yakaka wani É—an É—akin da ya wadata da fitilun haske ,'
Suka fara aikin su , goge nan wanke chan , dirza nan shafa wannan goge wancen , har dai suka samar da yadda suke so a jikin yakaka , duk da cewa su da kan su sun yi mamakin irin dauɗar da take danƙare a kowanne lungu da sakon jikin yakaka ,
,misalin karfe takwas na dare suka fito da ita , tayi kyau ba kaÉ—an ba , É—an nude makeup É—in da suka mata ya sake fiddo da zallar manyan kyaun da take da shi , jikin ta sanye da É—aya daga cikin dogayen rigunan da ya saya mata ,sun yi mata naÉ—i da gyalen rigar bayan sun tara mata gashin ta mai rangwamen duhu sai tsanananin laushi da tsawo a tsakiyar kan ta sun kama mata shi da roba ,"
, ita da kan ta jin kanta take kamar ba ita ba kamar an sauya ta , wani irin nishaɗi ne yake huda ta , ƙamshin da yake mamaye da sassan jikin ta yana bata wani irin farin ciki na musamman, tsafta tayi a rayuwa ," ita kuwa me bature kam silum zai biɗa a wajen ta da baza ta iya masa ba ? ai babu !
Da ido yake bin ta da kallo lokacin da suka fito , duk da cewa idanuwan sa sun saba ganin kyawawan mata daga bangarori daban daban na duniya , amma kwarai irin nata kyaun ya burge shi ," daga inda yake yana jin tashin ƙamshin ta ,"
Da hakan ya sa shi sakar mata murmushi da suka haɗo ido , a karo na farko da yakaka ta ga murmushin sa wanda yake ƙarawa fuskar sa haiba , nan take ta washe gajerun hakoran ta da suka sha wanki tana maida masa da martanin dariya , tsintar kan ta tayi da tambayar sa ,"
   Nayi kyau ko ?
Murmushin bai gushe ba akan fuskar sa ya haɗa yatsun sa biyu babban da mabiyin sa ya mata alamu da kinyi kyau sosai !
Hannun sa ya miƙa mata ta ɗora nata akai ya ja ta suna mai ficewa a shagon
 ma'aikatan shagon suka bisu da kallon sha'awar da suka basu ,"Cikin ran su suna aiyyanawa ma'aurata ne irin sabon auren nan har wata ƴar gaza gani daga cikin su ta tanka ," perfect couples"
Kwanakin da suka biyo bayan wannan ranar biyamuradi youssouf da yakaka zama suke irin na masoyan ma'aurata , babu wata rana da ta tsallake musu da basu kwana tare ba .
Yayin da biyamuradi yake fidda kuɗi yana mayar da yakaka irin macen da yake so , ƴar hutu ƴar gayu mai tsafta , tata salons ya zama wurin zuwan su , bai jin ƙyashin kashe mata kuɗi tare da bata farin kuɗin tsurar su domin ta biya wasu buƙatun , har ƴar ƙaramar waya ya saya mata , wanda yake amfani da ita wurin kiran ta idan ya zo ɗaukar ta ," a yanzu burkutu guzurin ta yakaka take yi masa , har ɗakin da suka mayar na kwanan su a garki Guesthouses ,
Yakaka kuwa sau da kafa take bin biyamuradi youssouf cikin dukkanin buƙatun da ya zo mata da shi bata iya kuya masa baya , tana bashin haɗin kai tare da juriyar ɗaukar bukatun nasa ,"
A yanzu aikin gidan madam saly ya ragu a kan ta , saboda yadda biyamuradi da ita kan ta yakakar suke sakarwa madam saly kuÉ—i , wacce a rana ta biyu da yakaka ta sake bin biyamuradi suka kwana alhalin bata gama mata aiyukan ta ba kusan raba dare tayi tana zagin yakakar tare da shan alwashin a gobe gobe zata kore su ,
Da hakan ya sa falmata kwana tana kuka ita ba kome yafi bata mata rai ba irin kalmar "ƙaramar karuwa sabuwar yar iska ," da madam saly ta danganta yakakar da shi ba ,"
cikin muryar kuka ta dunga maimaita kalmar
  Yakaka na ba ƴar iska bace
  Yakaka na ba ƴar iska bace
Ƙasa-ƙasa yadda madam saly bata jiyo ta ,' tsaf ta gama kintsa musu jakar kayan su tana jiran gari ya waye yakaka ta dawo su kama hanyar su,"
Sai dai abun da ya ɗaure mata kai washegari bayan dawowar yakaka gidan tayi ta kasa kunne ta ji hayaniyar madam saly tana zagin su tare da kora kamar yadda tayi rantsuwa , " sai taji tsit , sai ma jin madam saly tayi ta zo har cikin ɗakin nasu tana bawa yakaka wani abu tare da shaida mata idan har ta sha shi da madarar ruwa ko nono , ba ƙaramar kyauta saurayin ta zai yi mata ba ƙila ma ya bata "mota ,"
Saurayi kuma yakaka ?
 Wanne saurayi ? Tambayar da falmata ta jefawa yakaka kenan , bayan ta cika bakin ta da donut, wacce ita ma yakakar ta toshe mata baki da kayan maƙulashen da biyamuradi ya ciko mata manyan ledoji da su ,lokacin da ta so tada bori akan kwanan da yakaka ta sake yi a waje ,!
  Ba saurayi na bane wanda nake taimakawa ne ,"
  Wai yakaka wane irin taimako kike yi masa da har yake baki kayan daɗi haka ? ga turare mai ƙamshi da kika ce ya baki har da su mai ," to kawai mu koma gidan su mana mu dunga yi musu aikin tare koh ba taimakon sa kike da aiki ba ?
Cikin diriricewa yakaka ta ce,"
  Ba-ba ba agidan su muke aikin ba a wani waje ne ,falmata kiyi zaman ki anan tun da ni ina zuwa nemo mana , kuma ina samo mana kuÉ—i , kin ga tunda kuÉ—aÉ—en dayawa idan suka taru har É—aki zamu iya kamawa mu bar gidan nan , mu kama sana'a a hankali a hankali muna neman su maman mu ko ?Â