← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 269

Sashe 103

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da cewa bangaren youssouf ya ji kaso sittin cikin ɗari na damuwar sa ta tafi , saboda ya bayyana ta ga aminin nasa , ya kuma san Tafeeda zai yi duk yadda zai yi ya ga ya dai-daita kome a gida kafin komawar sa  , yanzu babbar matsalar sa ita ce rayuwar ɗiyar sa ,

A daren jiya kwana yayi yana dogon nazari akan yadda zai yi ya ga ya bata ingantatciyar rayuwa ba tare da gurbatatciyar hanyar da aka samar da ita ta zama ƙalulabe a gare ta ba , da mutum yana iya sauya kaddarar sa da a daren na jiya ya juya , ya gyaro hanyar da aka yi ƴar nan ta sa ta zo duniya , amma ya riga ya san bakin Alƙalami ya bushe ,

hakan ya sa ya ɗau ƙuɗirin zai jajirce akan duk wani ƙalubale da shi zai iya cin karo da shi cikin rayuwar sa wajen ganin ya inganta tare da kyautata rayuwar ɗiyar sa ta FARKO a duniya ,"

Tafeeda kuwa ya bar ƙasar ran sa cike taf da tunanin yaya zai yi yaga ya boyewa hajiya umma musabbin shiga damuwar yarima ?  Ya zai yi ya boye mata irin mummunan aikin da yarima ya aikata ? Yaya zai boye mata samuwar wata haramtatciyar ɗiya daga tsatson ta ? Kome yana neman kubce masa , shi ya kasance a tsakiya ne , ɗan aike ne shi , sai dai saƙon da zai koma da shi a yau me nawi ne wanda ya fi ƙarfin fitowa daga kan harshen sa ,

Cikin awanni (2) da tashin jirgin su daga Murtala Mohammed International Airport Lagos, Ya samu dira a Diori Hammani International Airport Niamey , duk yadda ya so ya tsaya wajen 'ubbo' su gaisa kamar yadda ya tsara , ya gagara saboda rashin nutsuwar zuci , Allah-Allah ya ke ya samu isa wajen hajiya umma ,"

Jirgin da zai sada shi da MaraÉ—i kai tsaye ya hau , yana isa gidan su wanka kawai yayi ya sauya kaya ,ko abinci bai duba ba ya yiwa fada tsinke , nan ya nemi iso ga hajiya umma , aka yi masa ba tare da jinkiri ba ,"

     Bayan ya gaishe ta yayi shiru yana son samun ƙarfin guiwar faɗin abinda ya shirya ,"
   Yayin da ita kuwa hajiya umma baki ɗaya ta tattara hankalin ta gare shi , tana nazarin sa ," ita ta katse shirun da tambayar sa ,'
    Yaya kun ka ƙarƙe da yarima ? Shin ya sanar da kai damouwar sa ? Ko kouwa ?
   
   Ƙwarai ranki ya dade yarima ya shaida min basshi da watta damouwa da ta wucce , na rashin aboukiyar zama , inda har ya nouna ra'ayi da zai yiwu ma yana buƙatar a amra masa mataye biyu a rana gouda wanna shine ɗai guda damouwar yarima , sai kouma yace ayi albishir yana nan tafe nan da ƙarshen wata me kamawa, bayan haka yarima yana nan lafiya cikin yanayi mai kyau !

   Tafeda ya ƙarasa zancen sa yana sunkui da kai da jin kunyar ƙaryar da ya gilla , wacce rashin mafita ya ja sa ga aikata ta ,"
  
  A take fuskar hajiya umma ta yalwatu da fara'a zuciyar ta ta haskaka , har haƙoran ta suka bayyana ,"

   Alhamdulillah , Madallah da kai Tafeeda yaron kirki , tashi maza ka tahi    ka sanya a fara shiri tare da gyara ga bangaren da anka gina na wagga ɗiya ƴar mutan agades , zan yi magana da mai martaba akan buƙatar da yarima ya tado da ita , amsa zai isar maka , Madallah da kai ,Madallah !
   
   Godiya Tafeeda yayi tare da miƙewa yana barin shigifar , yana sake ganin dacewar shawarar da ya bayar na aurawa Yarima mataye ganin sa hakan ne mataki na farko na dakile sa daga sake faɗawa cikin wata musibar a gaba , domin ya ƙare nazari kaf rashin aure shine dalili na farko da har ya sa Yarima faɗawa ga zina ,

Yana fatan yadda ya rufa asirin mummunan labarin nan a nan gaban hajiya umma , Youssouf ma ya rufawa kan sa asiri ya bar ɗiyar chan a Nigeria kamar yadda ya faɗa masa , idan kouwa har ya ƙi jin shawarar sa babu shakka jiki magayi ,"duka da ɗanyen kara ," tsuntsun da ya jaa ruwa kuma shi ruwa kan doka , shi dai yayi iya yin sa ," 

  Faɗuwa ta zo dai-dai da zama , shine abunda hajiya umma take kitsimawa cikin ran ta , ganin cewa a saukaƙe tare kuma da haɗin kan yarima auren sa da Siyama zai tabbata , kai wannan Al'amari yayi kyau gwanin daɗi , cikar gata da martaba ne ga ɗan nata ya auri mataye biyu a rana gouda , tabbas maƙiya zasu cija yatsa , girma da martaba kouwa zasu tabbata ga Yarima Youssouf ,"
    Nan ta kudurce sanar da maimartaba a daren na yau da ita ke da turakar !

          *****

Biyamuradi Youssouf yana barin airport inda ya raka Tafeeda gidan su Dr Hamza ya nufa , maigadi shi ya nema masa izni,

  Yana shiga ya tadda prof yana karin kumallo , suka gaisa faram-faram nan ya masa umarnin ya matso su ci abincin ,

Babu musu ya wanke hannun sa ya matso suka fara cin abun ƙarin ,"Fankaso ne da miyar ganyen alayyahu , sai kuma danderun tsokar ƙaramar dabba , gefe guda kuma kwaɗon zogale ne da yake mahaɗin kowanne cin abinci na prof ,sai kuma green tea ,

    Sosai ya nutsu ya ci abincin yana yabawa girkin maiduguri , bayan sun gama cin abincin ne prof ya gyara zama yana fuskantar Youssouf ɗin ,cikin nazari yace
    Zan so ka sanar da ni takaitatcen tarihin ka da kuma halin da ka kasance a ciki bayan rabuwar ka da iyalin ka da ta sanar da mu cewa ka mutu sanadin ƴan tawayen nan na boko haram ,"

     Shiru yayi yana jin yadda tausayin ta ke sake mamayar sa , Allah sarki ashe ta rufe kome , ta rufa musu asiri , ta lulluɓe laifin sa , ta gyara masa asalin ɗiyar sa a idanun jama'ar ta , idan haka ne shi kuwa zai cigaba da kare martabar ta a idanun su har abada , shi ma bazai taɓa tono laifin su da ta binne ba ,

  Asali na ni mutumin niger dagga yankin ,"Malbaza Uzine," dake ƙassar Tahoua ," ni sojja ne aiki ya shiggo da ni nan nigeria har munka yi amre da itta , bayan amren mu bada jimawa ba boko haram sunka kawo hari mahaɗar mu inda sunka far mouna da yakin da yayi sanadiyyar rabouwar mu har ta kai ga tayi zaton na moutu, sun ka yi gudun hijira zouwa nan ,"

  Lokacin da kuka yi aure a hannun iyayen ta ta karbi auren ta ?
  
   Mukut ! Biyamuradi ya haɗiyi yawu , shi wannan mutumin matsayin me yake gare ta ? Zaton sa ɗan ouwa ne ga mahaifi ko mahaifiyar yarinyar ,"

Cikin ƙosawa yace

   Mahaifi gare ta ya rassu , sai dangin ta ,"
 
  Kayi hakuri ina maka tambayoyi ne domin mu tabbatar da gaskiyar Alaƙar ku saboda yau duniya babu gaskiya ,"

Mu ma ta shaida mana mahaifin ta ya rasu sanadin tarzomar boko haram , mahaifiyar ta tare da sauran dangin ta sun bata , ta zo nan mun ƙarbe ta tare da ƴar uwar ta sai kuma juna biyu tare da ita wanda ta rasu wajen haihuwar ƴar,  ɗan waje na shine ya kawo su nan bayan ya tsince su suna walagigi cikin wahalar rayuwa a bakin titi ,

  Ya tsahirta ,

Yana duban Youssouf wanda idanun sa suka yi jaa saboda jin tausayin Yakaka da ahalin ta,

   Idan har dattijon nan da ya ɗauka wani jigo ne ga yakaka , yace shi bashi da wata alaƙa da su asalima taimakon su ɗan sa yayi suka kasance ƙarƙashin inuwar su , shi kuwa ai babu dalili ɗaya da zai sa ya bar ɗiyar sa hannun su , wajibi ne ya tafi da ƴar sa ,

Kamar Prof ya san tunanin da Youssouf É—in yake yi , sai yace da shi
 
  Idan ka shirya tafiya da ƴar ka , koyaushe zaka iya zuwa ka amshe ta , tana tare ne da ƳAR UWA ga mahaifiyar ta wacce ka gan ta riƙe da ita jiya ,"

A hankali ya É—ago kan sa , yace zan iya ganin su ?

Ƙwarai kuwa bari a ƙira su ,"

Cikin mintuna kaɗan falmata riƙe da baby mama ƙarƙashin jagorancin hajja mai wurya suka bayyana a falon , fuskar falmata babu walwala , saboda ƙiran da aka mata na cewa ta kawo baby mutumin jiya ya dawo ganin ta , tambayar kan ta take yi wanene wannan mutumin da yake ta zaryar ganin baby mama ,?  Ita fa sam bata ƙaunar abunda zai ratsa tsakanin ta da ƴar kome ƙanƙantar sa ,

Bayan ta gaishe da prof da take jin tashin muryar sa tun shigowar ta falon ,

  Yace da hajja mai wurya
   Ƙarbi ƴar ki miƙa ta ga mahaifin ta , mun riga dai mun mata hudhuba tare da yanka kamar yadda addini ya zartar , ƙarƙashin yaddar uwar riƙon ta kuma ƴar uwa ta jini ɗaya da muka sani tare da yarinyar kafin bayyanar ka , amma kana da ikon sauyawa ƴar ka suna !

    Janye ƴar falmata tayi ta hana hajja mai wurya damar ɗaukar ta ,"

Waye baban baby ? Waye yace shine baban baby ? Baby ƴar mu ce ni da yakaka na , mu kaɗai muka haife ta , yanzu da babu yakaka ni ce mama , baba , yaya , kanwa , da gabaɗayan danginta , ko waye ma yace shine baban ta ƙarya yake muku wallahi ƙarya ne , ta ƙarasa zancen tana fashewa da kuka !
Chapter 103 · 0% Book details