← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 269

Sashe 23

Mafari Hargitsin Rayuwa Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaren sojojin su ma suna ƙarƙashin umarnin ubangidan su ne wanda yake cikin ɓakar motar sumfurin ( purchase ) mai ɗauke da ɓakaken gilasai daga shi sai direban shi , ya shaƙa har iya wuya , a saboda haɗa hanyar sa da ta siyama , sosai yake jin zafin yarinyar shi da kan sa kuma ya rasa dalilin hakan kullum abun sake gaba yake ,

Sai da ya mula dan kan sa ya ɗago ya kalle ta yadda har ta fara haɗa gumi a ƙwaleliyar ranar damina ," yayiwa direban sa umarni da ya buɗe mata gidan gaba ,"

Cikin nutsuwa tayiwa kanta matsugunni a gaban motar tana me sauke ajiyar zucin wahalar tsayuwar da tayi , karaf suka haÉ—a ido ta mudubin gaban motar , da hanzari ta janye idon ta , dai-dai lokacin da direban ya tada motar ,sauran motocin suka bi bayan su ,

Suna gaf da barin gari ya cewa direban nasa ,"agades muka nufa ",  cikin cika umarnin ubangidan sa ya amsa gami da karya kan motar ya ɗauki hanyar da zata kai su ga hawa titin katsina ,zuwa zender ,sannan yankin agades ,"

Ɗas ! Kirjin ta ya buga ta maimaita kalmar ',Agades ' me kuma zasu je yi agades su da suka nufi niamey wannan wane irin bahaguwar tafiya ce mai kwan gaba kwan baya ,a maimakon ayi gaba an sake nausawa baya ,? Gimbiya maimouna ta garin agades ", sunan da yayi amsa kuwwa kenan cikin ƙwaƙwalwar ta ,

Tabbas yankin su maimouna suka nufa , hakan yana nufin biyamuradi wurin budurwar sa yake nufin zuwa tare da ita ,!

Tunanin ta ya katse lokacin da ta tsinkayi muryar sa yana yin waya " hello Princess ,
dan kyakkawan murmushi ta hango saman fuskar sa,"da ya bata tabbacin wata kalma aka furta masa me daÉ—i,"
"Gamu bisa hanya,'
", ameen sai mun iso je t'aime ",
.
  Ji tayi ran ta yana tuƙuƙi ,kwantar da kan ta tayi gami da lumshe idanun ta ranta cike taf da tunanin gamuwar su da gimbiya maimouna tana kuma saƙawa da warware yadda zata yi amfani da duk wata damar da zata iya zuwa mata wurin yaƙin neman ƙwato biyamuradi youssof daga wurin kowacce mace , kamar yadda tun farko ta tsara wannan tafiyar tata zuwa wurin 'ubbo' da nufin fara dasa harsashin ginin ta ... Toh fah!

# *vote*
# *comments*
# *share*
*THANKS*
[6/24, 9:59 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association

*MAFARI.......*
_( Hargitsin rayuwa_ )

*Umm'muaz*

8

Miƙa tayi bayan ta ya bada sautin "ƙaƙas" sakamakon zaman awanni baƙwai da tayi wanda zata iya cewa wannan ne karon ta na farko da tayi doguwar tafiya irin haka a mota ,"

Wara idanun ta tayi sosai tana bin jerin gwanon bayin da ba sai an mata bayani ba tasan bayun yankin masarautar agades ne ,"cikin ranta kuwa mamaki fal take na ganin irin didima tare da sarewar da ake busa masu ,"wanda ya bata tabbacin anyi shiri sosai domin taryar biyamuradi,  nan take taji wani malolon bacin rai ya tokare ta a maƙoshi .,

Bata fargar ba sai gani tayi bayun nan sun jagoranci biyamuradi zuwa ainahin cikin ginin masarautar wasu ta baya wasu ta gefe da gefen sa ," yayin da sojojin sa suka dakata daga inda suke ,"

Ganin haka ya sa cikin sassarfa ta soma taku tana bin bayan su da har suka riga suka danna kan su cikin shigifofin gidan  ,"cikin ranta kuwa tarin nadama tare da bakin cikin biyo biyamuradi take ,"wanda duk da sanin cewa da tayi basa shiri amma bata zaci kiyayyar sa da walakancin sa sun kai har haka ba a gare ta , duba da cewa tun da suka ɗauko hanyar tafiyar awanni bakwai koh kalmar sannu bata sake haɗa su ba ,"sai ita da  take ta faman satar kallon sa haɗi da sauraron amon muryar sa ,"

Basu yi wata tafiya mai nisa ba a faffaɗan filin da yake mazaunin harabar gidan sarautar wanda yake rairayi ne tas-tas lallausa ,da ya ɗauki yanayin damina da sanyin la'asar yake bada wani irin sanyin ni'ima da kamshin ƙasa mai sanya nishaɗi a zukata .,

Amon sautin muryar biyamuradi taji ,"wanda ba ta kai ga fahimtar abun da yake faɗi ba , sai dai ta fahimci umarni ne ya basu ganin wasu tsiraru daga cikin su sun juyo gami da ƙarasowa gaban ta da take da ɗan tazara da su ƙadan ,"

"Ranki shi daɗe yarima yai umarni da a sada baƙuwathei ga shigifar gimbiya "
GyaÉ—a kai tayi yayin da dogarawan nan uku suka shige gaba ta juya ta bisu a baya tana waiwayar tawagar biyamuradi wanÉ—anda suka nausa shiyar gabas ba tare da ta samu arzikin da zata samu koh da kalma guda daga gwarzon nata ba ,"

Fiye da yadda tayi zato gini da tsarin masarautar agades ya tafi da hankalin ta tare da burgeta sosai da sosai ,"ware idanu tayi tana bin kowanne zane da taswirun da aka ƙawata bangon kowacce shigifa da ita ,da kallo mai bayyana shauƙi tare da burgewa ," kafafun ta da suke babu takalma tun a shigifar farko suna waɗakata cikin lallausan shimfiɗun alfarmar da suke ƙwance a kowacce shigifa,"

Cikin kowacce shigifar da zasu gifta bayu mata ne su huÉ—u suke zubewa gami da kai gaisuwa tare da tambayar inda suka nufa ,"amsa guda dogarawan suke badawa ."

    Wagga diya baƙuwace da suke tafe tare da yarima biyamuradi ,kuma wurin gimbiya aka biɗa da a sada ta ,"

Har zuwa ga shigifar da tafi kowacce tsaruwa inda daga nan dogarawan suka juya bayan sun damƙa ta a hannun wata baiwa wacce tayi mata umarnin zama akan ɗaya daga cikin shimfiɗun alfarmar dake wurin ,tare da sanar mata ta jira gimbiya na nan fitowa bayan almuru ,"

Cikin takaici take duban baiwar da ta miƙe bayan kammala bayanin ta ,"

   "Tou ki sada ni da inda zan yi alwala na kimtsa domin ina da bukatar yin haka ,

Siyama ta furta hakan ba tare da ta kai duban ta ga baiwar ba domin zuwa lokacin ta fara shaƙar takaicin halin ko'in kula da rashin girmamawan da ta fara hango alamun su ga hadiman gidan wanda ta hakikance ba kowa ya jawo mata hakan ba illa biyamuradi da ya danganta ta da matsayin Baƙuwa a gareshi a maimakon ƙanwar sa ƴar uwa ," domin ta tabbatar da ace ya kiraye ta da matsayin ƙanwa agareshi da tabbas ya samar mata da girma tare da matsayi a idanun hadiman gidan .,

    Bayan idar da sallar ta "na magarib" tayi kimanin mintuna talatin tana zaune ,wanda har zuwa lokacin babu wacce ta sake bi ta kan ta cikin tarin bayun da suke ta kai kawo da manyan tire da tasoshi na alfarma a hannayen su waɗanda suke rufe ruf da mayafai iri guda masu launin ruwan sararin samaniya ", suna nufar wani sashi da ƙofar sa take rufe ta hannun dama ,

Cikin ta kuwa idan ban da ƙugin yunwa babu abun da yake ,"yayin da ita kuma ta sha alwashin baza ta sake tuntubar hadiman gidan kan wata bukata tata ba ," hasalima kishingiɗa tayi gami da lumshe fararen idanun ta ,gefe guda na zuciyar ta tana nazarin yadda lamuran suke tafiya .,

Wani sassanyan ƙamshin turare ne ya fara bugar hancin ta kafin taji tashin muryoyin hadiman da suke cikin shigifar suna kirari tare da ƙwarzanta uwargijiyar su ,"

Ta ɗauki kimanin mintuna biyu kafin ta buɗe idanun ta a hankali ,"fes suka sauka cikin manyan idanun kyakkyawar budurwa da take zaune cikin shiga ta alfarma akan wata shimfida da ita bata san lokacin da aka samar da ita ba ,"kallon - kallo suka yi na adadin wasu daƙiƙai kafin siyama ta mayar da nata fatar idanun ta lumshe zuciyar ta kuwa bugawa take ɗas,ɗas,ɗas ,

tabbas wannan ce gimbiya maimouna , babu shakka ta amsa sunan ta ,' ganin ta kuma ya zo dai-dai da jin labarin ta ," sai dai koh kusa bata ji ta karaya ba bata ji ta tsorata ba ,sam ƙwarjinin ta bai ɗimautata ba ," hakan ya sa ta cigaba da lumshe idanun ta tamkar mai bacci wanda babu wanda ya lura da buɗesu da tayi ta rufe sai ita gimbiya maimouna wacce hasken lantarkin da yake tarwai ya bata damar hango cikin ƙwarar idanun siyama wacce bata kai ga sanin wacece ba hasalima bata san da zuwan ta ba ,"

  Gnala wagga ɗiya daga ina ta tahou ?
   Wacece ita ? Gimbiya maimouna ta furta hakan tana mai kai duba ga inda siyama take kishingiɗe

Cikin girmamawa wacce aka kira da "gnala" ta amsa

      "afuwa take biɗa , wagga ɗiya baƙuwa ce da suke tafe tare da mai girma yariman maraɗi tun da yammaci ta samu isowa nan ƙarƙashin rakiƴar dogarai su sunka isar da sakon wanzuwar ta anan daga bakin yarima ,"

Mayar da duban ta ta sake yi ga kyakyawar hausa/fulanin fuskar siyama ," nan take ta hango yanayin kamannin masoyin ta akan fuskar siyamar da take da tabbacin ba bacci take ba ,"ginshiri ne kawai tare da ƙasaita wanda ta danganta hakan ga kasancewar ita ma siyamar ɗiyan sarki ce kamar yadda tayi zato ,"siyamar ƙanwar youssouf ce wacce bata kai ga sanin ta ba , domin duk cikin tarin ƙannen sa da ta hakiƙance yana da su bai taɓa yi mata zancen kowa ba sai na "Aisha merama" ta kuma tabbatar ba ita bace wannan domin ya sha gwada mata hoton meramar maraɗi ,"

Nan take ta hango kuskuren da hadiman ta suka aykata na barin gimbiyar maraÉ—i bisa wannan shimfiÉ—ar da bata kai ba a wurin ta .

Gyaran murya tayi cikin yaren su na azbinawa tace ,"

    Gnala a samarwa gimbiyar maraɗi kyakyawar shimfiɗa a wadata ta da abin sha da na ci haɗi da bigire mai kyau domin tayi wanka ta sauya kaya ta huta kafin mu gaisa ,wagga ɗiya gimbiyar maraɗi ce , kar a sake ayi wani abu na rashin ɗa'a da zai taɓa martabar mu har zuwa tafiyar ta ,ɗiyar girma ce maza a girmamata,"
Chapter 23 · 0% Book details